in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin cinikin waje da kasar Sin ta yi a watan Janairu ya karu da 8.7%
2019-02-15 11:56:42 cri

A jiya Alhamis, babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar da alkalumai, cewar a watan Janairun bana, jimillar darajar dukkan kayayyakin da kasar Sin ta yi fici da shigin su a watan Janairu ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 2730, wato ya karu da kashi 8.7 cikin dari bisa makamacin lokacin bara, ya wuce hasashen da aka yi a da.

Bisa alkaluman da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayar, an ce, a watan Janairun bana, darajar kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa waje ta kai kudin Sin RMB yuan biliyan 1500, wato ya karu da kashi 13.9 cikin dari. Sannan, darajar kayayyakin da aka shigo da su kasar Sin ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 1230, wato ya karu da kashi 2.9%. Yawan ribar cinikin waje da kasar Sin ta samu ta kai kudin Sin RMB yuan biliyan 271.16, wato ya ninka sau 1.2.

Mr. Bai Ming, mataimakin direktan sashen nazarin kasuwannin kasa da kasa na cibiyar nazarin kasuwanci ta kasar Sin yana ganin cewa, a yanayin raguwar tattalin arzikin duniya da bukatun da ake da su a kasuwannin duniya, har yanzu cinikin wajen kasar Sin yana samun ci gaba mai dorewa kamar yadda ake fata, wannan ba abu mai sauki ne ba. Bai Ming ya kuma bayyana cewa, bikin bazara na murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ma ya yi tasiri ga cinikin waje da aka yi a watan Janairu.

"A farko watan Fabrairu, an fara bikin bazara na murnar sabuwar shekara. Sakamakon haka, galibin kamfanoni sun kammala kwagilolin cinikin waje kafin bikin. A hakika dai, an kammala wasu kwangilolin a watan Janairu maimakon watan Faburairu bisa shirin, wannan ma ya bada gudummawa ga karuwar cinikin waje da muka yi a watan Janairu."

Alkaluman sun kuma bayyana cewa, a watan Janairun, yawan kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa kasashe mambobin tarayyar Turai da ta Asean da Japan ya karu, har ma yawan kayayyakin da ta fitar zuwa kasashen dake yankunan da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shafa ya karu cikin sauri. Amma a bayyane ne yawan kayayyakin da cinikayyar da aka yi tsakanin Sin da Amurka ya ragu fiye da kashi 10% bisa makamancin lokacin bara. Daga cikinsu, yawan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasar Amurka ya karu da 1.9%, amma yawan kayayyakin da take shigowa daga kasar Amurka ta ragu kusan kashi 40%.

Abin da ya kamata a ambata shi ne, yawan kayayyakin da kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin suka fitar zuwa waje a watan Janairu ya karu da kashi 17%, darajar kayayyakinsu da suka fitar waje ta kai kashi 42.3 cikin dari bisa na dukkan kayayyakin da kasar Sin ta fitar a watan. Mr. Bai Ming yana mai cewa, a nan gaba, kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin za su taka karin rawa ga cinikin wajen kasar.

"A 'yan shekarun baya, kamfanoni masu zaman kansu suna taka muhimmiyar rawa a kasuwannin kasa da kasa sakamakon bunkasar tattalin arziki mai zaman kansa a kasar Sin. Yanzu gwamnatin kasar Sin ta fi maida hankali kan yadda za a kara bunkasa kamfanoni masu zaman kansu, alal misali, ta fitar da wasu manufofin kawar da damuwar da wasu kamfanoni masu zaman kansu suke nunawa, da kuma ba su hakikanin goyon baya. A nan gaba, kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin za su kara taka muhimmiyar rawa a fannin cinikin waje."

A kwanan baya, Mr. Chu Shijia, direktan sashen kula da harkokin yau da kullum ta ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, koda yake har yanzu aikin cinikin wajen kasar Sin yana cikin mawuyacin hali, amma akwai wasu kyawawan sharudan da suke kasancewa a kasuwa. Sakamakon haka, ana da imanin tabbatar da ganin cinikin wajen kasar Sin ya samu ci gaba mai dorewa a shekarar 2019.

"Bisa hakikanin halin da ake ciki, yanzu akwai wasu kyawawan sharudan da suke kasancewa ga cinikin wajen kasar Sin. Bangaren daya shi ne, koda yake tattalin arziki na fuskantar matsin lamba sosai, amma yana samun farfadowa sannu a hankali. Daya bangaren na daban shi ne, kasar Sin wadda ta jima tana bin manufar bude kofarta ga waje, ta yi bakin kokarin ta na daukar matakan tabbatar da sa kaimi ga cinikin waje, da hanzarta kyautata tsarin sana'o'i, da kuma karfafa karfin takarar kayayyakin masana'antu da dai makamatansu. Wadannan matakai na nuna goyon baya mai karfi ga cinikin wajen kasar Sin. Saboda haka, muna da imanin tabbatar da ganin cinikin wajen kasar Sin ya samu ci gaba mai dorewa a shekarar 2019." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China