in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Amurka suna da moriya iri daya a fannoni 3 na kare 'yancin mallakar fasaha
2019-02-24 17:16:55 cri

A yayin taron tattaunawar batutuwan tattalin arziki da cinikayya karo na 7 da ake yi tsakanin kasashen Sin da Amurka a birnin Washington DC, fadar kasar Amurka, an samu kyakkyawan ci gaba a fannonin kokarin samun daidaiton cinikayya, da aikin gona da musayar fasahohi, da kare 'yancin mallakar fasaha da kuma batun bada hidimomin hada-hadar kudi da dai makamatansu. Daga cikinsu, kan yadda za a iya kara kare 'yancin mallakar fasaha, bangarorin biyu sun cimma matsaya iri daya a fannoni daban daban. Dalilin da ya sa haka shi ne, yanzu "kare 'yancin mallakar fasaha" ya riga ya zama "bukatu ta tilas" ga kowace kasa wadda take kokarin kirkiro sabbin fasahohin zamani. Kasashen Sin da Amurka, da tattalin arzikinsu yake sahun gaba a duk duniya, suna da moriya iri daya a fannoni 3 wajen kare 'yancin mallakar fasaha.

Da farko dai, kare 'yancin mallakar fasaha, bukata ce da kasashen Sin da Amurka dukkansu suke da ita domin kara karfin goggayar tattalin arzikinsu. Wasu sun nuna cewa, 'yancin mallakar fasaha ya kasance wata gadar dake hade kokarin kirkiro sabbin fasahohi da kuma kasuwa. Yanzu ana cikin wani muhimmin hali, wato, a lokacin da ake son canja shekar masana'antu, ana ta fitar da sabbin fasahohin zamani. Sakamakon haka, huldar dake tsakanin bangarorin uku ta kara zama ta kut da kut.

A bangaren Sin, a cikin shekaru 40 da suka gabata bayan kaddamar da babbar manufar bude kofarta ga ketare da yin gyare-gyare a cikin gida, ta riga ta kafa da kuma gyara wasu dokoki, kamar "dokar kare alamar mallaka" da "dokar lambar ciniki" da "dokar wallafe-wallafe". Sannan musamman ta kafa kotun kare 'yancin mallakar fasaha, da kuma yin kwaskwarimar hukumar kula da 'yancin mallakar fasaha. Hakan ya sa, ya zuwa karshen shekarar 2018, yawan 'yancin mallakar fasaha da kowane mutane dubu goma-goma suke da su ya kai 11.5. Sakamakon haka, karo na farko ne kasar Sin ta zama daya daga cikin kasashe 20 wadanda suke sahun gaba wajen kirkiron sabbin fasahohin zamani a duk duniya a shekarar 2018.

Babu shakka, yanzu kasar Sin babbar kasa, amma ba kasa ce mai karfi ba wajen kare 'yancin mallakar fasaha. Sabo da haka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, kara kare 'yancin mallakar fasaha wani muhimmin mataki ne wajen ingiza karfin goggayar tattalin arzikin kasar Sin.

To, yaya za a kara kare 'yancin mallakar fasahar? Kara yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan 'yancin mallakar fasaha wata muhimmiyar hanya ce. Kasar Amurka babbar kasa kuma kasa ce mai karfi wajen kirkiro sabbin fasahohin zamani, sannan tana da cikakkun dokoki da kwararan matakai na kare 'yancin mallakar fasaha. Wannan ya sa kasar Sin ta yi koyi da ita. A lokacin da ake fuskantar sabon ci gaban kimiyya da fasaha, kasar Amurka tana da fifiko, amma tana kuma nuna damuwa, tana fatan za ta iya samun karin kasuwanni a duk duniya ta hanyoyin kare 'yancin mallakar fasaha. Sakamakon haka, a 'yan shekarun baya, sau da dama ne kasar Amurka ta sanya abubuwan kare 'yancin mallakar fasaha a cikin sharudan tattaunawa da ta yi da bangaren Sin, tabbas ne ya zama wani muhimmin batu ga tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da ake yi tsakanin bangarorin biyu.

