Mataimakin shugaban hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, kana mataimakin babban darektan aikin binciken duniyar wata Mr.Wu Yanhua ya bayyana a yau Litinin a nan birnin Beijing cewa, bayan da na'urar bincike ta Chang'e-4 ta kammala aikinta yadda ya kamata, za kuma a fara gudanar da aikin binciken duniyar wata a zagaye na hudu a karshen wannan shekara, inda za a harba na'urar bincike ta Chang'e-5 zuwa doron duniyar wata tare da dawo da wasu samfura daga can, kana nan da shekarar 2020, kasar Sin za ta fara gudanar da aikin binciken duniyar Mars a karo na farko.
Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin tana son hada kai da kasashen duniya wajen bunkasa harkokin binciken sararin samaniya bisa tushen zaman daidaito da samun moriyar juna.(Lubabatu)