in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a daddale yarjejeniya ba yayin ganawa karo na 2 tsakanin shugabannin DPRK da Amurka
2019-03-01 10:36:46 cri

Shugabannin kasashen Koriya ta Arewa wato DPRK da Amurka, sun yi ganawa karo na biyu a Hanoi, fadar mulkin kasar Vietnam, ganawar da ta ja hankalin al'ummomin kasashen duniya matuka. Sai dai abun takaicin shi ne, sassan biyu ba su daddale wata yarjejeniya yayin ganawartasu ba, amma shugaban Amurka Donald Trump ya furta cewa, sun samu sakamako yayin ganawar da suka yi cikin kwanaki biyu, wato a ranar Laraba da jiya Alhamis.

Rahotanni sun ce, duk da cewa shugabannin kasashen biyu ba su daddale yarjejeniya bisa shirin da suka tsara ba, ganawar da suka yi ta shaida cewa, suna kokari matuka domin warware batun hana yaduwar makaman nukiliya a zirin Koriya.

Da farko, tun bayan da shugabannin biyu suka yi ganawa karo na farko a kasar Singapore a watan Yunin shekarar bara, sassan biyu wato Koriya ta Arewa da Amurka, sun cimma burin kara zurfafa fahimtar juna a tsakaninsu, hakan ya aza harsashi mai kyau ga shawarwarin da za su yi a nan gaba.

A sa'i daya kuma, yayin ganawarsu a wannan karo, shugabannin biyu sun tabo batutuwan da suka fi jawo hankalinsu duka, misali shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya bayyana cewa, idan ba zai amince da shirin hana yaduwar makaman nukiliya a zirin Koriya ba, to da ba zai yiyu ya je birnin Hanoi don halartar taron ba. Kana an ba da labari cewa, yayin ganawar, bangaren Amurka ya gabatar da wata shawara cewa, yana fatan za a kafa wani ofishin kasar a Pyongyang, fadar mulkin kasar Koriya ta Arewa, inda bangaren Koriya ta Arewa shi ma ya yarda da shawarar nan take.

Ban da haka, bayan ganawarsu, kakakin fadar White House ta Amurka ya fitar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa, shugabannin Amurka da Koriya ta Arewa sun yi ganawa mai ma'ana, har sun tattauna kan batutuwa da dama wadanda ke shafar hana yaduwar makaman nukiliya a zirin Koriya da kuma harkokin tattalin arziki, a don haka sassan biyu suna sa ran cewa, za su ci gaba da gudanar da irin wannan shawarwari a nan gaba. Ana ganin cewa, duk da cewa, ba su daddale yarjejeniyar ba yayin ganawar ta wannan karo, kila za su cimma burin a nan gaba.

Batun hana yaduwar makaman nukiliya a zirin Koriya ya shafe tsawon shekaru sama da goma, shi ya sa ba zai yiyu a daidaita shi cikin gajeren lokaci ta hanyar gudanar da ganawa sau daya ko biyu kawai ba. sakamakon da aka samu a halin yanzu shi ma ya nuna cewa, batun yana da sarkakiya matuka.

Hakika Koriya ta Arewa ta damu sosai kan tsaron kasarta, akwai bukatar a tabbatar da tsaronta kafin ta tsai da kudurin dakatar da amfani da makaman nukiliya, amma a cikin shekarun baya bayan nan, gwamnatin Koriya ta Arewa ta riga ta sanar da cewa, tana son warware batun bisa bukatun kasashen duniya, a maimakon haka, za ta kara mai da hankali kan aikin raya tattalin arzikin kasar. kana tun bayan shekarar 2017, Koriya ta Arewa ta daina gwajin kera makamai masu linzami ko makaman nukiliya, lamarin da ya aza harsashi mai kyau ga shawarwarin dake tsakaninta da Amurka, wanda ya nuna cewa, Koriya ta Arewa ta yi kokari a fannin.

Daga sakamakon da sassan biyu suka samu a cikin shekaru biyu da suka gabata, an lura cewa, shawarwari ita ce hanya daya da ta dace da warware batun yaduwar makaman nukiya a zirin Koriya.

Kwanan baya mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi shi ma ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan Koriya ta Arewa da Amurka za su ci gaba da yin tattaunawa a tsakaninsu, ta yadda za su cimma burin kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya daga duk fannoni, tare kuma da kafa wani tsarin shimfida zaman lafiya a zirin, yana mai cewa kasar Sin ita ma tana son ba da gudumowarta kan batun.

Hakazalika, ana sa ran kasashen duniya za su nuna goyon bayansu domin taimakawa da kuma ingiza shawarwarin dake tsakanin sassan biyu, ta yadda za a warware batun hana yaduwar makaman nukiliya a zirin yadda ya kamata, tare kuma da kawo wadata da kwanciyar hankali mai dorewa ga yankin arewa maso gabashin nahiyar Asiya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China