Bisa rahoton ayyukan gwamnati da firaministan kasar Li Keqiang ya gabatar wa majalisar wakilan jama'ar kasar wato NPC don dubawa, a bana kasar Sin za ta zurfafa yin kwaskwarima kan harajin da ake biya saboda karuwar ingancin kaya, inda za a rage yawan haraji da za a biya a wasu sana'o'i, ciki har da masana'antun kere-kere daga kashi 16 cikin dari da ake biya a baya zuwa kashi 13 cikin dari, kana za a rage yawan harajin da za a biya kan wasu sana'o'i kamar sufuri da masana'antun gine-gine da dai sauransu daga kashi 10 cikin dari a yanzu zuwa kashi 9 cikin dari. A sa'i daya kuma, za a rage kudin da mazauna birane da garurruwa za su biya kan gidauniyar inshora. Rahoton ya nuna cewa, shirin zai taimaka wajen rage harajin da masana'antu za su biya da kudin da jama'a za su biya bisa kan ba da tabbaci ga zamantakewar al'umma da yawansu zai kai kusan RMB triliyan 2.
A farkon bana, kasar Sin ta fitar da jerin manufofin rage harajin da dukkan matsakaita da kananan kamfanoni za su biya a cikin shekaru 3 masu zuwa. A waje daya, bisa wannan manufar rage haraji, an sassauta ma'aunan wadanda za su iya zama kananan masana'antu ko kamfanoni.
A bayyane yake cewa, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wadannan jerin manufofi ne bisa hakikanin halin da kasar take ciki a fannin neman ci gaba. A duk fadin duniya ma, yanzu tattalin arziki na samun ci gaba sannu a hankali, baya ga tattalin arzikin yankunan dake amfani da kudin Euro da ke fama da koma baya, tattalin arzikin kasar Amurka ma ya shiga hali mai sarkakiya. Haka kuma, akwai wasu al'amura iri iri, kamar batun ficewar Burtaniya daga EU, rigingimun cinikayya da ake yi tsakanin Sin da Amurka da dai makamatansu. A nan kasar Sin kuwa, tattalin arzikinta yana fama da matsin lamba sosai, dole ne a yi rigakafin aukuwar duk wasu hadura da ka iya kunno kai. "Haduran da ake ganin za su iya faruwa, ko wadanda ba san ko za su iya faruwa ko a'a, suna nan dare da mu, dole ne mu yi cikakken sharin tunkararsu su gaba daya."
Matakin da kasar Sin ta dauka wajen rage haraji da kudin inshorar da ake biya zai taimakawa ci gabanta, musamman ma ci gaban manyan kamfanoni, kana matakin zai samar da karin guraben aikin yi ga al'ummar kasar, tare kuma da kara adadin kudin shigar al'ummar kasar, ban da haka kuma, matakin zai kara kyautata harkokin sayayya a kasar, zai kuma rage dogaron tattalin arzikin kasar Sin kan fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje. Game da masu zuba jari ko wadanda za su zuba jari a kasar Sin da suka zo daga kasashen waje kuwa, idan sun samu rangwame kamar wadda ake baiwa Sinawa, za su ci gajiyar matakin gwamnatin kasar Sin.
A cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta cimma burin samu saurin ci gaban tattalin arziki da ba taba gani a tarihin dan Adam, da mutane kusan miliyan 800 da aka kawar daga talauci. Yanzu kasar ta shiga wani mataki na samun ci gaba mai inganci, kana tana gamuwa da kalubale. Ga alama, matakan da Sin ta dauka na rage yawan haraji da yawan kudin da jama'a za su biya kan ba da tabbaci ga zamantakewar al'umma za su karawa masana'antu da jama'ar kasar karin gwiwa, hakan zai ba da tabbaci ga kasar wajen tabbatar da burinta na samun karuwar tattalin arziki na kashi 6 zuwa 6.5 cikin dari. (Masu fassarawa: Bilkisu Xin, Sanusi Chen, Jamila Zhou, Ma'aikatan sashen Hausa)