A watan Maris na ko wace shekara ce, kasar Sin ke shirya muhimman taruka biyu, wato taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar wato CPPCC a wannan lokaci, baya ga tsara shirin ci gaban kasar Sin, tarukan biyu suna zama wata muhimmiyar kafa ga kasashen duniya wajen sa ido kan kasar ta Sin. A matsayinsa na wani tsari mai halin musamman na kasar Sin, taron CPPCC yana ta kara taka muhimmiyar rawa wajen neman ci gaba, tun bayan aka kafa sabuwar kasar Sin kusan shekaru 70 da suka wuce, kana yana ta hadin kan Sinawa dake ciki da wajen kasar, kuma yana ta inganta kasar Sin wajen kafa abin al'ajabi na neman bunkasuwa.
Hadin kai da demokuradiyya su ne muhimman batutuwa biyu na ayyukan CPPCC. 'Yan majalisar CPPCC sun fito ne daga bangarori daban daban na kasar Sin, don haka suna wakiltar yawancin Sinawa, hakan ya sa kungiyar ta iya hada karfin bangarori daban daban na kasar. Ga misalin, a cikin mambobi sama da 2000 na majalisar CPPCC a wannan karo, wadanda suka fito daga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun kai kashi 39.8 cikin dari, wadanda ba 'yan jam'iyya ba sun kai kashi 60.2 cikin dari. Wasu sun fito daga jam'iyyun demokuradiyya guda 8, da kungiyar 'yan kasuwa da masana'antu ta kasar, da wasu ba su cikin ko wace jam'iyya ba, da wakilai daga sana'o'i daban daban, da wakilai daga yankunan musamman na Hongkong, Macau, da kananan kabilu, da bangaren addinai, da kuma fannonin al'adu da motsa jiki. Akwai kuma wani yanayi na musamman na 'yan majalisar CPPCC, wato wasu 'yan majalisar da yawa kwararru ne a fannoninsu, ga misalin, a cikin 'yan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa a wannan karo, akwai masana fannin kimiyyar kasar Sin da masana fannin injiniyanci na kasar guda 105.
Babban aikin mambobin majalisar CPPCC shi ne bayar da kyawawan shawarwari ga ayyukan neman bunkasuwa na kasar Sin, kuma ya kamata su maida hankali sosai kan yadda za'a yi domin rayawa gami da inganta tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da taimakawa jama'a wajen warware matsaloli da kalubalen dake tattare da zaman rayuwarsu na yau da kullum. Kididdiga ta yi nuni da cewa, tun da aka yi zaman taro na farko na majalisar CPPCC karo na 13, zuwa yanzu, gaba daya an samu daftarorin shirye-shirye 5360 da mambobin majalisar CPPCC suka gabatar, wadanda suka shafi habaka tattalin arziki yadda ya kamata, da yin kwaskwarima ga tsarin siyasar kasar, da aiwatar da harkokin kasa bisa doka da oda, da raya harkokin al'adu, da yaki da fatara da kare muhallin halittu, da kyautata zaman rayuwar al'umma, da fadada mu'amala da cudanyar sada zumunta da kasashen waje da makamantansu, wadanda suka samar da muhimmin tabbaci da goyon-baya ga gwamnatin kasar Sin wajen tsara manufofi.
Majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa, wata muhimmiyar hanya ce da kasar Sin ke bi wajen gina tsarin demokuradiyyar jama'a, kana kuma ba da shawarwari ga harkokin siyasa da sa ido bisa turbar demokuradiyya da kuma shiga cikin harkokin siyasa duk sun nuna kuzarin da tsarin da gurguzu ke da shi. Tun lokacin da aka kira babban taro karo na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya zuwa yanzu, kwamitin tsakiya na jam'iyyar ya dade yana bukatar majalisar CPPCC da ta sa ido kan harkokin don taimakawa jam'iyyar kwaminis aiwatar da muhimman manufofin raya kasa da kyautata zaman rayuwar al'ummar kasar. Haka kuma shawarwarin da mambobin majalisar suka bayar ga ayyukan gwamnatoci a matakai daban-daban suna yin babban tasiri ga harkokin siyasar kasar.
Bana, shekaru 70 ke nan da kafa sabuwar kasar Sin, haka kuma shekaru 70 ke nan da kafa majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, tarihin tsawon shekaru 70 ya shaida cewa, aikin ba da shawara kan harkokin siyasa na majalisar ya kasance dandalin musanyar ra'ayoyi tsakanin gwamnati da al'ummar kasa, ita ma tana ba da gudumowa wajen hadin kan jam'iyyu daban daban a kasar, a bayyane ne tana taka muhimmiyar rawa kan aikin raya kasar ta Sin.
Tsarin demokuradiya ya sha bamban a fadin duniya, a don haka tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da tsarin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa suna taimakawa ga ci gaban tattalin arziki da zaman takewar al'umma a kasar Sin, haka kuma suna samar da tabbaci ga kyakkyawan burin samun wadata na al'ummar kasar, ana iya cewa, sun kasance abin koyi ga sauran kasashe a matsayinsu na masu bin tsarin demokuradiya na bil Adama ta hanyar yin amfani da "cimma matsaya guda" da "hada kai tsakanin al'ummar kasar".(Bilkisu Murtala Jamila)