in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu daga cikin amfanin wasannin motsa jiki
2019-02-21 09:41:37 cri


Wasu mutane su kan je wuraren motsa jiki na Gym, ko kuma sassarfa kan tituna, don neman kyautata lafiyar jikinsu, masamman ma domin tabbatar da lafiyar zuciya da ta hanyoyin jini, da samun karin jijiyoyi, tare da neman samun tsarin jiki mai kyau. Ban da wannan kuma, ana ganin cewa, wasan motsa jiki zai iya taimakawa kyautata lafiyar kwakwalwa. A cikin shekaru fiye da 10 da suka wuce, masana na ta kokarin nazarin amfanin wasan motsa jiki a fannin tabbatar da lafiyar kwakwalwa. Sa'an nan sakamakon da aka samu ya nuna cewa, ba tare da la'akari da shekaru ko lafiyar jikin mutum ba, ko dan wasan gudun Marathon ne, ko kuma wadanda ke son yawo a cikin kasuwa kawai, wasan motsa jiki zai taimaka musu a fannin samun lafiyar kwakwalwa, da kwanciyar hankali. Sauran alfanun da ake samu bayan wasan motsa jiki sun hada da kyautata huldar dake tsakanin mutane, da taimaka musu wajen samun karin farin ciki da murna. Yanzu za mu bayyana wasu daga cikin amfani na wasan motsa jiki, wadanda yawancin mutane ba su lura da su ba.

Na farko, wasan motsa jiki yana taimakawa wajen rage matsin lamba da ake ji a zuci.

Idan an dade ana aiki a cikin ofis, dole za a gaji. Wata dabarar da za a iya dauka don kau da gajiyar ita ce motsa jiki, inda za a iya sassarfa, ko kuma gudu a cikin dakin Gym. Wannan wani muhimmin amfani ne dake tattare da wasan motsa jiki,wato rage matsin lambar da ake ji. Bayan an motsa jiki, an yi gumi, kamar duk wani matsin lambar shi ma ya fita daga jikin mutum tare da gumin. Masana sun ce dalilin da ya sa haka, shi ne domin wasan motsa jiki zai sa a samu karin wani sinadari a cikin jini, wanda zai daidaita kwakwalwar mutum, don kada ta mayar da martani fiye da kima ga matsalolin da ake fuskanta.

Wani amfani na biyu dake tattare da wasan motsa jiki shi ne zai farantawa mutum da ransa.

Yadda aka yi gudu har tsawon wata tazara mai nisa ba wani abu ne mai sauki ba, amma ya cancanta, domin yayin da ake kokarin motsa jiki, kwakwalwarmu za ta fitar da wani sanadarin da ake kira "Endorphin", wanda zai farantawa mutum ransa. A wannan zamanin da muke ciki, a kan samu masu kamuwa da cutar damuwa, wato "Depression" a turance. Wasu mutane, yayin da suka je ganin likita, ya kan basu shawarar kara motsa jiki. Saboda a fannin daidaita yanayin zuciya da kwakwalwa, amfanin motsa jiki ya yi daidai da na magunguna. Don cimma burin samun farin ciki, babu bukatar zama a cikin dakunan Gym a ko da yaushe. Abin da ake bukatar kawai, shi ne a motsa jiki sau 3 zuwa 4 a kowane mako, sa'an nan a yi minti 30 ana motsa jiki a duk wuni sau 1, ta haka za a samu damar kiyaye mutum cikin wani yanayi na farin ciki.

Ban da wannan kuma, wani amfanin wasan motsa jiki shi ne yana taimakawa mutum samun karin imani da kansa.

Yayin da ake motsa jiki, a kan ji yadda jiki yake da karfi. Wannan abun da ake ji a zuci zai sa mutum ya samu karin mutunci, da kallon abubuwa cikin karin yakini. Ba tare da la'akari da nauyin jikin mutum, da tsarin jikinsa, da shekarunsa ba, wasan motsa jiki zai sa a fara ganin karfin jikinsa nan take. Za a ga yadda ake samun canji zuwa wani bangare mai kyau bayan dorewa kan wasannin motsa jiki.

Sa'an nan, wani amfani na 4 da ke tare da wasan motsa jiki shi ne, baiwa mutane damar jin dadin zama a wajen daki.

Zaman rayuwar zamani ya sa mutane dadewar zama cikin gida, amma hakika zama a waje, musamman ma motsa jiki a wajen daki, zai taimakawa mutum samun karin mutunci, da kishin kai. Za a iya neman wani irin wasan da ya dace da kai, irinsu hawan dutse, da yawon bude ido, da tuka kwale-kwale, ko kuma gudu a cikin gidan shakatawa. Sa'an nan zama a karkashin hasken rana shi ma zai taimaka wajen rage yiwuwar kamuwar da cutar damuwa.

