in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ingiza ci gaban kasuwanci mai inganci
2019-01-16 10:57:24 cri

Kwanan baya a nan birnin Beijing, ministan kasuwancin kasar Sin Zhong Shan ya bayyana cewa, a cikin sabuwar shekarar 2019 da muke ciki, ma'aikatar kasuwancin kasar Sin za ta kara sa kaimi kan ci gaban kasuwanci mai inganci.

Ministan kasuwancin kasar Sin Zhong Shan ya bayyana cewa, a shekarar 2019, kasar Sin za ta ingiza ci gaban kasuwanci mai inganci ta hanyoyi daban daban, misali sa kaimi kan sayayya, da samun daidaito wajen cinikayyar waje da samun jarin waje, da gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu, da daidaita rigingimun tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninta da kasar Amurka, da ingiza aikin gina yankunan gwajin cinikayya maras shinge, da kafa tashar ruwan cinikayya maras shinge da sauransu, ta yadda za ta cimma burin kasance kasa mai karfi wajen raya tattalin arziki da cinikayya a fadin duniya.

A shekarar 2018, adadin kudin da aka kashe kan hajojin da suka saya ya kai kudin Sin yuan biliyan dubu 38, adadin da ya karu da kaso 9.1 bisa dari idan aka kwatanta shi da na shekarar 2017, a bayyane ne an lura cewa, sayayya tana taka rawa mafi muhimmanci kan ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin a cikin shekaru biyar da suka gabata, a sa'i daya kuma, kasar Sin ta kasance kasa mafi girma wajen sayayya, game da wannan, ministan kasuwancin kasar Zhong Shan ya bayyana cewa, kasuwa tana da muhimmnci matuka, a don haka ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta tsai da kuduri cewa, za ta kara samar da kayayyaki masu inganci ga masu sayayya a bana, yana mai cewa, "Idan muna son ingiza sayayya a kasar, dole mu sanya kokari a fannoni uku, na farko, kara ingancin sayayya a birane, na biyu, sa kaimi ga manoma, su kara kashe kudin sayayya a kauyuka, ta hanyar samar musu hidimar sayar da kayayyaki ta yanar gizo, da kara sayar da kayayyakin masana'antu a kauyuka, da kuma kara sayar da kayayyakin aikin gona a birane, ta haka za a kara habaka kasuwannin birane da kauyuka tare, kuma yadda ya kamata. Na uku kuma, a raya sayayya a fannin samar da hidima. Bana kasar Sin za ta kara gina cibiyoyin samar da hidima a birane, da kuma kauyuka, domin yaki da talauci, tare kuma da samar da guraben aikin yi da yawansu zai kai dubu 150 a kauyukan kasar."

Bisa alkaluman da aka samu, an ce, darajar adadin cinikayyar wajen kasar Sin a shekarar 2018 ya kai kudin Sin yuan biliyan 30510, adadin da ya karu da kaso 9.7 bisa dari idan aka kwatanta shi da na shekarar 2017, har ma ya kai matsayin koli a tarihi, kana adadin jarin wajen da kasar Sin ta yi amfani da su, ya kai dalar Amurka biliyan 135, adadin da ya karu da kaso 3 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2017, hakan ya sa kasar Sin ta kai sahun gaba a fannin a fadin duniya.

Jami'in ya kara da cewa, nan gaba muhallin kasuwancin kasar Sin zai kara kyautata, kamar yadda alkaluman da bankin duniya ya samar, kana a watan jiya kwamitin cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka na kasar Amurka, ya fitar da wani sakamakon bincike, inda ya bayyana cewa, kamfanonin kasar Amurka kaso 90 bisa dari suna ganin cewa, kasar Sin daya ce daga cikin muhimman kasuwannin kasarsu, kana kamfanonnin kaso 95 bisa dari sun bayyana cewa, za su kara zuba jari ko ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu a kasar Sin a cikin shekara daya mai zuwa. Zhong Shan ya fayyace cewa, kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga 'yan kasuwa ketare domin su kara zuba jari a kasar, yana mai cewa, "Kasar Sin za ta kara kyautata aikin jawo hankalin masu zuba jari a fannoni uku, wato kara habaka fannonin bude kofa, da kara samun jarin waje ta hanyar gudanar da manyan ayyuka, da kuma kara gina yanki, ko tashar ruwa, ta gudanar da cinikayya maras shinge, misali a birnin Shanghai ko lardin Hainan."

A cikin sabuwar shekara ta 2019, yanayin da kasashen duniya ke ciki yana da sarkakiya, kila ne tattalin arzikin duniya ba zai samu ci gaba cikin sauri ba, jami'in ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi kokari domin samun daidaiton cinikayyar waje, ya ce, "Da farko, kasar Sin za ta kara habaka kasuwanni guda 30 a ketare, domin samar da damammaki ga kamfanonin kasar. Na biyu, kara rage kudin harajin kamfanoni masu zaman kansu domin sa kaimi ga ci gabansu. Na uku, kara kyautata ingancin kayayyakin da ake fitar da su zuwa ketare, tare kuma da gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 2 lami lafiya."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China