in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batun kirkire-kirkire da shugaba Xi ya tattauna da al'ummar kasa
2019-02-09 16:34:23 cri


Kirkire-kirkire shi ne muhimmin batu dake cikin yunkurin kasar Sin wajen neman ci gaba cikin sabon zamani. Babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS Xi Jinping ya taba jaddadawa sau da dama a wurare daban daban cewa, "wanda ya yi kwaskwarima zai sami ci gaba, mai yin kirkire-kirkire zai zama mai karfi, kana mai yin kwaskwarima da kirkire-kirkire zai cimma nasara". Me ya sa, ya kamata kasar Sin ta nemi ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire? Kuma ta yadda al'ummar kasar za su cimma burinsu a lokacin nan na yin kwaskwarima? A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da labari na biyar da ke cikin jerin Labaran Yadda shugaba Xi Jinping yake kulawa da zaman rayuwar fararen hula, watau batun yin kirkire-kirkire da shugaba Xi ya tattauna da ma'aikata, shugabannin kamfanoni, da masu aikin kimiyya na kasar.

Shugabar Kamfanin Gree:"Ko kuna murna a yau?"

Ma'aikatan Kamfanin Gree:"Muna murna!"

Wannan babbar muryar murna ce ta ma'aikatan kamfanin na'urorin wutar lantarki na Gree. A lokacin da ya kai ziyarar aiki kamfanin, Babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS Xi Jinping ya yaba matuka da wannan kamfani da kuma ma'aikatansa, sabo da kokarin da suka yi a fannin kirkire-kirkire. Ko da yake, a lokacin farko da aka kafa wannan kamfani, wani karamin kamfani ne na hada sassan na'urar iyakwandishan wato AC. Amma, a halin yanzu, an raya kamfanin Gree zuwa wani babban kamfanin masana'antu, wanda ya kera na'urorin wutar lantarki na yau da kullum da na'urori masu fasahohin zamani da kuma na'urorin sadarwa da dai sauransu, har ya kai ga sayar da na'urorinsa zuwa kasashe da yankuna kimanin 160. Kuma, babbar dabararsa wajen cimma wannan babbar nasara ita ce tsayawa tsayin daka wajen ci gaba da yin kirkire-kirkire.

Xi Jinping ya zaburar da ma'aikatan kamfanin, inda ya ce, ya kamata su dukufa wajen karfafa aikin kirkire-kirkire da kansu, domin neman ci gaba a fannin.

Shugaba Xi: "Daga babbar kasa zuwa wata kasa mai karfi, ya kamata mu mai da hankali wajen raya sana'o'i iri daban daban, masana'antun kira su ne muhimmin tushen raya tattalin arzikin kasa, kana, yin kirkire-kirkire shi ne babban tushen raya masana'antun kira, ya kamata mu dukufa da kanmu, da kuma neman ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire. Ina fatan dukkanin kamfanonin kasar Sin za su dukufa kan wannan aiki."

Ma'aikata: "Tabbas za mu kara kokari, domin kowa yana son kayayyakin da Sin ta kera!"

Kamfanin Inspur shi ne kamfanin dake kan gaba a kasar Sin a fannin fasahohin lissafi da adana bayanai, wanda yake samar da kayayyakin fasahar sadarwa da ba da hidimar abubuwa masu alaka da shi ga kasashe da yankuna da dama. A watan Yunin shekarar 2018, shugaba Xi ya kai ziyarar aiki sansanin sarrafa na'urori masu kwakwalwa na kamfanin Inspur, inda ya saurari bayanan da aka yi masa kan fasahohin sadarwa na zamani. Shugaba Xi ya ce, ya kamata mu inganta ayyukan kirkire-kirkire ta hanyar yin hadin gwiwa da dukufa tare, domin gudanar da muhimmin aiki, hakan kuma, ya dace da tsarin gurguzu na kasar Sin.

Shugaba Xi ya ce, "A halin yanzu, muna kusa da burinmu na farfado da babbar kasa ta Sin, kuma a wannan lokaci, muna fuskantar kalubaloli da matsalolin da ba mu taba gamuwa da su ba. Shi ya sa, ya kamata mu dauki nauyin dake gabanmu, yin hadin gwiwa da kuma gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata, domin raya manyan fasahohi na zamani da kanmu, yin amfani da tsarin gurguzu wajen aiwatar da babban aikin dake gabanmu."

A yankin kimiyya da fasaha na Zhong Guan Cun dake yankin Binhai na birnin Tianjin, akwai kamfanonin fasahohin zamani da dama, wadanda suka hada da kamfanin yanar gizo da kamfanin al'adu da kuma kamfanin magunguna da likitanci mai amfani da fasahar halittu da dai sauransu. Ko da yake, bai wuce shekaru biyu da aka kafa wannan yanki ba, an riga an cimma sakamako da dama a fannin kirkire-kirkire. A farkon shekarar bana, shugaba Xi ya kai ziyarar aiki yankin.

Babban manajan kamfanin kimiyyar jiragen sama maras matuki na Efy Qi Juntong ya yi wa shugaba Xi bayani, kan tsarin tuka jiragen sama maras matuki da kamfaninsa ya kera, wanda ke kan gaba cikin kasashen duniya, ya kuma bayyana cewa, "Manufofin da kasar ta fidda sun baiwa masu nazari da hukumomin nazari kwarin gwiwa wajen karfafa ayyukansu na yin kirkire-kirkire, tabbas za mu cimma burikanmu."

Shugaba Xi ya ce, a halin yanzu, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar suna nazari kan manufofin da abin ya shafa domin samar da yanayi mai kyau wajen raya harkokin yin kirkire-kirkire.

Ya kara da cewa, "Yin kirkire-kirkire shi ne tushen neman ci gaba mai inganci, kuma muna dogaro kan yin kirkire-kirkire wajen raya kasa. Ya kamata mu ci gaba da dukufa wajen baiwa masu son yin kirkire-kirkire damammaki masu kyau wajen gudanar da ayyukansu."

Bayan cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 18 da aka yi a shekarar 2012, an fara samun bunkasar sana'o'i daban daban ta hanyar yin kirkire-kirkire a nan kasar Sin. To yaya a nan gaba kuma, za a ci gaba da samun bunkasar wannan fanni? Shugaba Xi Jinping ya ce, "Ko shakka babu, mun cimma nasarar yin kirkire-kirkire karo daya bisa kasawa da dama da muka yi. Amma ya kamata mu kara himmar kirkire-kirkire, mu dukufa wajen warware dukkan matsalolin dake gabanmu ta yadda za mu cimma nasara a karshe. " (Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China