190205-Likitocin-kasar-Sin-dake-aiki-a-kasashen-Afirka-na-kokarin-inganta-lafiyar-alummar-wurin.m4a
|
Deng Jianhua shi ne daya daga cikin tawagar likitocin kasar Sin da gwamnatin kasar ta tura zuwa kasar Equatorial Guinea kashi na 29. Yayin da wakilinmu ke shiga cikin dakin ganin likita, likita Deng yana kokarin duba wani maras lafiya da yaren Spaniyanci. Deng ya fara aiki a Equatorial Guinea a watan Janairun bara wato 2018, yanzu shekara daya cif ke nan .
Equatorial Guinea kasa ce dake tsakiya maso yammacin nahiyar Afirka, wadda ke kusa da tekun Atlantika. Fadin kasar ya kai murabba'in kilomita dubu 28, kuma kashi 80 bisa dari na yankin kasar gandun daji ne. Tun bayan da aka hako albarkatun man fetur a kasar, Equatorial Guinea ta samu babban ci gaba har ma ta zama daya daga cikin kasashen duniya wadanda tattalin arzikinsu ke bunkasa cikin saurin matuka. Amma wasu cututtuka masu yaduwa, ciki har da malariya da kanjamau suna ta kashe mutane masu tarin yawa a wannan kasa. Tun daga shekara ta 1971 ya zuwa yanzu, sau 29 gwamnatin kasar Sin tana tura kungiyoyin likitocinta zuwa kasar Equatorial Guinea don bada taimako ga harkokin kiwon lafiyar kasar.
Tawaga ta 29 ta likitocin kasar Sin da gwamnatin kasar ta tura zuwa Equatorial Guinea ta zo daga birnin Zhuhai na lardin Guangdong, wadda ke kunshe da likitoci 27, wadanda suka shafi sassan zuciya da jijiyoyi da tausa da kayan ciki da bangaren haihuwa da mata da yara da ido da kashi da sauransu. Suna aiki ne a wasu sassa uku dake Equatorial Guinea, ciki har da fadar shugaban kasa, da birnin Malabo da kuma yankin Bata.
Equatorial Guinea na fama da matsalar ingantattun kayan kiwon lafiya da likitoci za su yi amfani da su a asibiti, al'amarin da ya baiwa likitocin kasar Sin mamaki. Shugaban kungiyar likitocin kasar Sin reshen birnin Malabo, likita Xu Jiwen wanda ya yi shekaru sama da 30 yana aikin yin allura ga wadanda za'a yiwa tiyata, ya bayyana cewa, Equatorial Guinea na fama da karancin magunguna da na'urorin jinya, matsalar da ta jawo tsaiko ga ingantuwar lafiyar jama'ar kasar.
Bayan da ya yi shekara daya yana aikin jinya a Equatorial Guinea, likita Xu ya ce ya gamu da marasa lafiya da dama da suka je neman taimako wajen likitocin kasar Sin, amma abun da ya fi burge shi, ita ce tiyatar da likitocin kasar Sin suka yi a idon wani yaro dan kasar mai shekaru 8 da haihuwa.
Babban likitan da ya yiwa idon yaron tiyatar, Mista Deng Jianhua ya bayyana cewa, yaron da gilashi ya raunata idonsa na dama, na fuskantar hadari sosai, inda ya ce:
"Idan muka yi masa tiyatar a ido, za mu fuskanci babban hadari. Saboda idan mun yi tiyatar, akwai yiwuwar idonsa na dama ba zai warke ba, kuma watakila mu cire shi, in ba mu yi aiki mai kyau ba, domin zai shafi idonsa na hagu, wato ke nan wannan yaro mai shekaru 8 zai makance baki daya, kuma wannan na iya zama wata babbar masifa a gare shi. Amma bayan da muka yi tattauna wa mai zurfi, mun yanke shawarar yi masa tiyata."
A karshe, sakamakon kokarin da likitocin kasar Sin suka yi, sun yi nasarar yiwa wannan yaron tiyata, yaron ya samu waraka sosai daga matsalar idon.
Irin himma da kwazon da likitocin kasar Sin suka nuna wajen inganta lafiyar mazauna wurin, shi ma ya burge takwarorinsu na kasar Equatorial Guinea. Likita Celestino Edjang Nguema wanda ke aiki a sashin ido na babban asibitin Malabo ya ce:
"Likitocin kasar Sin suna da kwarewa sosai wajen yiwa marasa lafiya magani da tiyata, wadanda suka kawo mana sabbin fasahohin da ba mu da su a kasarmu. Gaskiya sun taimaka sosai wajen inganta harkokin kiwon lafiya na kasarmu."
Wata matsala ta daban da kasar Equatorial Guinea ke fuskanta ita ce, adadin yawan mace-macen mata masu juna biyu ko matan da suka haihu da kuma jariran da za a haifa a nan gaba. Wakilin gidan rediyon kasar Sin ya kuma ziyarci sashin kula da jarirai na babban asibitin Malabo, inda likita Kuang Wenying ta bayyana cewa:
"A kowace rana muna duba jarirai a nan, idan jariri ba shi da matsala, za mu sallame shi zuwa gida."
Madam Francisca wadda ba ta dade da haihuwa ba ta gayawa wakilinmu cewa, tana son likitocin kasar Sin sosai:
"Likitocin kasar Sin na da kirki kwarai. Suna maida hankali sosai da sosai ba mu kulawa, har ma da 'ya'yanmu."
