in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sanannun 'yan jaridun kasashen dake kan hanyar siliki sun zanta da malaman addinin Musulunci a jihar Xinjiang
2019-01-14 19:54:56 cri

A kwanakin baya ne, wata tawagar sanannun 'yan jaridun kasashen dake kan hanyar siliki karo na bakwai da babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gayyato su zuwa kasar Sin, ta yi tattaki zuwa kwalejin koyon ilimin addinin Musulunci ta Xinjiang dake birnin Urumqi, inda 'yan jaridu daga kasashen Turkiyya da Masar da Afghanistan da Pakistan da Bangladesh da Sri Lanka wadanda ke yankunan dake cikin shawarar 'ziri daya da hanya daya' suka kara fahimtar manufar bin addini cikin 'yanci ta gwamnatin kasar Sin.

Lokacin da muka shiga cikin dakin karatu a kwalejin koyon ilimin addinin Musulunci ta Xinjiang, muna iya jin muryar daliban da ke karatu. Wani dalibi dan kabilar Uyghur mai suna Kawsar zai kammala karatunsa a makarantar nan da watanni shida masu zuwa. Yayin da yake zancen kan aikin da yake yi a nan gaba, ya bayyana cewa:

"Zan koma gida, don koyawa mabiya addini ilimin da na koya a nan."

A nasa bangaren, shugaban kwalejin nan na koyon ilimin addinin Musulunci ta Xinjiang, kana mataimakin shugaban kungiyar addinin Musulunci ta kasar Sin, Abdulrekep Tumiaz ya ce, a halin yanzu akwai dalibai 630 wadanda ke karatu a kwalejin, kuma darussan da ake koyawa daliban sun hada da yare da kalmomin Sinanci, da ilimin addini da sauransu. Haka kuma kwalejin ya bude wasu rassansa takwas a wurare daban-daban na jihar Xinjiang. Abdulrekep Tumiaz ya bayyana cewa:

"A yayin da suke karatu a makaranta, gwamnatin jihar Xinjiang tana bawa kowane dalibi tallafin kudin abinci na Yuan dari shida a kowane wata. Kana kuma, dalibai daga kauyukan yankunan kudancin jihar ba sa biyan kudin dakin kwana. Bugu da kari, kashi 90 bisa dari na daliban makarantar za'a ba su tallafin kudin karatu da kyautar kudin karatu na Yuan dubu hudu a kowace shekara."

Wakilin gidan talabijin na ATV na kasar Turkiyya Erdal Kurucay, yana daya daga cikin 'yan jaridun da suka kai ziyara kwalejin ya bayyana farin-cikinsa yana mai cewa:

"Muna ganin makaranta tana da kyau, ga na'urorin koyarwa na zamani, abu mafi muhimmanci shi ne muna ganin dalibai na kokarin karatun Alkur'ani mai tsarki. Lokacin da muka zo wannan kwalejin, cike muke da imani da yarda."

A kwalejin kuma, gwamnatin jihar Xinjiang ta gina wani masallaci don biyan bukatun dalibai musulmi ta fannin yin Ibada, kuma dalibai sama da 1200 za su iya sallah a lokaci guda.

A yayin da suka ziyarci kwalejin, Abdulrekep Tumiaz ya bayyanawa 'yan jaridun kasashen waje ainihin manufofin gwamnatin kasar Sin kan addini, inda ya yi amfani da jimloli uku don amsa tambayoyin kasashen waje game da batun bin addini cikin 'yanci a kasar Sin, inda ya ce:

"Gwamnatin kasar Sin ta rubuta batun tabbatar da 'yancin jama'a na bin addini a cikin kundin tsarin mulkin kasar, da aiwatar da dokoki da ka'idoji na kare hakkin bin addini cikin 'yanci, da nufin bada tabbaci ga mabiya addini don su yi addinansu yadda ya kamata. Na biyu, gwamnatin kasar Sin ta yi kira ga mabiya addinai da wadanda ba su da addini da su mutunta juna, da zaman jituwa tare. Na uku shi ne, gwamnatin kasar Sin na aiwatar da manufar raba mulkin kasa da addini, kuma babu wani addini da zai yin harkokinsa wadanda suka saba wa kundin tsarin mulki da dokokin kasar, kuma ko ta yaya ba za'a amince da kowane addini ya yi katsalandan cikin harkokin aiwatar da mulki da dokoki da tarbiyya da aure na kasar Sin ba."

A nata bangaren, wata edita daga mujallar Al-Ahram Ektassdy ta kasar Masar mai suna Samia Fakhry Mansour ta ce, maganar Abdulrekep Tumiaz ta burge ta kwarai da gaske.

"Shi mutum ne mai sabon tunani wanda ya dace da zamanin da muke ciki, kuma bai hada batun addini da harkokin siyasa waje guda ba. Abun da ya burge ni shi ne, ya jaddada yadda 'yan ta'adda suka jirgita ayoyin Alkur'ani mai tsarki, suke fakewa da harkokin kabilu da addinai, inda suke yayata tsattsauran ra'ayin addini da yunkurin kawo baraka, da kuma rura wutar kiyayya tsakanin kabilu."

Shi ma a nasa bangaren, wani dan jarida daga gidan rediyon FM98 Dosti na kasar Pakistan, Tassawar Zaman Babar ya bayyana cewa, kafofin watsa labaran yammacin duniya na yunkurin shafawa gwamnatin kasar Sin kashin kaji kan manufofinta game da harkokin addini, amma abubuwan da ya ji ya kuma gani da idonsa ya shaida cewa, zargin da kafofin watsa labaran kasashen yamma suka yiwa kasar Sin ba shi da tushe balle makama, inda ya ce:

"Mutanen da suke yunkurin yada shaci fadi, ya kamata su kawo ziyarar gani da ido, ko kuma su bari mu bayyana musu ainihin abubuwan da suke wakana a nan, ta yadda za su kara fahimtar gaskiyar abun dake faruwa a nan."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China