Ban da wannan kuma, idan an yi bincike kan tsarin ciniki na kasa da kasa, za a gano cewa mutunta 'yancin mallakar fasaha ya riga ya zama wata ka'idar da kowa ke bi. Hakiki wata halayyar musamman ga cinikin kasa da kasa na zamani ita ce dunkulewar tattalin arzikin duniya a waje guda, gami da yadda ake mai da ilimi ya zama kadara. Yanzu kasashen Sin da Amurka a matsayinsu na manyan kasashen tattalin arziki mafi girma a duniya, dake kan gaba a duniya a fannin ciniki, suna da moriyar bai daya ta fuskar kare 'yancin mallakar fasaha.

Na uku, ta hanyar la'akari da huldar ciniki a tsakanin Sin da Amurka, ya kamata dukkansu su yi kokarin kare 'yancin mallakar kadarorin fasaha. Yanzu kasar Amurka ita ce kasar da Sin take fitarwa mafi yawan kayayyakinta, gami da na 6 a duniya da kasar Sin take yawan shigo da kayayyaki daga wajen, yayin da kasar Sin ita ce babbar kasuwar dake karbar karin kayayyakin Amurka, gami da kasar da ta samar da mafi yawan kayayyaki ga bangaren Amurka. Tun da huldar ciniki dake tsakanin kasashen 2 tana da kyau, don haka ana samun karin bukatu a fannin karewa junansu 'yancin mallakar fasaha.

Hakika yadda kasar Amurka ke bukatar kasar Sin don ta kara taimakawa kamfanonin kasar Amurka dake kasar Sin a fannin kare 'yancinsu na mallakar fasaha, ya dace da manufar kasar Sin na gyare-gyaren tsarin tattalin arzikinta. Wani babban jami'i mai kula da aikin kare 'yancin mallakar fasaha na wani kamfani na kasar Amurka mai taken ABRO Industries, William Mansfield, ya bayyanawa kafofin watsa labaru na kasar Sin cewa, kamfaninsa ya taba neman kare ikonsa a fannin mallakar fasaha a kasar ta Sin har sau da yawa, kuma a kowane karo kamfanin ya kan samu biyan bukatunta. Hakan, a cewar jami'in, ya nuna gwamnatin kasar Sin ta dora cikakken muhimmanci kan batun kare 'yancin mallakar fasaha, kana tana girmama kamfanonin kasashen waje bisa la'akari da muhimmiyar rawar da suke takewa a fanin raya tattalin arzikin kasar Sin.

A sa'i daya kuma, a wannan zamanin da muke ciki, karin kamfanin kasar Sin na kokarin raya harkokinsu a kasashen waje, don haka kasar Sin ita ma tana fatan ganin sauran kasashen za su kare 'yancin mallakar fasaha na wadannan kamfanonin kasar Sin. Ta yi la'akari da yadda kamfaonin kasar Sin suke samar da karin sabbin fasahohi, kamata ya yi, kasar Amurka, a nata bangare, ita ma ta karfafa aikinta a fannin kare 'yancin mallakar fasaha na kamfanonin kasar ta Sin.

A hakika, duk wani batu da tawagogin kasashen Sin da Amurka masu kula da batun tattalin arzikin da cinikayya ke tattaunawa, illa dai za su mai da hankali ne kan moriyar bai daya ta kasashen biyu, gami da ta sauran kasashe daban daban, sa'an nan su yi kokarin cimma ra'ayi daya, da takaita sabanin ra'ayoyinsu, to, tabbas za su samu damar zama kusa da burinsu na kulla wata yarjejeniya da za ta tabbatar da moriyar junansu. (Sanusi Chen, Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China