Ban da wannan kuma, wani amfani na 5 ga wasan motsa jiki shi ne rigakafin tsufar kwakwalwa.

Mutane na tsufa, yayin da kwakwalwarsu ita ma na rashin kaifinta sannu a hankali. Wasu cututtuka irinsa Alzheimer, wato cutar mantuwa, za su iya kashe kwayoyin hallitun kwakwalwa, da haddasa shanyewar kwakwalwar. Duk da cewa motsa jiki da abinci mai gina jiki ba za su taimaka wajen kawar da cutar ba, amma za su iya taimakawa wajen rage saurin lalacewar kwakwalwa, wanda a kan fara fuskanta bayan shekarun mutum sun kai 45. Masana sun ce, dalilin da ya sa ake saukin samun matsalar kwakwalwa bayan da aka tsufa shi ne domin wani bangare mai taken "Hippocampus" dake cikin kwakwalwa, wanda ke kula da ayyukan tunawa da rike abubuwa, yana lalacewa sannu a hankali. Amma motsa jiki zai sa saurin lalacewar ya ragu, musamman ma ga wadanda shekarunsu ke tsakanin 25 zuwa 45.

Sa'an nan, wani amfani na 6 dake tare da wasan motsa jiki, shi ne kau da damuwa.

Jama'a, ko kun san, tsakanin wanka da ruwa mai zafi, da kuma gudu har tsawon mintuna 20, wane zai fi taimakawa kau da damuwar da ake ji? To, amsa ga wannan tambaya watakila zai ba ku mamaki, domin masana sun ce gudu zai fi amfani a wannan fanni. Sun ce, bayan an motsa jiki, cikin jininmu za a samu wani sanadarin da zai taimakawa kwantar da hankalinmu. Sa'an nan gudun da ake yi yana sanya jikinmu ya saba da wani yanayin da ya yi kamar yayin da ake fuskantar wani muhalli mai ban hadari, daga bisani ba za a yi saurin damuwa ba yayin da ake fuskantar wata matsala.

Daga bisani, za mu duba amfanin wasan motsa jiki na 7, wato kara hikima.

Nazari da gwaje-gwajen da aka yi kan bera da mutum sun nuna cewa, wasan motsa jiki, musamman ma wadanda ke sa mutum shakar iska sosai, wato "Cardiovascular exercise" a Turance, zai taimaka wajen samar da sabbin kwayoyin halittu cikin kwakwalwa, ta yadda zai kara hikimar mutum. Ban da haka, yadda ake motsa jiki zai samar da wasu sinadarai masu amfani ga kwakwalwa, wadanda suke taimakawa tunani, yanke shawara, gami da karatu.

Na 8 daga cikin amfanin wasan motsa jiki shi ne taimakawa shawo kan jaraba.

Wasu ayyukan da mutane suke yi za su iya sanya kwakwalwa ta samar da wani sinadarin da ake kira "Dopamine", wanda zai sa mutum jin dadi matuka. Wadannan ayyuka sun hada da cin abinci, da jima'i, da shan giya ko miyagun kwayoyi, gami da motsa jiki. Abin bakin ciki shi ne wasu mutane sun zama masu tsananin bukatar Dopamine, abin da ya sa suka dogaro kan kwayoyi, ko kuma barasa don samun sinadarin. Ga wadannan mutane, motsa jiki shi ne wata hanyar da za a iya bi don taimakawa kawar da jarabarsu. Domin yin motsa jiki zai rage tsananin kwadayinsu kan kwayoyi da kuma giya. Ban da wannan kuma, yadda ake shan giya da yawa ya kan karya al'adar rayuwar mutum, da sanya mutum kasa barci a dare, idan sun daina shan giya. Amma motsa jiki zai iya taimaka musu barci yadda suke bukata.

Sa'an nan na 10 daga cikin amfanin wasan motsa jiki shi ne taimakawa kammala ayyukan ofis.

Idan an gaji wajen kula da ayyukan da ake fuskantar a cikin ofis, wata dabarar da za a iya dauka ita ce a tashi domin a dan yi tafiya ko kuma sassarfa. Nazarin da aka yi ya nuna cewa, wadanda su kan motsa jikinsu sun fi wadanda ba su son motsa jiki kwarewa wajen aikinsu. Kuma ba kasafai su kan gaji sakamakon yin aikin ba. Ko da yake ayyuka da yawa su kan hana mutum zuwa dakin gym, amma masana na ganin cewa, tsakar rana shi ne lokaci mafi dacewa wajen motsa jiki.

To, mun ambaci wasu fannoni na amfanin motsa jiki, ta wadannan bayanai muna sane da cewa, ya cancanci a motsa jiki a kai a kai, idan ana son samun imani da kai, ko farin ciki, ko kuma hikima. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China