in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na nuna kwazo wajen yaki da matsalar cin hanci da rashawa
2019-01-17 21:01:50 cri
Guizhou, wani lardi ne dake kudu maso yammacin kasar Sin, wanda ya yi suna sosai ta fuskar samar da wani shahararren nau'in giya mai suna Mouta, inda a yau Alhamis, gwamnatin lardin ta bullo da wata sanarwar haramtawa jami'an gwamnatin gami da iyalansu amfani da giyar Mouta don biyan bukatunsu na neman cin moriya. Wannan sanarwa ta bazu a kafar yada labarai ta Intanet a kasar Sin, al'amarin dake nuna cewa, kasar Sin na yin duk wani kokari na haramtawa jami'an gwamnati gami da dangoginsu amfani da matsayi ko mukamansu wajen biyan bukatu ko azurta kansu.

A yayin taron kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka shirya kwanan baya, an bayyana cewa, ayyukan murkushe matsalar cin hanci da rashawa a yanzu haka sun samu gagarumar nasara a kasar. Tun lokacin da aka gudanar da babban taro karo na 19 na wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya zuwa yanzu, hukumomin shari'a da sa ido na kasar Sin suna daukar tsauraran matakai iri daban-daban don yakar mutanen da suka aikata laifin cin hanci da karbar toshiya. A shekarar da ta shude wato 2018, gaba daya an yanke hukunci kan mutanen da suka aikata laifin da adadinsu ya kai dubu 620, ciki har da wasu manyan jami'an gwamnati guda 51. Bugu da kari, a cikin shekaru hudu a jere da suka wuce, kasar Sin ta tuso keyar mutane sama da dubu biyar wadanda suka aikata laifin cin hanci da rashawa daga kasashe da yankuna sama da 120, tare kuma da dawo da kudade fiye da Yuan biliyan goma.

Yaki da cin hanci da rashawa da ake ta yi ya samu goyon bayan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ma jama'ar kasar. Binciken da hukumar kididdigar kasar Sin ta yi ya nuna cewa, tun bayan babban taron wakilai karo na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, yadda Sinawa ke gamsuwa da ayyukan tsaftace jam'iyya da na yaki da cin hanci da rashawa yana ta karuwa a ko wace shekara, har ya wuce kashi 90 cikin 100. Ban da wannan kuma, yaki da cin hanci da rashawa ya kyautata yanayin ci gaban tattalin arzikin kasar. Rahoton yanayin gudanar da harkokin cinikkayya da bankin duniya ya fitar a shekarar 2018, ya nuna cewa, kasar Sin ta koma matsayin na 32, daga ta 46 a duniya a wannan fannin.

A baya, kasashen duniya suna nuna shakku game da niyyar kasar Sin wajen yakar cin hanci. Sai dai sannu a hankali, an fara ganin yadda kasar Sin ke cimma nasarori mataki mataki. Har ma kamfanin dillancin labarai na RIA Novosti ya ce, yadda kasar Sin ke daukar matakan yaki da cin hanci da rashawa daga dukkan fannoni ya kara tsaftace jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, tare da kara imanin al'umma kan jam'iyyar ta fannin gudanar da mulkin kasar.

Amma duk da haka, akwai sauran rina a kaba. Bayanai na nuna cewa, a shekarar da muke ciki kasar Sin za ta mayar da hankali kan matsalar cin hanci da rashawa dake damun fannonin manyan ayyukan da suka shafi ci gaba da tsaron kasa, da kuma kudi, za kuma a gudanar da bincike tare da yanke hukunci kan wadanda aka bankado suna hana ruwa gudu da barnata kudaden gwamnati. Musamman za a gudanar da bincike kan wadanda ke ba da kariya ga masu aikata laifuffuka, domin a samar da yanayi mai kyau na samun ci gaban kasar.(Masu fassara:Murtala Zhang, Bilkisu Xin, Lubabatu Lei)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China