in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zantawa da Solomon Elusoji dan jaridar This Day daga Najeriya
2019-01-15 19:41:18 cri


A wannan makon shirin ya karbi bakuncin wani matashin dan jarida ne wanda ke aiki a jaridar This Day daga tarayyar Najeriya mai suna Solomon Elusoji, wanda ya kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin karkashin gayyatar da cibiyar yada labaru ta kasashen Sin da Afrika ta yi masa a wani shirin karawa juna sani da cudanyar harkokin aikin jarida na kasar Sin da kasashen Afrika na tsawon watanni goma.

Solomon ya bayyana cewa, wannan ziyara ta kasance mai ciki da alfanu da karin ilmi a gare shi musamman sakamakon yadda ya samu damar ziyarar larduna sama da 10 da yankuna daban daban na kasar Sin don ganawa da wasu ma'aikata da jami'an hukumomin gwamnatocin kasar Sin domin kara fahimta game da yadda kasar Sin take da yanayin al'adunta da tattalin arzikinta, da ci gabanta, da yanayin zamantakewar al'ummarta da kuma yanayin karfin ci gaban fasahohinta da dai sauransu. A cewar dan jaridar, wannan shi ne karon farko da ya kawo ziyara kasar Sin kuma wannan wata babbar dama ce da ya samu don kara samun ilmi da yin kudanya da al'ummar Sinawa har ma da baki 'yan kasashen Afrika.

Game da yadda ya kalli yanayin kasar Sin, ga abin da yake cewa:

"Kasar Sin tana da ban sha'awa saboda watakila idan kana hangen kasar ne daga waje, to ba lalle ne ka fahimci hakikanin irin ci gaban da kasar ta samu cikin sauri ba tun bayan da ta aiwatar da manufarta na yin gyare gyare a cikin gida da bude kofa ga waje a shekarar 1978, wani abu guda da lura da shi a kasar Sin shi ne, yadda take da ingantattun kayayyakin more rayuwa kamar gine ginen gwamnati da ingantattun hanyoyin mota, da tsarin wutar lantarki, gaskiya lamarin yana da kayatarwa, daga Shanghai zuwa Jiangsu zuwa Hangzhou a gaskiya yanayin kayayyakin more rayuwa a duk fadin kasar yana da matukar inganci".

Ya ce ko da yake, wannan shi ne karon farko da ya ziyarci kasar Sin, amma zuwansa ya ba shi damammaki masu yawa, musamman kafin zuwansa kasar Sin ba shi da wani aboki ko kuma wanda ya sani a kasar Sin, amma a yanzu ya yi mu'amala da abokai masu yawan gaske, ya hadu da abokai Sinawa masu yawa kuma wannan shi ne ya ba shi dama ya samu karin fahimtar yadda kasar Sin take, da al'adun kasar, har ma ya samu damar fara koyon yaren Sinanci a matakin farko. Ya ce bayan shafe tsawon watanni 10 a kasar Sin, ya samu kwarin gwiwar fahimta yadda hakikanin kasar Sin take sabanin yadda yake kallonta a lokutan baya da ma yadda duniya ke kallon kasar.

Mista Solomon ya ce, babban abin da ya fi burge shi game da kasar Sin shi ne, yadda shugabancin kasar ke gudana da irin kwazon da mahukuntan kasar ke nunawa wajen gina kasa da harkokin tafiyar da mulki. Ya ce:

"Game da tsarin siyasarta, ya sha banban da yadda kasashen yammacin duniya ke tafiyar da nasu tsarin, ta wannan fannin hakika abin yana da matukar ban sha'awa, musamman duba da yadda gwamnatin kasar ta himmatu wajen tsame mutanenta daga kangin talauci, wannan gaskiya babban al'amari ne mai girman gaske, hakazalika duba da yadda kasar ta samu bunkasuwa cikin wasu 'yan shekaru hakika wannan abin ban sha'awa ne kuma wannan shi ne abin da nake son zan kara yin nazari a kansa, sa'annan zan cigaba da yin rubuce rubuce na a kansa nan da wasu shekaru masu zuwa."

