in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burin kasar Sin a kauyen Liangjiahe
2019-02-05 16:18:57 cri

Liangjiahe, wani karamin kauye ne dake kan tudu a arewa maso yammacin kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zauna a wurin daga lokacin da yake da shekaru 15 zuwa 22, wanda ya sa ya kara fahimtar ainihin zaman rayuwar mazauna yankunan karkarar kasar. Haka kuma ra'ayoyin mazauna yankunan karkarar kasar Sin sun karfafa gwiwar Xi Jinping wajen cimma burinsa na bautawa al'ummar kasar. Tun daga yau za mu fara gabatar muku da wasu jerin rahotanni guda bakwai game da yadda shugaba Xi Jinping yake kulawa da zaman rayuwar fararen hula, inda a yau za mu gabatar muku da rahoto na farko mai suna burin kasar Sin a kauyen Liangjiahe.

A ranar 22 ga watan Satumbar shekarar 2015, a wajen liyafar maraba da zuwan shugaban kasar Sin Xi Jinping jihar Washington dake kasar Amurka da gwamnati gami da kungiyoyin sada zumunta na kasar suka shirya tare, Xi ya gabatar da wani labari ga mahalarta liyafar, inda ya bayyana cewa:

"A karshen shekarun 1960, shekaruna goma ne da 'yan kai. Na tashi daga birnin Beijing zuwa wani karamin kauye mai suna Liangjiahe dake birnin Yan'an na lardin Shaanxi, inda na yi shekaru bakwai ina aikin gona a wajen. Kafin daga bisani kuma na zama darektan reshen jam'iyyar kwaminis dake kauyen, inda na jagoranci manoman wurin raya ayyukan gona. Abun da nake fata a wancan lokaci shi ne, kowa ya iya cin nama har ya koshi, haka kuma za su iya samun nama su ci a kullum."

Sa'annan a shekara ta 1969, Xi Jinping, mai shekaru 15 da haihuwa a wancan lokaci, tare da sauran wasu matasa dalibai miliyan 17 suka amsa kiran da gwamnatin kasar Sin ta yi musu, inda suka bar birane da garuruwansu suka shiga yankunan karkara don aiki tare da zama. Xi Jinping ya yi shekaru bakwai yana aiki tukuru a kauyen Liangjiahe, inda ya sauya daga dan babban birni zuwa matashin dake iya aikin komai a kauyen. Shi Chunyang, mai shekaru 63 a duniya, wanda ke zaune kauyen Liangjiahe ya yi waiwaye adon tafiya yana mai cewa:

"Yayin da muke gina madatsar ruwa, Xi Jinping bai yi wata-wata ba ya nade kafar wandonsa ya cire takalmi ya shiga cikin kogi don kwashe kankara. Bai damu da cutar da za ta iya kama shi ba."

Daga baya kuma, Xi Jinping ya karanta wani labarin dake cewa, ana kokarin samo iskar gas daga najasa a yankunan karkarar lardin Sichuan. Sai ya je birnin Mianyang na lardin Sichuan don karatun wannan fasaha, kafin daga bisani kuma ya hako ramin samo iskar gas daga najasa na farko a lardin Shaanxi. Xi Jinping ya bayyana cewa:

"Mun sha walaha sosai wajen hako rami na farko. Mun ga ruwa na kara yin sama a cikin ramin, amma babu iskar gas, da na kara hakowa, sai kashi ya watsu a fuskata, amma sai muka ga iskar na fitowa. Ba tare da bata lokaci ba muka hada bututu, inda wuta ke fitowa daga na'urar dafa abinci."

A cikin shekaru bakwai da ya yi a kauyen Liangjiahe, Xi Jinping ya yi aiki tare da zama da manoman wurin, inda ya yi aikin shimfida titi, da hako ramin samo iskar gas daga najasa, da shiga cikin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, har ya kai ga zama darektan reshen jam'iyyar a wajen. Haka kuma zama da aiki a kauyen Liangjiahe ya karfafa imanin da Xi yake da shi, inda ya bayyana cewa, a matsayinsa na mai bautawa al'ummar kasar, tudun dake arewacin lardin Shaanxi ya kasance tamkar saiwarsa, saboda a can ne aka karfafa masa imanin cewa, ya kamata a yi iyakacin kokari don bautawa jama'a!

Xi Jinping ya ce:

"Na ga karfin jama'a, na ga tushen zaman rayuwarsu, har na fahimce su, da kara sanin zamantakewar al'umma, wannan yana da muhimmanci matuka. Ra'ayoyi da dama da nake da su, sun samo asali ne a wancan lokaci, wadanda har yanzu suke yi min tasiri."

Shugaba Xi ya san muhallin kauyen Liangjiahe, har ma ya san kowane iyali a wajen. A gabannin bikin bazara na shekara ta 2015, Xi ya koma wannan kauye, inda ya hadu da abokansa mazauna kauyen, har ma ya kira su da lakabinsu:

"Zhang'er, Ying'er, Yingchun, ina iyayenku?"

Game da ziyararsa kauyen Liangjiahe a shekara ta 2015, Xi ya bayyana manyan sauye-sauyen da aka samu a wajen yayin da ya ziyarci Amurka, inda ya ce:

"Kauyen Liangjiahe ya sha bamban da na lokacin da, inda aka shimfida hanyoyin mota, jama'a ma sun shiga cikin dakuna masu inganci, da fara amfani da yanar gizo ta Intanet. Tsoffi na jin dadin zaman rayuwarsu, mutane kuma suna da inshorar kiwon lafiya, har ma yara suna iya karo ilimi a makaranta ba tare da matsala ba, balle ma batun cin nama. Duk wadannan sauye-sauyen sun kara fadakar da ni cewa, burin kasar Sin buri ne na jama'a, kuma ya zama dole a hada shi da irin kyakkyawan fatan da jama'ar kasar suke da shi, na neman jin dadin zaman rayuwa, domin cimma babbar nasara."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China