Malam Bahaushe kan ce, rigakafi ya fi magani. Wannan shi ma yana faruwa a yayin da likitocin kasar Sin ke gudanar da ayyukansu a kasar Equatorial Guinea. Wato ba kawai suna yiwa marasa lafiya jinya da ba su magani ba, har ma suna kokarin koyarwa likitoci gami da nas-nas na wurin ilimi da fasahohin aikin jinya. Likita Shi Shaoquan wanda ke aiki a sashin kula da mata na kungiyar likitocin kasar Sin reshen yankin Bata ya bayyana cewa:
"Mun taho da wata na'urar nuna majigi daga kasar Sin, kuma za mu koya musu fasahohin kula da mata masu juna biyu da matan da suka haihu. Haka kuma akwai littattafai da hotunan bidiyo da suka shafi kiwon lafiya na kasar Sin da muka samo daga Intanet, wadanda daga baya mun rarraba wa ungozomai, don su kara fahimtar fasahohin kasar Sin a wannan fanni."
A halin yanzu kasar Sin ta tura likitocinta zuwa kasashe 71 dake sassan duniya. A Equatorial Guinea, kungiyar likitocin kasar Sin tana kuma daukar babban nauyin kulawa da lafiyar shugaban kasa, wanda ba kasafai a kan gan shi a wasu kasashe ba.
Shugabar rukunin kula da lafiyar shugaban kasar Equatorial Guinea na kungiyar likitocin kasar Sin, Madam Jin Lizi ta bayyana cewa:
"Gaskiya muna farin ciki sosai da yadda shugaban kasar Equatorial Guinea yake son aikin jinya da kulawar da muka ba shi. Wannan ya shaida irin zumuncin dake tsakanin Sin da Equatorial Guinea."
Domin kara fadada samar da tallafin jinya da magani a Equatorial Guinea, kungiyar likitocin kasar Sin sun kuma shiga cikin yankunan karkarar kasar don samar da agajin jinya ga mazauna wuraren. A shekara ta 2018, likitocin kasar Sin sun yi wa marasa lafiya 62 tiyatar yanar ido a duk fadin kasar.
To, a daidai wannan lokacin da al'ummar Sinawa ke murnar shiga sabuwar shekara tare da iyalansu a gida, likitocin kasar Sin dake Equatorial Guinea ba su samu zarafin dawowa gida ba, duk da haka sun bayyana fatan alherinsu a sabuwar shekara. Shugaban tawagar likitocin kasar Sin karo na 29 da gwamnatin kasar ta tura zuwa kasar Equatorial Guinea, Mista Chen Lei ya ce:
"Za mu kara cin abinci mai dadi, tare da takwarorinmu a asibitin wurin. Muna fatan kowa da kowa zai samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, wannan shi ne abun da ya fi muhimmanci a gare mu."
Baya ga Equatorial Guinea, a kasar Burkina Faso dake yammacin Afirka kuma, akwai likitocin kasar Sin dake bayar da tallafin jinya da magani a wurin.
A ranar 7 ga watan Yulin shekarar da ta gabata, kungiyar likitocin da gwamnatin kasar Sin ta tura ta isa Ouagadougou, fadar mulkin kasar Burkina Faso. Shugaban kungiyar Mista Wang Yong ya bayyana cewa:
"Ita wannan kungiyar likitocin, kungiya ce da hukumar birnin Beijing ta tura, wadda ke kunshe da likitoci guda goma. A halin yanzu muna tafiyar da ayyukanmu yadda ya kamata a nan Burkina Faso. Na farko, mun tabbatar da wasu ka'idojin aikin jinya tare da bangaren Burkina Faso. Na biyu, mun ba su kyautar wasu kayan jinya kirar kasar Sin kuma mun yi amfani da su wajen yiwa marasa lafiya tiyata. Na uku shi ne, mun shiga cikin sassa daban-daban na kasar Burkina Faso, don yiwa marasa lafiya tiyatar da ta shafi ido, ta yadda za su rika gani kamar kowa."
A ranar 22 ga watan Disambar shekara ta 2018, wasu kwararru likitocin ido guda goma daga birnin Wenzhou na kasar Sin sun isa Ougadougou, inda suka fara yiwa mutanen wurin tiyatar yanar ido kyauta. Ya zuwa ranar 5 ga watan Janairun shekarar da muke ciki, sun yiwa mutane 146 tiyata a asibitin Tengandogo dake Burkina Faso.
A nasa bangaren, jakadan kasar Sin dake kasar Burkina Faso, Li Jian ya bayyana cewa, tiyatar yanar ido da likitocin kasar Sin suka gudanar, wani abun misali ne na hadin-gwiwar dake tsakanin Sin da Burkina Faso ta bangaren kiwon lafiya. Jakada Li ya ce:
"Tun bayan da Sin da Burkina Faso suka farfado da huldar diflomasiyya a tsakaninsu, ya zuwa yanzu, hadin-gwiwa da mu'amalar da ake yi tsakaninsu na bunkasa cikin sauri, musamman bangaren kiwon lafiya. Tiyatar yanar ido da likitocin kasar Sin suka yi, ba kawai yana kawo moriya ga jama'ar Burkina Faso ba, har ma zai taimaka sosai wajen inganta ayyukan kiwon lafiya na kasar."
Shugaban asibitin Tengandogo, Alexandre Sanfo, ya godewa likitocin kasar Sin saboda aiki tukuru da suka yi, gami da tallafin kayan jinya da suka bayar. Alexandre Sanfo ya ce:
"Kwararru likitocin ido daga birnin Wenzhou na kasar Sin sun bayar da babban taimako da gudummawa ga asibitinmu, sun kuma nuna mana fasahohin jinya na zamani tare da ba mu tallafin kayan jinya. Har wa yau, likitocin kasar Sin suna kokarin koyar da takwarorinsu dake asibitinmu, yadda asibitinmu zai bunkasa cikin sauri. Duk wadannan abubuwa sun shaida irin dankon zumunci dake tsakanin Sin da Burkina Faso."