Game da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Afrika kuwa, dan jaridar ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika matashiyar dangantaka ce wadda ke ci gaba da habaka sannu a hankali, amma kuma a cewarsa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu dadaddiyar dangantaka ce wadda ta shafe wasu karnoni masu yawa, ya ce dangantakar dake tsakaninn bangarorin biyu ta kara karfi musamman a cikin karni na 21, a halin yanzu yanayi alakar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika abu ne mai faranta rai, kuma ya bayyana kyakkyawar fatansa na ganin bangarorin biyu sun kara kyautata mu'amalar dake tsakaninsu kuma akwai wasu damammaki na moriyar juna masu yawan gaske, kana akwai bukatar daukar matakai na kara karfafa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu da kuma lalibo wasu mihimman hanyoyin kara kyautata mu'amala da yin aiki tare da juna da kuma neman wasu muhimman hanyoyin kirkire kirkire domin tabbatar da ganin an samu bunkasuwar mu'amala da hadin gwiwa da fahimtar juna domin amfanawa al'ummomin kasashen Sin da na Afrika baki daya, musamman karkashin yarjejeniyoyin ayyukan ci gaba na hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.

Idan za'a iya tunawa, a farkon watan Satumban shekarar 2018 ne kasar Sin ta karbi bakuncin muhimmin taron kolin dandalin hadin kan Sin da kasashen Afrika wato FOCAC a takaice wanda aka gudanar da taron a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Taron wanda ya samu halartar ilahirin shugabanni da manyan jami'an hukumomin gwamnatocin kasashen Afrika gami da wakilan hukumomin kasa da kasa, inda suka gana da mahukuntan kasar Sin domin karfafa zumunci, da kyautata mu'amala, da kuma kulla yarjejeniyoyin diflomasiyya, ciniki, tattalin arziki da dai sauransu domin cin moriyar al'ummomin bangarorin biyu. Najeriya tana daga cikin kasashen Afrika da suka halarci taron kolin na Beijing FOCAC 2018, inda babbar tawaga ta zo daga Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasar Najeriyar Muhammadu Buhari. Game da tambayar da aka yiwa Solomon ta cewar, ko menene ra'ayinsa dangane da dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriyar, ya ce ya samu nasarar tattaunawa da wasu daga cikin ministoci da manyan jami'an gwamnatin Najeriya, kuma bisa irin bayanan da ya samu a yayin tattaunawar tasu shi ne, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana da kyakkyawan burin kyautata mu'amalar hadin gwiwa tsakanin gwamnatinsa da gwamnatin kasar Sin, musamman wajen yin hadin gwiwa da kasar ta Sin don tallafawa Najeriyar wajen gudanar da muhimman ayyukan samar da kayayyakin more rayuwar jama'a wadanda su ne Najeriyar ta fi bukata a yanzu kamar ingantattun hanyoyin mota, layin dogo, lantarki wadanda za su taimkawa kasar wajen samar da guraben ayyukan yi ga al'umma da kyautata yanayin zamantakewar jama'ar kasar. Ya ce idan wadannan ayyukan da aka cimma yarjejeniyar hadin gwiwa kansu tsakanin kasar Sin da Najeriya aka samu nasarar kammala su kamar yadda aka tsara gudanarwa tun da farko, to za su yi matukar amfanawa dukkan bangarorin biyu.

