in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Buhari ya taya shugaban Xi murnar sabuwar shekarar Sinawa
2019-02-03 20:06:35 cri

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya taya takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, murnar zuwan sabuwar shekarar Sinawa bisa kalandar gargajiyar kasar.

Cikin wata wasikar da shugaban na Najeriya ya sanyawa hannu, wadda kuma mai ba shi shawara a fannin watsa labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce a duk fadin duniya, zagayowar sabuwar shekara lokaci ne na murna tare da abokai, da 'yan uwa, da abokan arziki, don haka a cewarsa "Ina taya al'ummar Sinawa murnar wannan biki".

Kaza lika shugaba Buhari ya bayyana farin cikinsa game da ci gaba, da daukaka da kasar Sin ta kara samu karkashin shugabancin jami'iyya mai mulkin kasar. Ya ce "Na yi matukar farin ciki da dacewar wannan lokaci, da cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin ta zamani karkashin JKS. Karkashin jagorancin wannan jam'iyya, Sin ta samu gagarumin ci gaba, da tarin nasarori, baya ga kyautatuwar rayuwar al'ummun ta. Mai girma Shugaban kasa, ina murnar kasancewa abokin mu'amalarka, da JKS, musamman duba da yadda Sin ke kara yin kyakkyawan tasiri a mataki na kasa da kasa, wanda nahiyar Afirka ke kara amfana da shi karkashin lemar dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC. Hakika na gamsu da ci gaban dangantaka tsakanin Sin da Najeriya, yayin da kuma nake fatan ganin an aiwatar da kudurorin taron FOCAC na birnin Beijing da ya gudana a shekarar 2018". (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China