in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kalmomin kwantar da zuciya da Shugaba Xi Jinping ya yi wa tsoffi
2019-02-07 16:26:15 cri

A cikin hotuna kalilan kan iyalan Shugaba Xi Jinping da aka bayar, akwai wasu biyu da suka nuna kauna matuka a tsakaninsa da iyayensa. Daya shi ne yadda Xi Jinping yake tura mahaifinsa da ke kan kujerar tura maras lafiya, dayan kuwa shi ne yadda ya rike hannun mahaifiyarsa ya yi yawo tare ita. Ba ma kawai Xi ya kula da gidansa ba, har ma da dukkan gidajen kasar Sin, ba ma kawai yana kaunar iyayensa ba, hatta ma da dukkan tsoffin kasar Sin. A cikin zamanin yau da ake kara samun yawan tsoffi a zamantakewar al'ummar Sin, yadda ko wane tsohon mutum ke iya jin dadin zamansa, wani batu ne da ya jawo hankalin Xi Jinping sosai. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu gabatar muku da labari na uku da ke cikin jerin Labarai kan Yadda shugaba Xi Jinping yake kulawa da zaman rayuwar fararen hula, wato Kalmomin kwantar da zuciya da Shugaba Xi Jinping ya yi wa tsoffi.

Tsoffi: Albarkacin Shugaba! Muna jin dadin zamanmu!

Xi Jinping: Samun lafiyar jiki da tsawon rai burinmu ne na bai daya. Ina fata za ku ji dadin zamanku har abada!

Wannan hira ce a tsakanin Shugaba Xi Jinping da wani tsoho mazauna birnin Shanghai, yayin da Xi ya je ziyara da gaishe shi. Samun karuwar yawan tsoffi, wata babbar matsala ce a gaban kasar Sin a halin yanzu. Bisa hasashen da aka yi, an ce, ya zuwa shekarar 2050, yawan tsoffin kasar Sin zai kai miliyan 487, wanda zai kai kashi 34.9 cikin dari bisa na duk yawan al'ummar kasar.

Tun bayan da Xi Jinping ya kama mukamin babban daraktan kwamitin tsakiya na JKS a shekarar 2012, kullum ya kan je gidajen kulawa da tsoffi don gaishe da tsoffin, da kuma yin nazari kan ci gaban sha'anin kulawa da tsoffi na kasar.

Birnin Shanghai wani babban birni ne da ya fi sauran birane wajen gamuwa da matsalar samun yawan tsoffi a kasar Sin, a ciki yawan tsoffi da shekarunsu suka zarce 60 da haihuwa a yankin Hongkou ya kai kashi 40 cikin dari, bisa na duk yawan al'ummar yankin. A ranar 6 ga watan Nuwamban shekarar 2018, Shugaba Xi Jinping ya ziyarci gidan rainon tsoffi na titin Jiaxing da ke yankin Hongkou, inda ya bayyana kulawarsa ga tsoffi. 

"Matsalar yawan tsoffi tana daya daga cikin matsalolin da suka fi jawo hankalin kwamitin tsakiya na JKS. Yanzu mun riga mun shiga wani zamani na samun karuwar yawan tsoffi, don haka yadda mutane suke jin dadin zamansu yana da alaka da yadda tsoffi suke jin dadin zamansu. Shin ko wane tsohon mutum ya samu kulawa yadda ya kamata? Shin suna da lafiyar jiki? Lallai abun da kuke yi a nan na da babbar ma'ana, na ga suna murna sosai a nan. Ina fata za ku ji dadi a ko wace rana kuma har abada."

Yadda za a aiwatar da manufar kulawa da tsoffi domin kawo musu alheri, wani batu ne da shugaba Xi ya dora muhimmanci a kai a ko da yaushe. Kawo yanzu dai, yankin Hongkou na birnin Shanghai ya riga ya fitar da shirin da zai aiwatar a shekaru uku masu zuwa wajen kyautata aikin ba da hidima ga tsoffi. An kiyasta cewa, ya zuwa karshen shekarar 2021, yawan gidajen rainon tsoffi zai karu zuwa 60, yayin da yawan wajen samar wa tsoffi abinci zai kai 100, kuma yawan masu kulawa da tsoffi kuwa zai kai kimanin 500. Chen Yuebin, shugaban sashen kula da harkokin tsoffi na hukumar kula da harkokin jama'a ta Shanghai ya gaya wa wakilinmu cewa,

"Za mu kokarta wajen ninka kayayyakin ba da hidima ga tsoffi a cikin shekaru uku ko hudu masu zuwa. Nan gaba kuma ba ma kawai za mu mai da hankali kan karuwar yawansu ba ne, har ma za mu kyautata ingancin hidima, ta yadda tsoffi za su kara jin dadin zamansu."

Ban da babban birnin da ke gabashin kasar Sin, wasu birane da lardunan da ke yammacin kasar, na kokarin samar da hidimomi iri daban daban ga tsoffi. A ranar 4 ga watan Fabrairu na shekarar 2013, Shugaba Xi Jinping ya yi rangadin aiki a dakin samar da abinci ga tsoffi da ke unguwar Chengguan ta birnin Lanzhou na lardin Gansu, inda shi kansa ya bai wa tsoffin abinci da zafi-zafinsa. Fu Lianhong, mai dakin cin abincin, wanda yake da bukata ta musamman ya yi waiwaya cewa,

"Ni ne na karshe, yayin da Shugaba Xi ya zo gabana, ya rike hannuna ya ce, kai wani mutum ne da ke da bukata ta musamman, amma kana bayar da gudummawa ga zaman al'ummarmu. JKS da gwamnatin kasar dukkanmu muna maka godiya. Har yanzu na kan tuna da kalaman da ya yi mini. Lamarin da ya kara min kwarin gwiwa sosai wajen ci gaba da gudanar da aikin rainon tsoffi."

A 'yan shekarun nan da suka wuce, Fu Lianhong ya yi kokarin tattara kudi, ya kuma kafa sabuwar cibiyar kulawa da tsoffi rana da dare, da kuma ta rainon tsoffi, yayin da yake habaka dakin samar wa tsoffi abinci.

Masu sauraro, abin da kuke saurara yanzu, wata hira ce a tsakanin Shugaba Xi Jinping da Shi Pazhuan, wata tsohuwa mai fama da fatara da ke zaune a yankin Xiangxi na lardin Hunan. Da ta ga Shugaba Xi da ya je gidanta don ziyara, ta yi matukar farin ciki, ta yaba wa Shugaba Xi a matsayin babban jami'in da ke kulawa da jama'a sosai, kamar yadda iyaye suke kulawa da yaransu. Da jin hakan, Shugaba Xi ya amsa cewa, "Ni mai bautawa jama'a ne kawai".(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China