in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shekara-shekara na NPC, inda aka gabatar da shirin tafiyar da kasa na shekarar 2019
2019-03-05 15:10:47 cri

A yau Talata da safe, aka bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wato hukumar kolin mulkin kasar a nan Beijing, inda firaministan kasar Li Keqiang ya gabatar da wani rahoto game da ayyukan da gwamnatinsa ta yi a bara, da ayyukan da gwamnatinsa za ta yi a bana. A lokacin da ake tinkarar yanayi mai sarkakiya a ciki da wajen kasar, yaya kasar Sin, kasa ta biyu mafi bunkasar tattalin arziki a duniya za ta ci gaba da bunkasa tattalin arzikinta ba tare da tangarda ba kamar yadda ake fata? Sannan yaya za ta kara aiwatar da manufar ta yin gyare-gyare da bude kofarta ga ketare, da kuma neman ci gaba bisa gyare-gyaren da take yi? Yanzu ga wani cikakken rahoto.

A shekarar 2018, sabuwar gwamnatin kasar Sin ta tinkari yanayi mai sarkakiya da ake fuskanta a ciki da waje da ba ta taba ganin irinsa ba a cikin shekaru da dama da suka gabata, ta kuma samu nasarar cimma wasu burika. Amma, Mr. Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya kuma bayyana a fili, cewar gwamnatinsa ta san matsaloli da kalubalolin da take fuskanta yanzu.

"Dole ne a yi la'akari da hadurran da za su faru a lokacin da ake zaman lafiya. A bana, kasarmu tana fuskantar matsanancin yanayi mai sarkakiya a lokacin da take kokarin neman ci gaba. Dole ne mu fara daukar matakan shawo kansu."

A lokacin da ya tabo batun babban buri da manufofin cimma burin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin a bana, ba ma kawai Li Keqiang ya jaddada cewa za a ci gaba da aiwatar da babbar manufar neman ci gaba ba tare da wata tangarda ba da kuma ci gaba da yin gyare-gyare kan masana'antun da ke samar da kayayyaki ba, ya kuma gabatar da wasu sabbin matakan da gwamnatinsa za ta dauka, alal misali za a hanzarta zamanintar da tsarin tattalin arziki, samar da karin guraben aikin yi da tabbatar da ganin aikin hada-hadar kudi ya samu ci gaba ba tare da wata tangarda ba da dai makamatansu. Li Keqiang ya ce, "A lokacin da ake fuskantar raguwar saurin bunkasa tattalin arziki, dole ne a daidaita huldar dake tsakanin gwamnati da kasuwa, dole ne a kara kokari, idan har ana fatan samun ci gaba a kasuwa bisa kokarin gyare-gyaren da ake yi. Muddin kasuwa tana da karfin samun ci gaba, tabbas za a samu karfin neman samun ci gaba da kuma tinkarar matsin lambar da tattalin arziki ke fuskanta. Dole ne a kara aiwatar da manufofin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, a hanzarta kafa kasuwannin zamani wadanda suke bude kofarsu ga juna, da kuma suke gogayya cikin adalci bisa doka."

Bisa wannan rahoton da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar, an kafa wani muhimmin burin bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin a bana, wato saurin bunkasa tattalin arzikin kasar, GDP zai kai 6% zuwa 6.5%.

A bara, kasar Sin ta shirya manyan bukukuwan murnar cika shekaru 40 da kaddamar da babbar manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare, inda ta sha nanata niyya da imaninta na kara bude kofarta ga ketare. A shekarar farko ta kaddamar da sabon zagaye na yin gyare-gyare da bude kofarta ga ketare, kuma a lokacin da tattalin arzikin duniya yake cikin mawuyacin hali, Li Keqiang ya nuna cewa, "Za a kara jawo jarin waje. Kuma za a kara sassauta sharudan shigar baki 'yan kasuwa kasar Sin, sannan za a samar da karin fannonin da baki 'yan kasuwa za su iya zuba jarinsu. Bugu da kari, za a tabbatar da daukar matakan yin gyare-gyare kan fannin hada-hadar kudi, da kuma kyautata manufofin bude kasuwar neman basussuka, ta yadda za a iya bullo da wani yanayin kasuwanci, inda za a iya yin gogayya cikin adalci. Kuma za a kara kare 'yanci da muradun baki 'yan kasuwa. Tabbas yanayin zuba jari a kasar Sin zai kara samun kyautatuwa, baki 'yan kasuwa wadanda suka zuba jari a kasar Sin za su samun karin damammakin samun ci gaba." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China