in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da sabbin dokokin sassauta kudaden haraji
2019-03-17 16:05:01 cri

A jiya Asabar kasar Sin ta sanar da sabbin dokokin da suka shafi biyan kudaden haraji domin samar da sassauci ga daidaikun mutane game da batun biyan kudaden haraji na kudin shigarsu na kasashen ketare wato (IIT) a takaice.

A bisa dokokin na hadin gwiwa tsakanin ma'aikatar kudi ta kasar Sin da hukumar tattara kudaden harajin kasar wato (STA), daidaikun mutanen wadanda ke zaune a cikin babban yankin kasar Sin na tsawon shekaru 6 a jere kuma sun zauna a kasar cikin kwanaki 183 ko kuma sama da haka, a duk shekara za'a bukaci su biya kudaden harajin na IIT daga cikin kudaden da suke samu na kudin shigarsu daga kasashen waje. Idan ba haka ba, kudaden shigar da suke samu daga kasashen waje za'a tsame shi daga cikin tsarin biyan harajin na IIT.

Za'a sake tsara wa'adin shekaru 6 idan mutum ya bar ainihin babban yankin kasar sama da kwanaki 30 a jere a cikin shekara guda, kamar yadda dokar ta nuna.

Dokokin, sun fara aiki ne tun a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2019, kana zaman da mutum ya yi a kasa da sa'o'i 24 a cikin babban yankin kasar ba za'a lissafa shi a matsayin kwana guda ba, kuma za'a a fara lissafi ne daga ranar 1 ga watan Janairun wannan shekarar.

Sauye sauyen da aka gudanar an yi shi ne da nufin kyautatawa wajen samar da sassauci ga biyan haraji daga kudaden shigar da baki 'yan kasashen waje suke samu da kuma 'yan kasar wadanda ba 'yan asalin babban yankin kasar ba ne da suke gudanar da aiki a babban yankin kasar. Matakin zai kara janyo hankalin baki 'yan kasashen waje dake son zuba jari da kuma kwararru 'yan kasashen waje don sha'awar yin aiki a babban yankin kasar Sin, in ji hukumar ta STA cikin wata sanarwa ta shafinta na intanet. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China