in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a cimma burin tabbatar da tsaro ne ta hanyar yin hadin gwiwa kawai
2019-02-18 19:44:53 cri

Jiya Lahadi aka rufe taron kwanaki uku kan harkokin tsaron kasa da kasa karo na 55 a birnin Munich na kasar Jamus, inda kasashe da dama kamar kasar Sin da Jamus da Rasha da sauransu suka gabatar da ra'ayoyinsu wajen nacewa kan manufar martaba juna yayin da ake tafiyar da harkokin kasashen duniya, da ingiza hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya, ra'ayoyin da suka samu karbuwa da goyon baya daga wajen wakilai mahalartan taron matuka.

Mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma darektan sakatariyar kwamitin kula da ayyukan harkokin waje na kwamitin tsakiyar Yang Jiechi shi ma ya halarci taron na Munich, kuma ya gabatar da wani rahoto, inda ya bayyana cewa, martaba juna yayin da ake tafiyar da harkokin kasashen duniya, shi ne zabin yawancin kasashen duniya, hakakinan abubuwa sun shaida cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa ya dace da ci gaban duniya, haka kuma martaba juna yayin da ake tafiyar da harkokin kasashen duniya, shi ne adalcin da ya dace da ci gaban duniya, idan ana son gina kyakkyawar makomar bil Adama, dole ne a nace ga wadannan manufofin. Kana gwamnatin kasar Sin tana ganin cewa, ya zama wajibi a ci gaba da nacewa ga manufofin gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa tare kuma da martaba juna yayin tafiyar da harkokin duniya, ta yadda za a tsara tsarin kasa da kasa mai adalci.

Rahoton da Yang Jiechi ya gabatar, ya nuna cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, ba ma kawai kasar Sin tana aiwatar da manufar harkokin wajenta bisa tushen yin zaman tare cikin lumama ba, har tana yin kokari matuka domin cimma sabon burin gina kyakkyawar makomar bil Adama da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, dalilin da ya sa haka shi ne domin kasar Sin babbar kasa ce ta biyu da tattalin arzikinta ke saurin bunkasa, a don haka ya dace ta kara sauke nauyi dake wuyanta a cikin harkokin duniya, amma duk wadannan ba su nuna cewa, kasar Sin za ta kawo barazara ga sauran kasashen duniya ba.

Wasu na bayyana haka ne domin kasar Sin ta jaddada cewa, dole a yi shawarwari a maimakon nuna kiyayya, ba zai yiyu kasar Sin ta kaucewa tsarin kasa da kasa da aka tsara ba, ta hanyar nuna fin karfi a fannonin aikin soja ko siyasa. Hakika gina kyakkyawar makomar bil Adama ya alamanta cewa, kasar Sin tana son ingiza ci gaban daukacin bin Adama bisa tushen yin zaman tare cikin lumana, kasar Sin tana ganin cewa, idan ana son cimma wannan burin, ya dace a tafiyar da aikin kamar tsarin MDD ya tanada, hakan zai taimaka wajen tafiyar da harkokin duniya bisa doka.

Ana iya cewa, manufar harkokin wajen kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki yanzu ta samu amincewar yawancin kasashen duniya. Yayin taron tsaron Munich na wannan karo, shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ta bayyana cewa, tafiyar da harkokin duniya bisa bangare guda daya zai kawo barazana ga tsarin kasa da kasa, kana ta jaddada cewa, ya kamata a kara mai da hankali kan samun moriya tare, kamar yadda kasar Sin take yi a nahiyar Afirka. Amma a cikin rahoton da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya gabatar a yayin taron, kamar kullum ya jaddada cewa, kasarsa tana da karfi matuka, a don haka ba zai yiyu ba ta canja manufarta, ban da haka Amurka tana fatan sauran kasashen duniya, musamman ma kasashen Turai su bi tsarin munafofinta yayin da suke gudanar da harkokin kasa da kasa, amma wakilai mahalartan taron sun yi tafi yayin da shugaba Merkel take jawabi, sai dai sun yi shiru yayin da Pence yake jawabi.

A bayyane ne an lura cewa, manyan jami'ai wadanda suka halarci taron sun riga sun tsai da kudurinsu kan batun, wato martaba juna, ko son yin hadin gwiwa da kuma tattaunawa a tsakaninsu, kamar yadda shugaba Merkel ta bayyana, kasar Sin ta riga ta nuna sahihancinta ta hanyar taimakawa kasashen Afirka, haka kuma ta nuna wa kasashen duniya sakamakon da ta samu a fannin gina kyakkyawar makoma bil Adama wanda shi ne sabon ra'ayin tabbatar da tsaro a fadin duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China