in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kaddamar da shirin tiso-keyar masu cin hanci da rashawa na shekarar 2019
2019-01-30 17:09:54 cri

Kasar Sin ta kaddamar da shirin tiso-keyar masu cin hanci da rashawa daga kasashen da suke samun mafaka na shekarar 2019 a kwanan baya, bisa umurnin da ofishin kula da aikin farautar masu aikata cin hanci wadanda ke tserewa kasashen waje da kwato kudaden da suka sata na cibiyar dake yaki da cin hanci na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar ya bayar, da nufin maida hankali kan wasu muhimman kasashe da mutane domin rage yawan wadanda ake tserewa dasu zuwa ketare da kuma hana wandanda ke da shirin gudu zuwa waje. Li Shulei, matamakin daraktan kwamitin lura da ladabtarwa na jam'iyyar kuma mataimakin shugaban kwamitin sanya ido kan harkokin kasar ya bayyana cewa, za a kokarta wajen aiwatar da shirin tiso-keyar masu cin hanci da hana tserewa zuwa waje da ma kwato dukiyoyin da aka sata aka gudu dasu, domin dakile hanyar tserewa da ma bata ransu kwata kwata.

Shirin tiso-keyar masu cin hanci da rashawa daga kasashen da suke samun mafaka wani muhimmin aiki ne da kasar Sin ta fara gudanarwa a shekarar 2015 bisa umurnin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kwamitin tsakiya na JKS, wanda keda aniyar farautar masu aikata cin hanci dake tserewa kasashen waje da kwato kudaden da suka sata ta hanyoyin diplomasiyya da doka da shari'a da sha'anin kudi. Bisa labarin da aka samu, an ce, a cikin shirin nan na shekarar bara, an maido da masu tserewa zuwa ketare kimanin 1335, yayin da yawan kudaden da aka kwato daga wajensu ya zarce Yuan biliyan 3.5.

Mataimakin shugaban sashen kula da dokoki na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Sun Xiaofei ya fayyace cewa, a matsayinta na hukumar bada taimako wajen tuntubar kasashen waje don maido da masu aikata laifuka, ma'aikatar harkokin wajen ta sa hannu cikin aikin maido da wasu. Ya kara da cewa,

"A bara, mun gabatar da roko 30 ga ketare don neman maido da masu aikata laifi, lamarin da yasa muka maido da masu aikata laifi 20 cikin nasara, lallai muna samun ci gaba sosai a wannan fanni. Alal misali, mun taimaka wajen maido da Yao Jinqi daga kasar Bulgaria, wanda aka kwashe kwanaki 44 daga lokacin da bangaren Bulgaria ya kamashi har zuwa maido dashi kasar Sin, kana ya zama mutum farko da kasar Sin ta maido dashi daga kasa mambar kungiyar EU."

Banda wannan kuma a cikin wadanda aka maido dasu kasar Sin cikin shirin tiso-keyar masu cin hanci da rashawa na bara, an kamo masu aikata manyan laifuka 5 wadanda ake nemansu ruwa a jallo, ciki har da Jiang Lei, tsohon zaunannen mataimakin shugaban kungiyar kula da ayyukan kera motoci ta kasar Sin wanda ya tsere zuwa kasar waje har na tsawon shekaru 11.

Yayin da ake kokarin farautar masu aikata cin hanci dake tserewa kasashen waje da kwato kudaden da suka sata, kwamitocin masu sanya ido kan harkokin kasa na wurare daban daban sun dukufa wajen aikin hana tserewa zuwa ketare. Yueling, wani jami'i na kwamitin sanya ido kan harkokin jihar Jiangsu ya yi bayanin cewa, jihar ta fitar da wasu fayiloli don kyautata ayyukan wasu hukumomin tuntubar waje. Ya kara da cewa,

"Yayin da muke kokarin maido da masu aikata laifi, muna daukar matakai don hana sabbi su gudu zuwa ketare. A bara, mun tattauna da manyan kamfanonin gwamnatin jiharmu musamman ma wadanda keda ayyuka a ketare, baya ga fitar da wasu ka'idoji don rigakafin tserewar ma'aikatan kamfanonin da hukumomin kudi da jami'o'i, da ma satar kudaden da aka yi. Lallai aikin nada muhimmiyar rawa wajen hana tserewa zuwa ketare cikin dogon lokaci."

Haka zakila Furofesa Huang Feng na jami'ar horar da malamai ta Beijing, wanda shima shugaban cibiyar nazarin aikin farautar masu aikata cin hanci dake tserewa kasashen waje da kwato kudaden da suka sata na G 20 ne, yana ganin cewa, shirin tiso-keyar masu cin hanci da rashawa zai bada taimako wajen kafa tsarin hadin kan kasa da kasa wajen yaki da cin hanci da rashawa. Ya ce,

"bayan da aka gudanar da shirin cikin shekaru da dama, an kafa wani tsarin farautar masu aikata cin hanci dake tserewa kasashen waje da kwato kudaden da suka sata sannu a hankali. Alal misali, an daidaita wannan batun cikin babin hadin kan kasashen waje na dokar sanya ido, kana an tanadi jerin ka'idoji da matakai wajen maido da masu cin hanci da kwato kudaden da suka sata cikin dokar bada taimako ga aikin hukunta manyan laiffuffuka ta kasa da kasa. Duk wadannan sun taimaka wajen gudanar da aikin farautar masu aikata cin hanci dake tserewa kasashen waje da kwato kudaden da suka sata bisa doka."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China