Yayin zantawarsu, Pompeo da Taro Kono sun nanata kudurinsu na sake nazartar shirin kawar da makaman nukiliya na kasar Koriya ta arewa.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Robert Palladino, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, Pompeo da takwaransa na Koriya ta arewa Kang Kyung-wha sun yiwa juna karin bayani game da shirin kasashen na ganawa da Koriya ta Arewa.
Bugu da kari, mayan jami'an kasashen biyu, sun nanata kudurinsu kan kawancen dake tsakanin Amurka da Koriya ta kudu.
A ranar Jumma'ar da ta gabata ce,mataimakin shugaban kwamitin koli na jam'iyyar kwadago ta Koriya ta Arewa Kom Yong Chol ya gana da shi Pompoe da shugaba Trump na Amurka a birnin Washington.(Ibrahim)