in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ta sa niyyar yin namijin kokarinta na neman ci gaba mai inganci
2019-03-05 17:08:05 cri

A cikin rahoton da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatarwa taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar, wato hukumar kolin tafiyar da kasa ta kasar, game da ayyukan da gwamnatinsa ta yi a bara da kuma za ta yi a bana, an bayyana cewa, muhimman burikan da gwamnatin kasar Sin take son cimmawa a bana wajen bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar su ne, saurin bunkasar tattalin arzikin kasar GDP zai kai 6% zuwa 6.5%, sannan samar da sabbin guraben aikin yi fiye da miliyan 11 a garuruwa da birane, farashin kayayyakin masarufi zai karu da wajen 3%, za a yi kokarin kubutar da mutanen dake zaune a yankunan karkara fiye da miliyan 10 daga kangin talauci, har ma yawan makamashin da ake amfani da shi domin samar da kayayyaki zai ragu da wajen 3%.

A lokacin da saurin bunkasar tattalin arzikin duniya yake raguwa, kasar Sin tana fuskantar haduran da suke shiga kasar daga waje, har ma tattalin arzikin kasar bai samu ci gaba kamar yadda ake fata ba, wadannan burikan da gwamnatin kasar Sin ta kafa sun yi daidai da hakikanin halin da kasar ke ciki, kuma za su iya biyan bukatun da ake da su domin neman bunkasuwa. Za su taimakawa kasar wajen neman ci gaba mai inganci ba tare da wata tangarda ba.

Ka'idojin bunkasar tattalin arziki sun bayyana cewa, ba zai yiyu wata kasa ta iya bunkasa tattalin arzikinta cikin sauri a kullum ba, tabbas ta rika samun ci gaban tattalin arzikinta sannu a hankali. Sannan bayan da tattalin arzikin wata kasa ya samu ci gaba har ma ya kai wani matsayi, dole ne a canja salon bunkasa tattalin arziki domin neman ci gaba mai inganci.

Bisa matsayinta na kasa mafi saurin ci gaban tattalin arziki ta biyu a fadin duniya, adadin GDP na kasar Sin ya zarta trilliyan 90 a shekarar 2018 da ta gabata, yanzu haka tana kokarin ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arzikinta mai inganci a maimakon samun ci gaba cikin sauri.

Idan ana son samun ci gaban tattalin arziki mai inganci, ya dace a cimma burin samun ci gaba mai dorewa, ta hanyar kara habaka boyayyen karfi da kuzuri da karfin goyayya a fannin ci gaban tattalin arziki, amma ba mai da hankali kan karuwar adadin GDP kawai ba. Bisa shirin da aka tsara, an yi hasashen adadin karuwar GDP na bana ba zai kai na bara ba, dalilin da ya sa haka shi ne, gamuwa da matsala da aka yi yayin da ake kokarin habaka cudanyar tattalin arziki a fadin duniya, kana an gamu da matsalar rigingimun cinikayya wadda ke kara tsanani, a don haka, zai yi wuya a samu ci gaban tattalin arzikin duniya, a karkashin irin wannan yanayi, hukumomin kasa da kasa da dama su ma sun rage adadin karuwar tattalin arziki a fadin duniya, shi ya sa gwamnatin kasar Sin ita ma ta rage adadin karuwar tattalin arzikinta domin dakile matsalolin da take fuskanta, ta yadda za ta cimma burin samun ci gaban tattalin arzikinta mai inganci.

Kana ya kamata a lura cewa, an yi hasashe kan karuwar adadin GDP tsakanin 6%-6.5% a nan kasar Sin ne bisa tushen na yanzu wato ci gaban tattalin arziki mai saurin gaske.

Yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana da girma a duniya, don haka idan ya karu da wani kaso, zai zama mai yawa sosai idan aka dubi adadinsa. Saboda haka ana ganin cewa ba wani laifi ba ne a kiyaye saurin karuwar tattalin arziki na kashi 6% zuwa 6.5% a kasar. Masanan ilimin tattalin arziki sun ce wannan karuwar ta kasance cikin wani yanayi mai kima, kuma har yanzu kasar Sin tana sahun gaba tsakanin manyan tattalin arzikin duniya a fannin samun karuwa, har ila yau tana taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya.

Don cimma burikan da aka sanya, wadanda muka ambata a baya, gwamnatin kasar Sin ta jera wasu ayyukan da za ta mai da hankali kansu a bana, wadanda suka hada da kara kirkiro sabbin fasahohi, da daidaita manyan tsare-tsaren kasar, da baiwa 'yan kasuwa muhalli mai kyau wajen gudanar da harkokinsu, da tabbatar da amfanin sabbin fasahohi ta fuskar jagorantar ci gaban tattalin arziki, da inganta kasuwannin gida, da kara kokarin rage talauci da raya kauyuka, da neman daidaita ingancin tattalin arzikin wurare daban daban, da magance gurbatar muhalli,da kyautata muhallin halittu, da zurfafa gyare-gyaren da ake yi a wasu manyan fannoni masu muhimmanci, da kara bude kofa ga kasashen waje, da raya harkoki masu alaka da zaman al'umma, da dai makamantansu.

Dukkan wadannan manyan ayyuka sun shafi wasu burikan da aka sanya, gami da bukatun da aka tanada. Bisa wannan shiri za a iya ganin cewa, tattalin arzikin kasar Sin na kara samun inganci, inda yake kara nuna wata halayyar musamman, wadda ta kunshi fannonin "kirkiro sabbin fasahohi, da samun daidaituwa, da kare muhalli, da bude kofa, gami da sanya kowa ya amfana". Wadannan fannoni sun shaida yadda tattalin arzikin wata kasa ke samun ci gaba mai inganci.

A bana ake cika shekaru 70 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. Ko da akwai rashin tabbas a yanayin da ake ciki a duniya, ana ba wa kasar Sin babbar damar samun ci gaba, ganin yadda take da babban sirrin bunkasuwa da sabon karfin kirkire-kirkire, da babban burin jama'arta na neman jin dadin zaman rayuwa, har ma da kwarewarta ta ci gaba da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikinta yadda ya kamata cikin dogon lokaci. Duk wadannan sun mara wa Sin baya sosai wajen kara ingancin bunkasarta da raya tsarin tattalin arziki na zamani. Kamar yadda Sinawa kan ce, tsara shiri na da muhimmnaci, amma yadda za a aiwatar da shi ya fi muhimmnaci. Yau gwamnatin kasar Sin ta bayar da rahoton aikinta na bana, babu shakka za ta haye duk wahalhalu da kalubalolin dake gabanta domin gudanar da ayyuka yadda ya kamata bisa namijin kokarinta da ra'ayin kirkire-kirkiren da take da shi, a kokarin raya kyakkyawar makoma. (Sanusi, Jamila, Bello, Kande)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China