in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An daidaita batutuwan da aka gabatar dubu goma yayin taruka biyu na 2018
2019-02-28 11:12:07 cri

A gabannin taruka biyu wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da taron bada shawara kan harkokin siyasa na kasar na shekarar 2019, wakilinmu ya samu labari cewa, hukumomi daban daban na majalisar gudanarwar kasar Sin sun daidaita shawarwari 6319 da wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar suka gabatar da batutuwa 3863 da mambobin majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar suka gabatar, adadin da ya kai kaso kusan 90 bisa dari dake cikin daukacin shawarwari da batutuwan da aka gabatar a yayin taruka biyu na shekarar bara wato 2018, lamarin da ya sa kaimi kan ci gaban kasar a fannoni daban daban.

Bisa alkaluman da aka samar, an lura cewa, adadin shawarwari da batutuwan da aka gabatar yayin taruka biyu na shekarar 2018 wadanda hukumomin majalisar gudanarwar kasar Sin suka daidaita yafi yawa matuka har ya kai kaso kusan 90 bisa dari, mataimakin shugaban babbar hukumar kwastam ta kasar Zou Zhiwu ya bayyana cewa, adadin shawarwari da batutuwan da babbar hukumar kwastam ta gabatar a bara ya kai 207, yawancinsu suna shafar kyautata aikin shigi da fici, misali rage lokacin shigo da kayayyaki daga ketare, ko rage lokacin fitar da kayayyaki zuwa ketare, ko kuma saukaka aikin gabatar da takardun da abin ya shafa yayin da ake gudanar da aikin shigi da fici, ko kuma rage kudin da ake bukata yayin da ake shigo da kayayyaki kasar daga ketare ko fitar da kayayyaki zuwa ketare, abu mai faranta rai shine hukumomin da abin ya shafa na hukumar kwastam sun daidaita daukacin su a kan lokaci, lamarin da yasa wakilai da mambobi wadanda suka gabatar da shawarwari da batutuwa sun nuna gamsuwarsu matuka, a sa'i daya kuma, an daga matsayin cinikayya tsakanin kasa da kasa na kasar Sin cikin nasara, Zou Shiwu yana mai cewa, "A shekarar bara da ta gabata, babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta yi kokari domin kyautata aikinta bisa bukatun wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da mambobin majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar, tare kuma da samar da muhallin kasuwanci mai inganci ga 'yan kasuwar fadin duniya, misali lokacin da aka rage yayin da ake gudanar da aikin shigo da kayayyaki daga ketare ya kai kaso 56 bisa dari, haka kuma lokacin da aka rage yayin da ake gudanar da aikin fitar da kayayyaki zuwa ketare ya kai kaso 61 bisa dari."

Mataimakin babbar hukumar sa ido da tafiyar da harkokin kasuwa ta kasar Sin Tang Jun ya bayyana cewa, gaba daya babbar hukumar ta daidaita shawarwari da batutuwa na taruka biyu na bara har suka kai 560, ya kara da cewa, babbar hukumar ta sanya kokari matuka domin daidaita wadannan shawarwari da batutuwan da aka gabatar, lamarin da ya ingiza kyautatuwar gyaran fuska kan tsarin kasuwancin kasar da muhallin kasuwanci a kasar, yana mai cewa, "Mun yi kokari domin warware matsalolin dake cikin aikinmu, misali mun dakatar da aikin neman samun iznin kafa kamfani, da aiwatar da shirin da aka tsara kafin lokaci, da kuma sanar da bukatun gwamnati ga kamfanoni tare kuma da bukatar kamfanoni su yi alkawari kan aikinsu, a sa'i daya kuma, mun yi kokarin rage lokacin da ake bukata kan aikin tantance iznin kafa kamfanoni, ya zuwa karshen bara, an riga an rage lokacin daga kwanakin aiki 20 zuwa kwanakin aiki 8 a manyan biranen kasar, yanzu kuma zamu kara sanya kokari domin habaka aikin har zuwa duk fadin kasar ta Sin."

Tang Jun ya ci gaba da cewa, bayan kokarin da ake, muhallin kasuwancin kasar Sin ya kyautata a bayyane, a cikin sabon rahoton da bankin duniya ya fitar, an ce, muhallin kasuwancin kasar Sin ya kai matsayi na 46 dake cikin kasashen duniya da yawansu ya kai 190, kana a fannin saukin kafa kamfani kuwa, kasar Sin ta kai matsayi na 28 a ciki.

Mataimakin ministan kiyaye muhallin kasar Zhuang Guotai ya bayyana cewa, kyautata gurbatacciyar iska aiki ne da ya fi jawo hankalin jama'a. shima batu ne da ya fi jawo hankalin wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar da mambobin majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar, a don haka shawarwari da bututuwan da suka gabatar yayin taruka biyu a bara suna shafar aikin kyautata tsarin masana'antu, haka kuma sun nuna fatansu cewa, ya dace a kara kyautata aikin kiyaye muhalli ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani, Zhuang Guotai yana mai cewa, "An kaddamar da bincike kan dalilin aukuwar gurbatacciyar iska da yadda za a tinkatar matsalar, musamman ma a yankuna Beijing da Tianjin da kuma lardin Hebei, yanzu haka an riga an samu sakamako bisa mataki na farko."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China