190320-Muhimmancin-sabuwar-dokar-kasar-Sin-kan-baki-masu-shaawar-zuba-jari.m4a
|
A shekarar 2018 ne, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC, ta ayyana dokar zuba jari ga baki 'yan kasuwa a cikin shirin kafa dokoki na shekarar.
Sabuwar dokar ta maye gurbin wasu dokoki guda uku da suka shafi zuba jari da ake amfani da su a halin yanzu. Wato, dokar kamfanonin hadin gwiwar jarin gida da waje, da dokar kamfanonin jarin waje da kuma dokar kamfanonin da Sin da kasashen waje suka kafa tare.
Haka kuma daftarin dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, tana kunshe da wasu ayoyi 6, ciki har da babbar manufa, da inganta zuba jari, kiyaye zuba jari,sanya ido kan zuba jari, nauyin doka da wasu karin manufofi.
Ana kuma fatan dokar za ta kyauttata tare da kirkiro tsarin dokokin zuba jari na 'baki 'yan kasuwa na kasar. Wani muhimmin abu dake cikinta shi ne, ta tanadi wani sabon tsari, wato masu zuba jari na kasashen ketare za su samu dama iri daya da takwarorinsu na kasar Sin a yayin da suke neman zuba jari a kasuwar kasar, baya ga haka, ban da sassan da baki 'yan kasuwa da a baya ba za su iya zuba jari ba, baki 'yan kasuwa za su samu matsayin daya da takwarorinsu na kasar Sin wajen zuba jari a kasar.
Masana na ganin cewa, bayan zartas da wannan doka, za ta taka muhimmiyar rawa wajen kwantar da hankalin kamfanonin masu jarin waje, ta yadda za su nemi ci gaba mai dorewa a nan kasar Sin. Ban da wannan kuma, za ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa tsarin tattalin arzikin kasuwanci na kasar Sin, da wani muhallin takara mai adalci.
Wannan doka tana da muhimmanci kuma ta amsa tambayoyi da kasashen waje ke yi a wannan fanni da ma nuna aniyar kasar Sin ta kara bude kofarta ga kasashe waje.(Ahmed,Saminu,Ibrahim,Sanusi Chen)