in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rann: Dubban 'Yan Gudun Hijira Sun Tsallaka Zuwa Kamaru
2019-01-18 20:02:22 cri
Labarin da jaridar Leadership ta wallafa ya shaida cewa, tabarbarewar tsaro a jihar Borno, wanda ya jawo zazzafan gumurzu tare da dauki ba dadi a tsakanin sojojin Nijeriya da mayakan Boko Haram, ya tilasta dubban 'yan gudun hijira a karamar hukumar Kala-Balge a jihar, arcewa zuwa Kamaru.

Bayanai sun tabbatar da cewa, a farkon wannan mako, mayakan sun kai wani hari da ya jawo asarar rayukan mutum 10, kana wasu gwammai sun samu raunuka daban-daban, a garin na Rann, yayin da mayakan Boko Haram suka hadu da turjiyar sojojin.

A hannu guda kuma, gidaje da dama da barikin sojoji da ofishin majalisar dinkin duniya dake garin mayakan suka kona kurmus.

Ganau sun shaida cewa, lamarin ya tilasta wa 'yan gudun hijirar da ke garin arcewa zuwa kan iyakar Jamhuriyar Kamaru. Hadi da karin wasu dubun-dubatar 'yan gudun hijira wadanda ke zaune a Gamboru-Ngala. "Mun kai kimanin mutum 50,000 wadanda ke zaune a matsugunin 'yan gudun hijira a garin Rann. Wadanda kuma suke zaune kara-zube ba wani tallafi. Sai dai dubun-dubatar 'yan hijirar sun ga abin da ya fi musu kyau shi ne su bar garin Rann zuwa Kamaru, don gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.ko kuma tsoron salwantar rayukansu".

Majiyar ta kara da cewa, wannan yanayi na tsananin damuwa a Ngala shi ne yadda dubban mutane ke rayuwa a sararin Allah- tarwai. Wani babban abin bakin ciki shi ne, duk da wannan yanayin muku-mukun sanyi, amma a haka yara kanana tare da mata ke kwanciya a hunturu, babu ko zanin rufa jikin su. Wannan abin damuwa tare da kaico", in ji majiyar wacce ta nemi a sakaya sunanta.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China