in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kasa da kasa na raya Afrika a Morocco
2019-03-15 10:01:00 cri
An bude taron kasa da kasa karo na 6, kan raya nahiyar Afrika, jiya Alhamis a birnin Casablanca na Morocco.

Shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio da kasar sa ke matsayin babbar bakuwa ne ya jagoranci bude taron mai taken "when East meets West" wato "a lokacin da gabas ya hadu da yamma".

Da yake jawabi, shugaban na Saliyo, ya jadadda cewa Afrika na da dimbin damarmaki da yawan al'ummarta da ya kai biliyan daya da kuma albarkatu daban-daban da take da su, sai dai kuma ba a amfani da wadananan dimbin albarkatu.

Ya kara da cewa, nahiyar na da damarmaki da dama ga masu zuba jari a fannoni daban-daban kamar aikin gona da cinikayya da makamashi mai tsafta.

Shugaba Maada Bio, ya jaddada bukatar cike gibin kayakin more rayuwa da kuma shawo kan manyan kalubalen inganta zaman lafiya da yaki da cin hanci.

Taron na yini biyu wanda asusun zuba jari na Morocco Al Mada ya shirya, dandali ne na tattaunawa da inganta zuba jari da cinikayya tsakanin kasashen nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China