in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da nune nunen yanayin hakkokin bil adam a Xinjiang na kasar Sin a birnin Geneva
2019-03-09 15:54:17 cri
An gudanar da nune nunen yadda yanayin 'yancin bil adama ke ciki a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, dake arewa maso yammacin kasar Sin, daga ranar 4 zuwa jiya 8 ga wata, yayin taro karo na 40 na majalisar kare hakkokin jama'a ta MDD.

Nune nunen da aka yi wa taken "ci gaba da nasarar 'yancin bil adama a Xinjing" wanda ya gudana a ofishin MDD dake Geneva, ya kunshi sama da hotuna 80 dake bayyana tsarin cin gashin kai na jihar, da zaben demokuradiyya a matakin yankuna da 'yancin bin addini da kare al'adun kabilun dake jihar da sauransu.

Shirin kasar Sin na dindindin a ofshin MDD na Geneva ne ya dauki nauyin nune-nunen da hadin gwiwar cibiyar nazarin hakkokin bil adama ta kasar Sin.

Shugaban shirin na kasar Sin Yu Jianhua, ya ce ya yi ammana hotunan za su taimakawa mutane kara fahimtar yanayin kare 'yancin bil adama a Xinjiang, musamman ma don saboda kada wasu dake da mummunan nufi su batar da su, ta hanyar jirkita gaskiya domin yin tsokacin da bai dace ba a kan jihar.

Mataimakin wakilin dindin-din na kasar Rasha a ofishin, Nikita Zhukov, ya ce yana ganin koyar da sana'o'in hannu da sauran matakan da gwamnatin Xinjiang ta dauka sun taimaka wajen inganta dabarun ayyuka yayin da ake raya jihar.

Ya kara da cewa, talauci ba ya iya kiyaye hakkokin al'umma da na siyasa, kuma idan babu ci gaba, babu yadda za a yi a samu nasarori a sauran fannoni. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China