in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mabudi ne dake taimakawa wajen fahimtar kasar Sin
2019-01-24 19:09:50 cri
A yayin da kasar Sin ke mu'amala da kasa da kasa, wata babbar matsala da ta fuskanta ita ce, kasashen waje ba su fahimce ta sosai ba, har ma su kan bayyana ra'ayoyi marasa kyau a kan ta. A nasu bangaren, kasashen waje, musamman ma kasashen yamma suna mamaki sosai kan ci gaban kasar Sin, manufar ta da sauransu, amma ba su fahimce ta sosai ba. Game da haka, mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan, wanda yanzu haka ke halartar taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya da ke gudana a Davos, ya gabatar da cewa, tarihi, al'adu da falsafa sun kasance mabudi na kara fahimtar kasar Sin.

Wato, za a kara fahimtar kasar Sin ta fannonin tarihi, al'adu da kuma falsafa, ciki har da manyan nasarorin da Sin ta samu, wadanda ke sanya kasashen duniya mamaki kwarai, da ma harkokinta na cikin gida da na waje.

Marigayi Deng Xiaoping ya taba bayyana cewa, ci gaba shi ne kome. Haka kuma ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, ci gaba shi ne babban jigo na zaman rayuwar bil'adama, kana shi ne ginshikin warware dukkan matsalolin kasar Sin. Sin ta jaddada cewa, ya kamata a raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma, kana ta tsara wasu manufofin da suka shafi tattalin arziki da zaman rayuwar al'umma, al'amarin da ya taimaka ga sauye-sauye da kuma bunkasuwar kasar Sin. A shekara ta 1978, yawan GDP na kasar Sin ya yi kasa da dala triliyan 0.15, amma adadin ya kai kimanin dala triliyan 13.6 a bara.

Akwai dalilai da dama wadanda suka jawo manyan sauye-sauyen da suka faru a kasar Sin, amma, manufar gwamnatin kasar Sin ta tafiyar da harkokin mulki, wato ba da muhimman ga batun jama'arta, ta taka muhimmiyar rawa.

Wannan shi ma dalilin da ya sa gwamntin kasar Sin ke dora muhimmanci a kan aikin saukaka fatara, matakin da ya sa har ta kai ga cimma nasarar fid da al'ummar Sinawa kusan miliyan 800 daga kangin talauci. Wani rahoton binciken da kamfanin Edelman mai kula da huldar jama'a na kasar Amurka ya fitar ya nuna cewa, yadda al'ummar Sinawa ke amincewa da gwamnati ya kai kaso 86%, wanda har ya kai na farko a duniya, lamarin da ya shaida gaskiyar ra'ayin da cewa, "Sai al'umma ta zauna lafiya ake samun kwanciyar kasa."

A yayin da kasar Sin ke hulda da kasashen duniya, ta kuma gabatar da sabon salon manufar raya hulda da cimma muradu tare da martaba ka'idoji, kuma hulda mai sabon salo na da ma'anar hadin gwiwar cimma nasara tare, wanda take ba da shawarar yin hadin gwiwa da juna a maimakon nuna kiyayya ga juna, kuma a cimma nasara tare a maimakon nasarar wani shi daya kawai.

Ra'ayi na hadin gwiwa da kokarin amfanawa juna wani bangare ne na al'adun gargajiyar al'ummar Sinawa, kana gwamnatin kasar Sin ta karfafa wannan ra'ayin yayin da take gudanar da ayyukan hulda da kasashen waje. A duk lokacin da mutum ya samu damar karanta wasu daga cikin tsoffin littattafan kasar Sin, zai fahimce cewa, akwai tsarin nan na "taimakawa wasu kafin samun moriyar kai", da na " kar a damu da wani kawai" a cikinsu. Wadannan ra'ayoyi sun sha bamban da ra'ayin siyasa na yammacin duniya, wanda ya fi mai da hankali kan takara da juna.

A fannin hulda da kasa da kasa kuwa, kasashen yammacin duniya suna da manufar "babu zumunci na har abada, sai kuma ribar da za a samu". Amma kasar Sin ta gabatar da ra'ayin lura da adalci, wanda ya sha bamban da na kasashen yamma, inda aka fi mai da hankali kan samun daidaito tsakanin adalci da moriya, gami da kokarin dora adalci a kan moriya idan akwai bukatar haka. Kimanin shekaru 2300 da suka wuce, Mencius, wani shehun malami na kasar Sin, ya taba bayyana ra'ayi mai kama da hakan, inda ya ce, "Ina son rayuwa, kuma ina son adalci. Idan har zan samu daya daga cikinsu, to, zan yi watsi da rai, kuma na zabi adalci."

Wasu na ganin cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar ta kalubalanci tsarin kasa da kasa da yammacin kasashen suke jagoranta. Wannan ba daidai ba ne. An gabatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya" ce bisa al'adun gargajiyar kasar Sin. Wani fitaccen dan siyasa a zamanin da, mai suna Mencius ya taba bayyana cewa, "Ya kamata mu taimakawa al'ummomin kasa da kasa, inda muka cimma nasara". Shi ya sa, a halin yanzu, kasar Sin ta yi kira ga kasa da kasa da su yi hadin gwiwa domin cimma moriyar juna, lamarin da ya dace da al'adun kasar Sin.

A yayin da duniya ke kokarin dunkulewa waje guda, talauci na kokarin zama babban abokin gaba na dukkanin bil Adama. A matsayinta na babbar kasa mai tasowa, kuma kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin ta sami wasu fasahohin neman ci gaba, ta kuma bunkasa sosai a fannonin tattalin arziki da kimiyya da fasaha. Shi ya sa, take fatan yin mu'amala da sauran kasashen duniya a wadannan fannoni domin neman ci gaba cikin hadin gwiwa.

Bisa wani rahoton da kamfanin ba da lamunin inshora na Euler Hermes ya fitar a kwanan baya, an yi hasashen cewa, jimillar cinikayyar kasa da kasa da ke da nasaba da shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta karu da dala biliyan 117 a shekarar 2019, wadda za ta ba da gudummawa kaso 0.3 cikin dari ga yawan karuwar cinikayyar duniya. Idan aka yi la'akari da tabarbarewar tattalin arzikin duniya a bana, wannan gudummawar za ta fi jawo hankalin mutane.

A cikin jawabin da ya bayar a yayin taron dandalin tattaunawa na Davos, Mr. Wang Qishan ya nuna cewa, kasar Sin tana bin wata hanyar da ke dacewa da halin da kasar Sin ke ciki, wadda kuma take iya biyan bukatun zamanin yanzu. Nan gaba kuma za ta ci gaba da kyautata da raya tsarin gurguzu mai halin musamman na kasar Sin yayin da take bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gidanta.

A cikin shekaru fiye da dari shida da suka gabata, wani jami'in daular Ming ta kasar Sin Zheng He ya jagoranci kwamban jiragen ruwa zuwa kasashen yammacin duniya, a wancan lokacin, Sin tana sahun gaba a duniya a fannonin fasahohin kera jiragen ruwa, da zirga-zirgar jiragen ruwa, da karfin aikin soja, amma Sin ba ta yiwa kowace kasa mulkin mallaka ba. Wang Qishan ya bayyana cewa, lokacin da da na yanzu da wadanda ke tafe suna hade da juna, idan ana son a san yanayin kasar Sin, ya kamata a yi kokarin sanin tarihin kasar Sin, nan za a yi hasashe da makomar kasar Sin.(Lubabatu Bilkisu Bello Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China