in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batun makamai masu guba na Syria shiri ne na jabu da kafofin watsa labarun kasashen yamma suka tsara
2019-02-17 20:41:12 cri

A kwanakin baya, an bayar da wani labari mafi janyo hankalin kasa da kasa game da kasar Syria, wato mai tsara shirye-shirye na kamfanin watsa labaru na BBC Riam Dalati ya bayyana cewa, bayan da ya yi bincike har na tsawon watanni 6, ya tabbatar da cewa, bidiyon game da harin makamai masu guba da aka kai a garin Douma dake kasar Syria a watan Afrilu na shekarar 2018, shiri ne na jabu da aka tsara. Kafin hakan, bangaren kasar Rasha da abin ya shafa ya gabatar da wasu batutuwa game da bidiyon na jabu da kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suka tsara. A lokacin, kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa sun kai hari ta sama kan kasar Syria saboda wannan bidiyon.

Abin mai ban mamaki shi ne a kan samu irin wannan labaru na jabu da manyan kafofin watsa labaru da wasu 'yan siyasa na kasashen yammacin duniya suka shirya. Wani batu da kusan kowa ya sani shi ne yakin kasar Iraki na shekarar 2003. A lokacin, gwamnatin kasar Amurka ta kai hari ga wata kasa mai ikon mulki domin wata shaida ta jabu, ba tare da samun izni daga MDD ba. Yakin ya haddasa mutuwar fararen hula na kasar Iraki fiye da dubu 100, tare da mutuwar sojojin kasar Amurka kimanin dubu 10. Amma har zuwa yanzu, babu wani dan siyasa na Amurka ko na Birtaniya da ya fito ya dauki alhakin batun. Kana manyan kafofin watsa labaru na kasar Amurka wadanda suka bayar da wannan labarin ba su nuna shakka ga gaskiyar lamarin ba.

Game da labaran da manyan kafofin watsa labarai na kasashen yamma suka bayar kan kasar Sin, cike suke da karyace-karyace. A 'yan kwanakin baya, kamfanin dillancin labarai na Amurka na CNN ya ba da labari kan wani batun da Mihrigul Tursun, wata 'yar kabilar Uygur ta ganawa idonta, wai an yi garkuwa da mutane 68 a cikin wani dakin da fadinsa ya kai murabba'in mita 37, har ma ta ce wai mutanen da dama sun mutu. Ko da yake abin da ta fada ba gaskiya ba ne, amma kalamanta sun zama muhimmin tushe yayin da dan majalisar dattijan Amurka Mark Rubio da sauransu suka gabatar da dokar da ta shafi manufar hakkin dan Adam na Uygur. Haka zakila ma, bayan da aka tabbatar da cewa, kalaman Mihrigul Tursun karya ne, CNN tana ci gaba da buga labarinta a kan shafinta na Intanet, har ma sauran kafofin watsa labarai suna ta ambatar labarin.

Bugu da kari kuma, a 'yan kwanakin nan, wata kafar watsa labarai ta yammacin duniya ta ba da labarin cewa, shahararren mawaki dan kabilar Uygur Abdurehim Heyit ya mutu a cikin gidan kurkuru, lamarin da ya haddasa zargin da gwamnatin kasar Turkiyya ta yiwa kasar Sin. Amma sabon bidiyon ya nuna cewa, ba ma kawai Abdurehim Heyit yana raye kadai ba ne, har ma yana cikin koshin lafiya. Yayin da yake zantawa da kafofin watsa labarai na kasar Sin, Adnan Akfirat, wakilin jam'iyyar adawa ta kasar Turkiyya ya bayyana cewa, wannan karya ce da hukumomin leken asiri na kasashen yammacin duniya suka yi da gangan, dalilin da ya sa kafofin watsa labarai na Turkiyya suka yi kuskure a kan batun shi ne saboda suna bibiyar kafofin watsa labarai na yammacin duniya kawai, sun bar 'yancin kansu wajen watsa labarai.

Idan an fahimci ainihin ma'anar walwalar watsa labarai ta kasashen yamma, za a lura cewa, hakika yawancin mutanen dake aiki a muhimman kafofin watsa labarai na wasu kasashen yamma, masu fada a ji ne, a don haka ra'ayin da suke dauka kan darajar labarai ya yi daidai da na masu fada a ji na kasashen, misali sun fi son tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na sauran kasashen duniya, kana yayin da 'yan jaridun kasashen yamma suke watsa labaran duniya, sun fi sabawa wajen mayar da kansu a matsayin masu tsarawa da kuma masu kiyaye ma'aunin hakkin dan Adam na kasashen duniya, a sanadin haka, su kan zargi sauran kasashe ko koyar da su yadda suke kiyaye hakkin dan Adam a kasashensu, a maimakon martaba su. Alal misali, yayin da suke watsa labarai game da kasar Sin, su kan gabatar da rahotanni wai "kasar Sin tana kawo barazara ga sauran kasashen duniya" ko "kasar Sin za ta rushe kanta" da sauransu. Yanzu haka shekaru da dama da suka gabata, ba wanda ya ga kasar Sin tana kawowa sauran kasashe barazana, haka kuma ba wanda ya ga kasar Sin ta rushe kanta. Duk wadannan sun nuna cewa, ainihin ma'anar walwalar watsa labarai na kasashen yamma ita ce, shafawa walwalar kasashe masu tasowa kashin kaji kamar yadda suke so.

A halin yanzu, muhimman kafofin watsa labarai na kasashen yamma sun fi kawo tasiri ga al'ummomin kasashen duniya, a don haka akwai wahala al'ummomin kasashen duniya su samu labarai masu adalci. Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Rasha Igor Yevgenyevich Konashenkov ya taba bayyana kan sakamakon binciken da aka yiwa mai tsara shiri na kamfanin BBC Riam Dalati cewa, kasar Rasha ba ta ji mamaki kan batun ba ko kadan, inda ya ce, yanzu ko shakka babu 'yan siyasa da dama na Amurka da wasu kasashen Turai suna yin kokari matuka domin mantawa da lamarin game da harba makamai masu linzami kan kasar Syira bisa dalilin hanawa a kai hari ga al'ummar Syria da makamai masu guba, saboda haka ne za su iya gujewa sauke nauyin harba makamai masu linzami bisa wuyansu a fannonin babban laifi da siyasa da kuma da'a. Kana masu jagorancin kamfanin BBC su ma ba su lura da ra'ayin da Dalati ya dauka ba, har sun bayyana cewa, ra'ayin kansa ne kawai. Ban da haka, kusan daukacin muhimman kafofin watsa labarai na kasashen yamma sun yi shiru kan sakamakon binciken da aka yi kan Dalati, har ba su gabatar da labari ko daya ba.

A sanadin haka, ana tsammani cewa, kafofin watsa labarai na kasashen yamma suna sabawa da yin karya bisa bukatun gwamnatocin kasashensu, bari mu duba me zai faru a nan gaba.(Zainab Kande Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China