in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan jarin da kasar Sin ta zuba wa kasashen waje kai tsaya ya kai dala biliyan 129.8 a bara
2019-01-17 11:31:16 cri

Ko da yake halin da kasashen duniya ya kasance ya kara sarkakiya da samun canji sosai a bara, amma yadda kasar Sin ta zuba jari ga kasashen waje, da hadin gwiwa tare da su, ya ci gaba da samu bunkasuwa yadda ya kamata ba tare da tangarda ba. Bisa alkaluman da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, da hukumar kula da kudin musaya ta kasar suka bayar, an ce, yawan jarin da kasar ta zuba wa kasashen waje kai tsaye ya kai dala biliyan 129.83 a shekarar 2018, wanda ya karu da kashi 4.2 cikin dari bisa na makamancin lokaci na shekarar 2017.

Bisa alkaluman da hukumomin gwamnatin kasar Sin suka bayar, an ce, yawan jarin da kasar ta zuba wa kasashen waje kai tsaye ya kai dala biliyan 129.83 a shekarar 2018, wanda ya karu da kashi 4.2 cikin dari bisa na makamancin lokaci na shekarar 2017. A ciki, yawan kudin da aka kebe ga ketare a fannin kasuwanci ya kai dala biliyan 9 da miliyan 330, wanda ya karu da kashi 105.1 cikin dari bisa na shekarar 2017; yawan kudin da aka kebe ga waje ta fuskar da ba ta shafi kasuwanci ba ya kai dala biliyan 120 da milyan 500, wanda ya karu da kashi 0.3 cikin dari bisa na shekarar 2017. Bugu da kari, yawan kudin shiga da aka samu daga aikin kwangila a ketare ya zarce dala biliyan 169, wanda ya karu da kashi 0.3 cikin dari bisa na shekarar da ta wuce. Yawan ma'aikatan da suka yi aiki a ketare kuwa ya kai kusan miliyan daya, wanda ya karu da dubu 17 bisa na makamancin lokacin shekarar 2017.

Han Yong, mataimakin shugaban sashen kula da zuba jari ga waje da hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki na ma'aikatar kasuwancin Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta zuba jari ga ketare ne a fannoni daban daban. Yana mai cewa,

"Yawancin kudin da kasar Sin ta kebe wa kasashen waje, ya shafi sana'ar haya, da ta ba da hidimar kasuwanci, da ta kere-kere, da ta sari da sai da kaya, da ta hakar ma'adinai, wadanda yawansu ya kai kaso 37, da kaso 15.6, da kaso 8.8 da ma kaso 7.7 cikin dari bi da bi. Ban da wannan, yawan kudin da aka keba wa sana'ar hidima ya kai dala biliyan 84.25, wanda ya kai karo 69.9 bisa dari. Sa'an nan babu sabbin jari a sana'o'in gidaje da motsa jiki, da nishadi, lamarin da ya shaida cewa, yadda aka zuba jarin ya kasance yadda ya kamata."

Haka zakila ma, kasar Sin ta kara kirkiro hanyoyin zuba jari ga waje a bara. Kamar kamfanonin kasar da dama sun sayi kadarorin waje, da tattara yawan kudaden gudanarwa a ketare. Bugu da kari, kamfanonin Sin sun yi hadin gwiwa tare da kamfanonin kasashen Birtaniya, Jamus, Faransa, Singapore da dai sauransu, bisa fiffikon da suke da shi domin gudanar da aiki tare a kasashen Asiya da Afirka. Wasu kamfanoni masu zaman kansu kuwa sun kara zuba jari ga waje, baya ga yadda aka samu ci gaba sosai wajen gina yankin hadin kan tattalin arziki da cinikayya a ketare, kana aka samu bunkasuwa lami lafiya ta fuskar zuba jari bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya". Mr. Han Yong ya furta cewa,

"Yawan kudin da kamfanoninmu suka kebe kai tsaye ga kasashe 56 da shawarar 'ziri daya da hanya daya' ta shafa, ta fuskar da ba ta kasuwanci ba, ya kai dala biliyan 15 da miliyan 640 a bara, wanda ya karu da kashi 8.9 cikin dari, inda jimillar ta kai kashi 13 cikin dari bisa na dukkan kudin da Sin ta kebe ga waje. Ban da haka kuma, yawan kudin shiga da Sin ta samu a fannin gudanar da ayyukan kwangila a kasashe 63 da shawarar ta shafa ya kai dala biliyan 89 da miliyan 330, wanda ya kai kashi 52 cikin dari bisa na dukkan kudaden."

Baya ga hakan kuma, aikin kwangila da kasar Sin ta gudanar a wasu kasashe, ya sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewarsu, wanda ya samar musu guraban ayyukan yi kimanin dubu 800. Han ya ce,

"Yawancin ayyukan kwangila da aka gudanar a waje sun shafi sana'o'in zirga-zirga, da gine-gine, da wutar lantarki, wadanda yawansu ya kai kashi 66.5 cikin dari. Kuma ayyukan sun kyautata manyan ababen more rayuwa na kasashen, har ma sun samar da guraban aikin yi kimanin dubu 842, lamarin da ya amfani kasashen sosai. A waje daya kuma, sakamakon wadannan ayyukan kwangila, kasarmu ta fitar da na'urori da kayayyakin da darajarsu ta kai kusan dala biliyan 17 zuwa ketare, adadin ya karu da kashi 10.4 cikin dari bisa na shekarar 2017."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China