in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun yaba da rahoton aikin gwamnatin kasar Sin
2019-03-06 10:44:39 cri

Firayin ministan kasar Li Keqiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnatinsa ga taro na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 13 jiya Talata, a madadin majalisar gudanarwar kasar Sin. Rahoton da ya samu yabo matuka daga bangarorin siyasa da 'yan kasuwa da malamai na kasashen waje, inda suka bayyana cewa, da kasar Sin ta yi namijin kokari a cikin shekarar da ta gabata, wanda ya kaita ga samu sakamako mai kyau. kana sun yi fatan sauran kasashen duniya za su ci gajiya daga ci gaban kasar Sin.

A cikin rahoton aikin gwamnatin kasar Sin, an yi nuni da cewa, a cikin shekarar 2018 da ta gabata, al'ummar kasar ta kabilu daban daban sun yi kokari matuka karkashin jagorancin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, bisa tushen tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki. Haka kuma, sun cimma muhimman muradun raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma da aka tsara, tare kuma da samun sabon ci gaba wajen gina al'umma mai matsakaicin karfi.

Darektan cibiyar nazari kan harkokin kasar Sin ta tarayyar Najeriya Charles Onunaiju ya bayyana cewa, har kullum, gwamnatin kasar Sin ta kan warware matsalolin da take fuskanta a kan lokaci, haka kuma tana cike da imanin cewa, tana iya samar da kyakkyawar rayuwa mai wadata ga al'ummar kasarta, tare kuma da daga matsayin al'adu a fadin kasar.

Shugaban cibiyar nazari kan harkokin kasar Sin ta jami'ar Sunkyunkwan ta kasar Koriya ta Kudu Lee Hee-ok ya bayyana cewa, a cikin shekarar 2018, duk da cewa tattalin arzikin duniya ya gamu da matsalar rashin tabbas, kasar Sin ta yi namijin kokarin da ya kai ta ga samun babban sakamako.

Shi kuwa mataimkin magajin birnin Antwerpen na kasar Belgium Ludo Van Campenhout, cewa ya yi, a cikin shekarar da ta gabata, yanayin da kasashen duniya ke ciki yana da sarkakiya, amma kasar Sin ta cimma muradun raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma da ta tsara yadda ya kamata, kana saurin karuwar tattalin arzikin kasar ya ba su mamaki matuka.

A nata bangaren, shugabar rukunin masanan tattalin arziki wato The Economist Groug a takaice Liu Qian ta bayyana cewa, gyaran fuska kan tsarin tattalin arziki da kasar Sin ta yi a bara ya jawo hankalin al'ummomin kasashen duniya. Ta ce an lura cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri a bara, lamarin da ya nuna cewa, kasar tana da karfi a asirce a fannin, wanda shi ma ya nuna cewa, ci gaban kasar Sin zai taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya.

Kana rahoton ya nuna cewa, an tsara shirin karuwar GDP da kaso 6%-6.5% a shekarar 2019, kuma kasar Sin za ta kara habaka kasuwa a cikin gida, domin biyan bukatun al'ummarta.

Darektan cibiyar nazari ta rukunin Al Jazeera na kasar Qatar Mohamadu ya nuna cewa, kasashen duniya suna dora muhimmanci sosai kan manufofin tattalin arzikin kasar Sin, saboda idan kasar Sin ta ci gajiya daga gyaran fuskar tattalin arziki, sauran kasashen duniya ma za su ci gajiya. Wato ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya.

Darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta kasar Brazil Ronnie Lins ya ce, gwamnatin kasar Sin tana yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arzikinta, musamman ma a fannin samar da kayayyaki da kara habaka kasuwa a kasar, wadannan suka ingiza bukatun gida, tare kuma da samar da karin guraben aikin a kasar.

Shehun malamin cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta kasar Afirka ta Kudu, Cobus Van Staden ya bayyana cewa, sabon matakin da kasar Sin ta dauka wato ingiza ci gaban sana'ar kere-kere mai inganci zai ciyar da sana'ar gaba cikin sauri.

Ban da wannan, rahoton ya nuna cewa, yanzu kasar Sin tana cike da kuzarin kirkire-kirkire, kuma burin al'ummar kasar na kyautata rayuwarsu yana da karfi matuka, a don haka, gwamnatin kasar Sin tana da babbar niyyar dakile daukacin matsalolin da take fuskanta yayin da take kokarin raya tattalin arzikin kasar.

Mataimkain magajin birnin Antwerpen na kasar Belgium Ludo Van Campenhout yana cike da imani kan karuwar tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba, ya ce, idan ka je kasar Sin, ko ina za ka ga Sinawa suna aiki, ko shakka babu kasar Sin za ta ci gaba da samun karuwar tattalin arziki cikin sauri.

Darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta tarayyar Najeriya Charles Onunaiju ya ce, kasar Sin tana kara bude kofa ga kasashen wajen, hakan ya tabbatar da cewa, ana hada tattalin arzikin kasar Sin da tattalin arzikin duniya yadda ya kamata, kuma a bayyane yake cewa, wadatar kasar Sin za ta amfanawa sauran kasashen duniya baki daya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China