in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan bindiga sun hallaka mutane 17 a arewacin Najeriya
2019-03-15 09:19:53 cri
Hukumar 'yan sandan jahar Kaduna dake arewacin Najeriya tace wasu 'yan bindiga dauke da makamai da ba'a san ko su wanene ba sun harbe 'yan kato da gora 17 a wani harin da suka kaddamar a kauyen Jan Ruwa a ranar Talata.

Wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Yakubu Sabo, kakakin hukumar 'yan sandan jahar ya bayyana cewa, 'yan bindigar sun shiga kauyen ne inda suka yi awon gaba da shanu masu yawa.

Yace jami'an kungiyar 'yan kato da goran dake kauyen suna bada taimako wajen samar da tsaro da kuma farautar bata gari dake fakewa a cikin dazuka. Sun yi mummunar arangama da 'yan bindigar masu dauke da makamai, lamarin da yayi sanadiyyar rayukan jami'an kungiyar 'yan kato da goran.

Ya kara da cewa, da farko an tsinci gawar 'yan kato da goran 15, kana daga bisani aka sake gano karin gawarwakin mutane biyu.

Kwamishinan 'yan sandan jahar Kaduna Ahmad Abdurrahaman, yayi Allah wadai da kisan sannan ya sha alwashin damke 'yan bindigar da suka aikata kisan.

Abdurrahaman ya bukaci al'umma dasu taimakawa jami'an 'yan sandan wajen basu muhimman bayanai game da duk wasu mutane ko kungiyoyi da basu amince da su ba domin samun nasarar kawar da bata gari a fadin jahar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China