A wajen taron manema labarai da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya, Mista Wang ya ce, a yayin da take kokarin magance hadduran da ake fuskanta, gwamnatin kasar Sin tana nuna himma da kwazo wajen kara bude kofarta ga kasashen ketare don sanya sabon kuzari ga kasuwar kudin kasar, da inganta karfin yin takara na kasar ta fannin harkokin kudi. A baya, kasar Sin ta bullo da wasu jerin muhimman matakai 15, don fadada bude kofarta ga kasashen waje, inda a cewar Wang Zhaoxing, ana tabbatar da aiwatar da wadannan matakai yadda ya kamata.
Har wa yau kuma, baya ga wadannan matakai 15, wasu hukumomin kasar Sin na kokarin nazarin wasu sabbin matakan bude kofa ga kasashen waje.(Murtala Zhang)