in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata kasashen duniya su yi kokarin neman bunkasuwa tare domin moriyar al'ummomin duniya
2019-01-25 11:22:28 cri

A ran 23 ga wata, bisa gayyatar da aka yi masa, mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan ya halarci taron tattaunawar tattalin arzikin kasa da kasa na Davos na shekarar 2019, ya kuma gabatar da jawabi, inda ya bayyana cewa, dole ne a rika furta magungunan da suka dace da matsalolin da ake fuskanta a lokacin da ake kokarin bunkasa tattalin arzikin duniya bai daya, sannan dole ne a kara neman ci gaba domin daidaita matsalar rashin samun ci gaba cikin daidaito. Game da jawabinsa, wasu masana sun nuna cewa, matsalar rashin neman ci gaba cikin daidaito tana addabar fadin duniya, al'ummomin kasa da kasa za su iya cin gajiya ce kadai, idan aka kara sanya ido kan yadda za a kara bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya.

A cikin jawabinsa, Mr. Wang Qishan, mataimakin shugaban kasar Sin ya nuna cewa, dole ne a kara neman ci gaba domin daidaita matsalar rashin samun ci gaba cikin daidaito. Za a samu hanyoyin raba moriya mafi kyau ne a lokacin da ake neman karin ci gaba, ba za a iya dakatar da neman ci gaba ba domin yin cacar baki kan hanyoyin raba moriya. Nuna rashin damuwa kan matsaloli da wasu mutane ke fuskanta ma ba zai daidaita matsalar ba. Game da kalaman nasa, Mr. Wang Jun, masanin farko kan harkokin tattalin arziki a bankin Zhongyuan na kasar Sin yana ganin cewa, matsalar rashin neman ci gaba cikin daidaito, matsala ce dake fuskantar fadin duniya, ya kamata kasashen duniya su kara sanya ido kan yadda za a kara bunkasa tattalin arzikin duk duniya domin kawar da matsalar gaba daya.

"Yanzu, ba ma kawai matsalar rashin samun ci gaba cikin daidaito ta kasance a tsakanin yankuna masu arziki da yankuna marasa arziki ba, tana kuma kasancewa a tsakanin yankuna masu arziki, da yankuna marasa arziki. Shugabannin kasar Sin sun gabatar da ra'ayoyinsu, wato kara neman ci gaba domin warware wannan matsala. Za a iya raba moriya ta hanyar samun karin ci gaba, bai kamata a sa ido kan yadda za a raba sakamakon da ake da shi a yanzu kawai ba."

A cikin jawabinsa, Mr. Wang Qishan ya bayyana cewa, kasar Sin ta kuduri anniyar tafiyar da harkokinta da kanta kamar yadda ya kamata domin tinkarar matsalar. Yanzu, kasar Sin ta shiga sabon zamanin dake da halin musamman na gurguzu. Tana kuma fuskantar matsalar rashin neman ci gaba cikin daidaito. Sannan matsala mafi tsanani dake kasancewa a nan kasar Sin ita ce, kasar Sin ba ta samun ci gaba cikin daidaito kamar yadda ya kamata, sakamakon haka, ba ta iya biyan sabbin bukatun al'ummomin kasar. Kasar Sin ta tsaya kan matsayinta na zurfafa yin gyare-gyare, ta kuma kawar da wasu matsaloli masu matukar tsanani.

Mr. Zhao Jinping, wani masani kan harkokin tattalin arziki na kasar Sin yana ganin cewa, kasar Sin tana gyara tsarin tattalin arzikinta bisa bukatun da ake da su a kasuwa domin kokarin kawar da matsalar rashin samun ci gaba cikin daidaito, tana kuma tsayawa kan matsayinta na daidaita matsalolin da take fuskanta da kanta domin kokarin bayar da gudummawarta ga ci gaban duniya baki daya.

"Ingiza gyara tsarin tattalin arzikin kasar Sin bisa bukatun da ake da su a kasuwa, babbar manufa ce da kasar Sin take bi, sannan a kullum mu kan jaddada cewa, dole ne a samu sabon karfin neman ci gaba bisa gyare-gyaren da muke yi. Muna kokarin kyautata yanayin kasuwa domin sa kaimi kan masana'antu su nemi ci gaba. Sannan kasar Sin na kokarin bullo da kyakkyawan muhalli da yanayi ga masana'antu ko kamfanoni kan yadda za su kirkiro sabbin fasahohin zamani bisa bukatun da ake da su a kasuwa. Bugu da kari, kasar Sin na kokarin kare 'yancin mallakar fasaha domin ba da tabbaci ga kokarin kirkiro sabbin fasahohin zamani."

Babban jigon wannan taro shi ne "an shiga juyin-juya halin raya masana'antu karo na hudu a lokacin da ake bunkasa tattalin arzikin duk duniya baki daya". A cikin jawabinsa, Mr. Wang Qishan ya kuma nuna cewa, sabbin fasahohin zamani ba wata dama ce kawai ba, hadari ne da kalubale. Dole ne a kare babbar ka'idar tabbatar da tsaron bil Adama a lokacin da ake tsara ka'idoji da ma'aunan yin amfani da sabbin fasahohin zamani, amma a waje daya, dole ne a kara sa kaimi ga ayyukan nazarin kimiyya da fasaha, yada da kuma yin amfani da sabbin fasahohin zamani. Sannan dole ne a kula da kuma daidaita moriya daban daban tsakanin kasashe masu arziki da marasa arziki. Game da batun, Mr. Wang Jun, masanin farko kan harkokin tattalin arziki a bankin Zhongyuan na kasar Sin yana ganin cewa, tabbas dukkan al'ummomin kasa da kasa za su ci gajiyar sabbin ilmin kimiyya da fasahohin zamani. Sabo da haka, ya kamata a tsaya kan matsayin bude kofa da kuma hakuri da juna a lokacin da ake kafa sabbin ka'idoji da ma'aunan da abin ya shafa.

"A hakika dai, juyin juya halin fasaha ya taka muhimmiyar rawa sosai ga ci gaban bil Adama da tattalin arziki da kuma zamantakewar al'umma. A lokacin da muke fuskantar sabon juyin juya halin masana'antu da fasahohin zamani, dukkan kasashen duniya na yin la'akari kan yadda za mu iya dacewa da sabbin fasahohin zamani, da yadda za su taka karin rawa. Muna tsammanin cewa, bayan bullar sabbin fasahohin zamani, ya kamata kowa zai iya cin gajiyarsu. A ganina, abin da ya fi muhimmanci shi ne ya kamata a kafa wani tsarin tantance ka'idojin yadawa da kuma yin amfani da su." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China