Zhang Jianlong, ya ce Kasar Sin ta kara fadada dazukanta da kusan kaso 10, tun bayan fara aiwatar da manufar bude kofa da gyare-gyare, inda ta zama kasar da ta samar da dazuka mafi girma ta hanyar shuke-shuke da kuma fadada yankunan dazuka da kaso 80.
Mamayar shuke-shuke a yankunan karkara ya kai kaso 20, yayin da na yankunan birane ya kai kaso 37.9.
A cewar Jami'in, a wani bangare na samar da kasar Sin mai kyan gani, kasar ta lashi takobin kara fadada dazuka da kaso 26 ya zuwa shekarar 2035. (Fa'iza Msutapha)