in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shafin CRI Online ya fara tattara hotuna masu taken "muna tare"
2019-02-28 15:37:57 cri

Tun daga ranar 28 ga watan Fabrairun bana, shafin CRI Online ya fara tattara hotuna masu taken "muna tare" a hukumance daga wajen masu shiga shafin yanar gizo a fadin duniya baki daya.

Makasudin shirya gasar shi ne,nuna sakamakon da aka samu yayin da ake aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta hanyar daukan hotuna, tare kuma da bayyana ainihin ma'anar shawarar wato gudanar da hadin gwiwa cikin kwanciyar hankali, da yin hakuri da juna ba tare da rufa rufa ba, da koyon fasahohi tsakanin juna, da samun moriya tare. Kana ana sa ran gasar za ta nuna wa al'ummomin kasashen duniya sabbin sauye-sauyen da suka faru a kasar Sin, da ma kasashen da suka shiga shawarar, da kuma sada zumunta da cudanyar al'adu tsakanin al'ummomin kasashen.

Za a gudanar da gasar ne tsakanin ranakun 28 ga watan Fabrairu da 10 ga watan Afililu, kuma za a kammala tattara hotuna kafin ranar 28 ga watan Maris, kana za a sanar da sakamakon gasar ne a ranar 10 ga watan Afililun.

Masu shiga shafin yanar gizo wadanda suke son shiga gasar suna iya tura hotunan zuwa ga adireshinmu na E Mail wato withyou2019@qq.com, haka kuma suna iya duba cikakken bayanin dake shafar gasar a shafin: www.cri.cn/withyou

Hotunan da za ku dauka za su shaida tarihin cudanyar sada zumunta dake tsakanin bil Adama a karni na 21.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China