in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda kasar Sin ke fatan ganin an gina duniya mai zaman lafiya
2019-03-17 15:10:57 cri

Yayin da ake ci gaban muhimman taruka biyu na kasar na shekarar 2019 ne, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Mr. Wang Yi, ya shirya taron manema labarai, inda ya amsa tambayoyin da 'yan jaridun kafofin watsa labaru na gida da na waje suka yi masa. Tambayoyin sun shafi fannoni kamar dangantakar dake tsakanin manyan kasashe, rikice-rikicen shiyya-shiyya, batun yankin Koriya, da na nahiyar Afirka wadanda dukkansu suke jawo hankulan kasashen duniya.

Mr. Wang ya kuma bayyana yadda kasar Sin take hangen yadda makomar duniya za ta kasance a nan gaba, da yadda kasar Sin za ta ba da karin gudummawa wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa, inda ya kuma bayyana yadda kasar Sin take kokarin mayar da duniya ta zama tamkar al'umma guda.

Duk da sarkakiya da sauye-sauye da duniyarmu take ciki, al'ummar Sinawa sun hada kansu a cikin shekaru 70 da suka gabata, musamman a cikin shekaru 40 da suka gabata, tun bayan kaddamar babbar manufar yin gyare-gyare a gida da bude kokfa ga ketare, Sinawa kusan miliyan dari 8 sun kubuta daga kangin talauci, lamarin da sanya kasar Sin zama kasa mafi girma ta biyu a fannin bunkasar tattalin arzikinta. Yanzu, salon neman bunkasuwa da kasar Sin take amfani da shi yana ta samun amincewa da ma koyo daga dimbin kasashe masu tasowa.

A zahiri, bunkasuwar kasar Sin cikin lumana na kara samun amincewar kasashen duniya. Binciken baya bayan nan da wasu hukumomin binciken ra'ayin jama'a na kasashen Jamus da Amurka suka yi, ya nuna cewa, jama'ar Turai da Amurka suna ganin cewa, sun fi amincewa da kasar Sin fiye da sauran kasashe. Sinawa na da ra'ayin duniya ta zama tamkar al'umma guda. kasar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiyar duniya, da ciyar da rayuwa da makomar dan Adam gaba. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China