in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin Bazara na nuna kyakkyawan al'adun Sinawa
2019-01-31 08:23:54 cri

Bikin bazara wato Spring Festival a Turance, bikin gargajiya ne mafi kasaita ga Sinawa, da ke alamanta shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar. Bikin bazara na kasar Sin yana da tsawon tarihin da ya kai kimanin shekaru 4000, kuma ya yi daidai da muhimmancin bikin kirsimeti ga Turawa, shi ne kuma biki mafi muhimmanci ga Sinawa. Bikin a wannan shekara ya fado a kwanakin makon farko na watan Fabarairun 2019.

Bikin Bazara na zuwa lokacin da Sinawa ke ban kwana da tsohuwar shekara, tare kuma da shiga cikin sabuwar shekara bisa kalandar Kasar.

Sin kasa ce da ke mai da hankali kan aikin gona, a shekaru aru aru da suka gabata, ana amfani da taurari domin kokarin gudanar da harkokin aikin gona kamar yadda ake fata. Sakamakon haka, aka kirkiro kalandar wata a nan kasar Sin bisa tsarin tafiye-tafiyen taurari. Bisa wannan kalandar ce, ake fara shiga sabuwar shekara a lokacin sanyi, wato a yayin da ake hutu bayan kammala girbin amfanin gona.

Bisa al'adar galibin sassan kasar Sin, ana fara shagulgulan bikin bazara ne a ran 23 ko 24 ga watan sha biyu bisa kalandar wata. Galibin iyalin Sinawa su kan fara tsaftace dakunansu, wato kawar da dukkan tsoffin abubuwa marasa kyau daga gida, sannan a yi bikin girmama manzon dafa abinci.

Bugu da kari, a daren ranar 30 ga watan sha biyu, bayan an ci abinci masu dadi da dare, kusan dukkan iyali su kan yi hira suna jiran gari ya waye domin murnar isowar sabuwar shekara, wato ranar 1 ga watan farko na sabuwar shekara. Bayan gari ya waye a safiyar ranar 1 ga watan farko, matasa su kan tafi gidajen tsoffi domin nuna musu girmamawa. Wato tun daga ran 23 ga watan sha biyu zuwa ranar 15 ga farkon watan sabuwar shekara, kusan kowace rana, ana da shagulgulan murnar bikin bazara.

A baya a kan shafe kusan kwanaki 20 ana murnar wannan biki musamman a yankunan karkara. Amma ga wadanda suke aiki a kamfanoni da hukumomin gwamnati, ba su da dogon lokacin hutu, a da su kan huta na kwanaki 3 kacal, amma yanzu su kan huta na kwanaki 7.

Saboda ci gaban zamani, yanzu karin Sinawa na amfani da lokutan hutun bikin bazara domin zuwa yawon shakatawa wasu sassa na duniya. Duk da hakan babbar manufar wannan biki mai muhimmanci ga Sinawa, ba ta sauya ba a tsawon shekaru masu yawa, wato haduwa da iyalai bayan tsawon shekara, don murnar shigowar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin.

A ko wace shekara Sinawa na amfani da dabbobi 12 domin wakilcin watannin shekara, a bana sabuwar shekarar gargajiya ta Sin shekara ce ta Alade. Sauran dabbobin da ke alamta watannin sun hada da Biri, da Rago da Doki, da Maciji, da Bera da dai sauran su.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China