in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutanen da na fi mai da hankali a kai
2019-02-06 16:07:30 cri





A ko wane lokacin gabannin zuwan bikin bazara na gargajiyar kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping ya kan tafi yankuna masu fama da talauci na kasar, don nuna gaisuwa, kamar yadda ya ce, "a gabannin bikin bazara, mutanen da suka fi jawo hankali na su ne wadanda ke fama da talauci." Idan aka duba ajandar ayyukan yin bincike a cikin kasar Sin na shugaba Xi, ake iya gano cewa, ya ziyarci duk yankuna mafiya fama da talauci a nan kasar Sin, inda ya yi bincike kan hakikanan halin zaman rayuwa da matalauta ke ciki, da sani sosai kan dalilan da suka sanya yankunan ke ci baya a fannin tattalin arziki, kana da tabbatar da burin da za a cimma wajen ayyukan fama da talauci. A matsayin sa na shugaban koli na kasar Sin, sau da yawa Xi Jinping ya jaddada cewa, kada a bar duk wani mutum mai fama da talauci a yayin da muke kokarin kafa zaman al'umma mai matsakacin karfi a dukkan fannoni, "ya kamata mu sanya manoma su ci gajiya sakamakon nasarorin da aka samu wajen yin kwaskwarima." A cikin shirinmu na yau, bari mu gabatar muku da labari na biyu da ke cikin jerin labarai kan yadda shugaba Xi Jinping yake kulawa da zaman rayuwar fararen hula.  


Xi Jinping: "maza nawa ne suka samu mata a bara?"

Guo Jianqun: "Bakwai."

Wannan ne hirar da aka yi a tsakanin shugaba Xi Jinping da Guo Jianqun, shugaban yanki mai cin gashin kai na kabilar Tujia da ta Miao a yammacin lardin Hunan, a yayin manyan tarrukan majalisun biyu na kasar Sin wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar, da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa na jama'ar kasar, wadanda aka shirya a shekarar 2016.

Xi Jinping ya yi tambaya kan yanayin da ake ciki a kauyen Shibadong na gundumar Huayuan a yammacin lardin Hunan, yadda halin aure da mazauna kauyen ke ciki, ya nuna yadda ake gudanar da ayyukan kawar da talauci a yankuna masu fama da talauci. Da ma sakamakon talauci ne, matasa maza a kauyen suka gamu da babbar matsala wajen yin aure. A watan Nuwamba na shekarar 2013, Xi Jinping ya yi bincike a kauyen Shibadong dake cikin babban dutse. A cikin gidan Shi Qiwen, wanda ya fi fama da talauci, Xi Jinping ya tambayi Shi Qiwen da matarsa game da halin da suke ciki.


Xi Jinping: "ko kuna da isasshiyar shinkafa?"

Shi Qiwen: "e, muna da isasshiyar shinkafa."

Xi Jinping: "ko kuna da guzuri? ko kuna da kudin shiga? Ko kuna samun kiwon aladu ko awaki?"

Shi Qiwen: "muna kiwon aladu biyu."

Bisa ma'aunin fama da talauci na kauyuka da gwamnatin kasar Sin ta kaddamar, ko wane mutum na iya samun kudin shiga RMB 2300 a ko wace shekara, amma a cikin wannan karamin kauye mai al'umma kusan dubu 1, matsakaicin kudin shiga bai kai RMB 1700 ba a shekarar 2013, wato bai kai kashi 1 cikin kashi 5 bisa na manoma a duk fadin kasar a lokacin ba. A kauyen Shibadong, karo na farko ne Xi Jinping ya gabatar da manufar "daukar takamaiman matakai na yaki da talauci", ya kuma jaddada cewa, ya kamata a dauki matakai bisa hakikanan yanayin da ake ciki, tare da ba da jaroganci bisa bambancin halin da ake ciki. Bayan da aka soma gudanar da ayyukan na daukar takamaiman matakai na yaki da talauci, kauyen Shibadong ya tabbatar da raya manyan sana'o'i guda biyar, wato tattalin arziki na kwadago, sana'ar shuke-shuke mai halin musamman, sana'ar kiwon dabbobi mai halin musamman, sana'ar dinkin hannu na kabilar Miao, da kuma sana'ar ba da hidima ta fuskar yawon shakatawa. A shekarar 2017, an tabbatar da kawar da talauci a kauyen nan baki daya, ban da wannan kuma, an samar da wani tsarin daukar takamaiman matakai na yaki da talauci ga sauran yankuna, wanda ake iya koya da kuma yada shi. A yayin da ake kokarin kawar da talauci, kuma matasa maza da yawa ma sun samu mata, kana zaman rayuwar Shi Qiwen da matarsa ma na samun kyautatuwa sosai.


