Ministan ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka yi a birnin Budapest.
Peter Szijjarto ya ce kaso 1.2 na abun da Hungary ke fitarwa zuwa nahiyar Turai ne take kaiwa kasar Sin, kuma kamfanonin Jamus da Birtaniya ne manyan abokan huldar Sin a Turai.
Ga Rasha kuwa, Ministan ya bukaci masu sukar Hungary da su daina munafurci, domin kamfanonin Jamus ne suka yi aikin shimfida butuntun iskar gas na Rasha, ba na Hungary ba.
Ya ce an dade ana hadin gwiwar tsaro da tattalin arziki tsakanin Hungary da Amurka, amma an sake kulla sabuwar dangantakar siyasa tsakanin kasashen biyu ne tun bayan da gwamnatin Trump ta fara aiki.
A nasa bangaren, Pompeo ya gargadi Hungary game da kulla alakar kut da kut da Sin da Rasha. (Fa'iza Mustapha)