Wasu jami'an MHRSS sun shaidawa taron manema labarai cewa, gwamnati za ta ragewa kamfanoni nauyin lura da ma'aikata, yayin da a yanzu haka ake ci gaba da gudanar da bincike game da tsarin ragewa kamfanoni nauyin inshorar ma'aikatan da suke dauka aiki a fadin kasar.
Jami'an sun ce kamfanonin da ba su sallami ma'aikata daga bakin aikin su ba, za su iya karbar rabin kudin da suka biya a baya na inshorar rashin guraben ayyuka, domin karfafa masu gwiwa.
Wani jami'in gwamnatin kasar ta Sin ya bayyana cewa, a bana kasar za ta fuskanci karin matsin lamba na neman guraben ayyukan yi, duba da cewa sama da mutane miliyan 15 za su karu a kasuwar neman ayyuka ta biranen kasar, ciki hadda daliban da ake sa ran za su kammala jami'o'i kimanin su miliyan 8.34.
Wani taron koli na raya tattalin arzikin kasar Sin da ya gudana a watan Disambar bara, ya amince da kasancewar batun daidaita samar da guraben ayyukan yi, a matsayin batun dake sahun gaba, a jerin manufofin gwamnatin kasar Sin a shekarar ta 2019. (Saminu Hassan)