A yayin taron manema labaru da ministan harkokin wajen kasar Sin, kana mamban majalisar gudanarwar kasar Mr. Wang Yi ya shirya a yau Juma'a a nan Beijing, Mr. Wang Yi ya shafe kusan sa'o'i biyu yana amsa tambayoyin da 'yan jaridun kafofin watsa labaru na gida da na waje suka yi masa. Wadannan tambayoyin sun shafi batutuwa, kamar dangantakar dake tsakanin manyan kasashe, rikice-rikicen shiyya-shiyya, batun yankin Koriya, da na nahiyar Afirka wadanda dukkansu suke jawo hankulan kasashen duniya. A lokacin da yake ba da amsa wadanan tambayoyi, Mr. Wang ya kuma bayyana yadda kasar Sin take hangen yadda makomar duniya za ta kasance a nan gaba, da yadda kasar Sin za ta ba da karin gudummawa wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa, inda ya kuma bayyana yadda kasar Sin take kokarin mayar da duniya ta zama tamkar al'umma guda.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha nuna cewa, yanzu duniyarmu tana fuskantar samun sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin shekaru 100 da suka gabata. A irin wannan yanayi mai sarkakiya da duniyarmu take ciki, bisa shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, al'ummar Sinawa sun hada kansu sun yi kokari tare a cikin shekaru 70 da suka gabata, musamman a cikin shekaru 40 da suka gabata, tun bayan kaddamar babbar manufar yin gyare-gyare a gida da bude kokfa ga ketare, Sinawa kusan miliyan dari 8 sun kubutar daga kangin talauci, lamarin da sanya kasar Sin zama kasa mafi girma ta biyu a fannin bunkasar tattalin arzikinta. Yanzu, salon neman bunkasuwa da kasar Sin take amfani da shi yana ta samun amincewa da ma koyo daga dimbin kasashe masu tasowa. Wani dan jaridar kasar Ghana ya bayyana cewa, akwai kasashen Afirka da dama wadanda suka amince da salon neman bunkasuwar kasar Sin, inda suka amince da shawarar "ziri daya da hanya daya".
"Ziri daya da hanya daya" shawara ce mai matukar ma'ana da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a shekara ta 2013, da nufin daukaka ci gaban duniya baki daya. A halin yanzu, akwai kasashe 123 gami da kungiyoyin kasa da kasa 29 wadanda suka rattaba hannu tare da kasar Sin kan takardun hadin-gwiwa a fannin inganta ayyukan shawarar "Ziri daya da hanya daya", al'amarin da ya shaida irin goyon-baya da amincewa da suka nuna ga wannan shawara. A kasar Kenya, layin dogon da aka shimfida tsakanin Mombasa da Nairobi ya taimaka da kashi 1.5 bisa dari na habakar tattalin arzikin wurin. Haka kuma rahotanni na cewa, kasar Italiya, wadda daya daga cikin kasashe membobin kungiyar G7, ta bayyana niyyarta ta shiga cikin ayyukan shawarar "Ziri daya da hanya daya", kuma a karshen watan Afrilun bana, wasu karin shugabannin kasashe da kusoshin gwamnatoci daban-daban za su zo kasar Sin don halartar babban dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar kasa da kasa ta fannin shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu. Wang Yi ya jaddada cewa, duk wadannan abubuwa sun shaida cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" ba "tarkon bashi" ba ne, dama ce ga ci gaban kowace kasa.
Amma abun bakin-ciki shi ne, har yanzu akwai wasu kasashen da suke nuna kiyayya ga kasar Sin gami da shafawa kasar Sin kashin kaji, wadanda ke ikirarin cewa, wai za su yanke alaka da kasar Sin, har ma sun yi barazana ga sauran kasashe don kawo cikas ga bunkasuwar kasar Sin cikin lumana. Game da wannan batu, Wang Yi ya bayyana a fili cewa, katse hulda da mu'amala da kasar Sin, tamkar katse dama ce da ma makoma, sannan katse hulda ce da duniya baki daya.
Sakamakon matakan da wasu kasashe suka dauka a kanta, kasar Sin tana karfafa gwiwar kamfanoni da daidaikun mutane da abin ya shafa, su dauki matakai bisa doka don kare muradunsu. Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ba ta saba matsawa kowa lamba ba, kuma neman mallakar duniya sakamakon nuna karfi shi ma ba hanya ce da Sin za ta yi amfani da shi ba. Ko da yaushe kasar Sin na tsayawa kan girmama mabanbantan al'adun juna, da neman zama tare ta hanyar lumana a tsakaninta da kasashe daban daban, da neman hada kai da kasashen duniya don cimma nasara tare.
A hakika, bunkasuwar kasar Sin cikin lumana na kara samun amincewa daga wajen kasashen duniya. Binciken baya bayan nan da wasu hukumomin binciken ra'ayin jama'a na kasashen Jamus da Amurka suka yi, ya nuna cewa, jama'ar Turai da Amurka suna ganin cewa, sun fi amincewa da kasar Sin. A yayin taron tsaro na Munich da aka kammala ba da dadewa ba, wasu masharhanta da yawa na Turai da Amurka sun bayyana cewa, ya zama dole Turai ta gaggauta hada kai tare da kasar Sin kan aikin tafiyar da harkokin duniya. Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ita ma ta ce, idan kasarta ba ta kulla alaka mai kyau tare da Sin, to zai yi wahala ita kadai ta kiyaye matsayinta a duniya. Frank Sieren, wakilin jaridar Handelsblatt ta kasar Jamus ya nuna cewa, yanzu tsarin duniya na fuskantar sauyi, bisa wannan yanayin da ake ciki, tattaunawa tare da kasar Sin shi ne mafi muhimmanci maimakon tattaunawa da Amurka a wasu fannoni.
Sinawa na da ra'ayin "Duniya tamkar al'umma guda". Akwai dalilin da ya sa mutane suka amince da kasar Sin, wadda ke tsayawa kan neman ci gaba ta hanyar lumana, da martaba ra'ayin hadin kai na samun nasara tare, da kiyaye tsari da dokokin kasa da kasa da ake amfani da su a halin yanzu, da karfafa daukar nauyi kan harkokin duniya, kasar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiyar duniya, da ciyar da rayuwa da makomar dan Adam gaba. (Sanusi Chen, Bilkisu Xin, Murtala Zhang)