A watan Yuni na shekarar 2017, Xi Jinping ya yi bincike a yankin dake dutsen Lvliang na lardin Shanxi, inda kauyen Zhaojiawa ya kasance kauye mafi fama da talauci a yankin. A gidan mazauna Liu Fuyou a kauyen, Xi Jinping ya zauna a kan gadon katako, ya tambaye shi kan yawan kudin shiga da yake samu a ko wace shekara, da kuma abun da ya fi damun shi. Liu Fuyou ya waiwayi cewa, "Ya zo gida na, kuma ya tambaye ni wasu hakikanan abubuwa, ya tambaye ni, a wane fanni ne kake kashe kudin ka? Na ce, na sayi wasu garin alkama da shinkafa, da kuma mai, gishiri, ruwan magin waken roya da kuma bininga, saura kashi 80 cikin 100 na yi amfani da su kan biyan kudin magani."

Bisa bincike da nazari da aka yi a nan kasar Sin, mutanen da suke fama da talauci da wadanda suke komowa talauci sakamakon kamuwa da cututtuka, sun kai sama da kashi 40 cikin dari. Idan ba a fahimci dalilin haddasa talauci ba, to ba za a iya daukar takamaiman matakai ba don yaki da talauci. Xi Jinping ya gabatar da cewa, matsalolin fama da talauci da sake komowa talauci sakamakon kamuwa da cututtuka su ne muhimmin fanni, wadanda za a mai da hankali a kai wajen kawar da talauci, ya kamata a dauki hakikanan matakai don taimakawa mutane masu fama da talauci, da wadanda sake komowa talauci sakamakon kamuwa da cututtuka, ta hakan za a kara karfin ayyukan kawar da talauci. A shekarar 2017, masu aikin jinya sama da dubu 800, sun yi amfani da watanni biyu don yin bincike kan iyalai masu fama da talauci na kasar baki daya, inda suka tabbatar da cututtuka masu tsanani 45 da suka haddasa talauci. Ta hanyar tallafin kiwon lafiya, da karfafa tsarin ba da tabbaci a fannin aikin jinya da ake gudanarwa a yanzu, da kuma sauran matakai, a shekarar da ta wuce, aka taimakawa mutane kimanin miliyan 5 da dubu 810 daga cikin wadanda ke fama da talauci, ko sake komowa talauci sakamakon kamuwa da cututtuka, wajen kawar da talauci a nan kasar Sin. A cikin jawabinsa na taya murnar sabuwar shekara na bana, Xi Jinping ya yi nuni cewa, "A wannan shekara, an samu labarai masu kyau da dama wajen kawar da talauci. Akwai gundumomi da dama da suke fama da talauci, wadanda yawansu ya kai 125 sun ci nasarar kawar da talauci, kana al'ummar masu fama da talauci miliyan 10 a kauyuka su ma sun cimma irin nasarar. Baya ga haka, an rage farashin magungunan cutar daji iri 17, kuma aka shigar da su cikin jerin magungunan na inshorar jinya, yanzu ana kokarin kara warware matsalar fama da talauci sakamakon kamuwa da cututtuka. Ko da yaushe ina kulawa da mutane masu fama da talauci. A lokacin sabuwar shekarar, ina fatan mazauna kauyuka za su kara samun kyautattuwar zaman rayuwarsu."

Shekarar 2020 na kusantowa, a cikin zuciyar Xi Jinping, kafa zaman al'umma mai matsakaicin karfi, shi ne sanya jama'ar kasar Sin da suka fi fama da talauci su iya yin zaman alheri mai mutunci. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China