A shekarar 2018 ne kasar Sin ta cika shekaru 40 tun bayan aiwatar da manufar yin gyare gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje, hakika, duniya ta shaida irin manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma cikin wadannan gwamman shekaru. Da aka tambayi dan jarida Solomon ko menene ra'ayinsa dangane da irin darasin da ya kamata kasashen Afrika su koya daga iri ci gaban da kasar Sin ta samu cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, sai ya ce:

"Abu ne mai sauki, ka sani, dogaro da kai shi ne komai, wani muhimmin batu game da ci gaba shi ne, babu wani mutum da zai gina maka kasarka, dole ne ka gina kasarka da kanka, dole ne ka bullo da dabaru iri daban daban, babu wani mutum da zai zo daga wata kasar waje ya gina maka kasarka dole ka yi tunanin matakan da za ka dauka domin magance matsalar talauci a kasarka, kasar Sin ta samu wannan nasara a cikin shekaru 40 da suka gabata, a shekarun baya kasar Sin ba ta cikin kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki, amma a yanzu tana sahun gaba, muhimmin abu shi ne amfani da tsarin siyasa mafi dacewa, da samun shugabanci na gari, idan aka samu shugabannin da za su tsaya kai da fata wajen tabbatar da gina kasa da dora kasar kan kyakkyawar hanyar neman ci gaba, hakika Afrika tana da dimbin matasa, tana da albarkatun kasa masu yawan gaske, Afrika tana da muhimman damammakin tsara dabaru musamman ta yadda za ta tsara makomar bunkasa ci gaban tattalin arzikinta a shekaru masu zuwa a nan gaba, hakika babban abin da muke bukata shi ne mu samu tsarin shugabanci na gari wanda zai dora kasashenmu kan kyakkyawar turba zuwa mataki na gaba."

Kasar Sin da Najeriya suna da kamanceceniya na yawan matasa, matasa su ne kashin bayan gina ci gaban kowace kasa a duniya. Solomon ya jaddada cewa, kamata yayi gwamnatocin kasashen Afrika su samar da yanayi mai kyau da damammaki, ta yadda matasa za su samu hanyoyin dogaro da kansu ba tare da dogaro kan gwamnatoci don samar da guraben aiki ba. Shugabanci na gari shi ne muhimmin batu da zai tabbatar da samun kyakkyawan ci gaba na kasashen Afrika da al'ummar nahiyar.

Dangane da batun hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika ta fuskar aikin yada labarai kuwa, Solomon ya ce, wajibi ne bangarorin biyu su bayyana ainihin muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban bangarorin ba tare bada kofa ga wasu kasashen duniya su yi katsalandan dangane da iri abubuwan dake faruwa a yankunan Sin da Afrika ba. Ya buga misali game da kalaman wani marubuci daga Najeriya Chinua Achebe, wanda ya taba bayyana cewa idan ba ka farin ciki da yadda wani yake yada labarinka, to ka daina yin korafi sai ka fara bada labarinka da kanka. Solomon ya ce, kasar Sin ta dauki matakai da suka dace wajen bayyana aihinin labarinta da kanta ba tare da barin wasu daga gefe suna bada labarin da ya shafe ta ba. Ya gargadi kasashen Afrika da su yi hattara wajen tabbatar da dogaro da kansu, musamman wajen yin amfani da damarsu na bada labaran da suka shafe su ba tare da barin al'amurran da suka shafe su kan kasashen yammacin duniya ba. Dole ne kasashen Afrika su dinga tsara labarai da suka shafi hakikan yanayin da suke ciki, labarai na gaskiya wadanda babu shaci fadi ko kuma karin gishiri a cikinsu.

Daga karshe ya bayyana irin darussan da ya koya har ma da irin kalubalolin da ya fuskanta musamman bambancin yanayi da ya tsinci kansa musamman yanayin sanyi, bambancin yare da dai sauransu, baki daya ya bayyana zamansa a kasar Sin a matsayin muhimmin ci gaba ga rayuwarsa da kuma bangaren aikinsa na jarida, wanda ya ba shi damammaki masu yawa na kara fahimtar yanayin kasar Sin, da al'adunta, da zaman rayuwar al'ummar Sinawa, da kuma irin muhimman ci gaban da kasar Sin ta samu musamman a cikin shekaru 40 da suka gabata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China