in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin kasan zamani na farko na Najeriya ya cika kwanaki 900 da fara aiki lami lafiya
2019-01-13 16:48:01 cri
Fasinjojin dake ta'ammali da jirgin kasan zamani dake zirga-zirga daga Abuja babban birnin Najeriya sun bayyana gamsuwarsu bayan da suka samu bayanai dake nuna cewa kimanin kwanaki 900 ke nan tun bayan fara amfani da jirgin kasa amma harkokin na gudana lami lafiya.

Wata muryar wani mutum dake bada sanarwa ga jama'a ta ayyana cewa, jirgin kasan ya shafe kwanaki 900 kenan yana cigaba da a zirga zirga ba tare da fuskantar wasu manyan haddura ba.

Mutane da dama abin ya burge su, kuma sun bayyana gamsuwarsu game da yadda jirgin kasan yake tafiyar da harkokinsa tsakanin Abuja-Kaduna, shi ne jirgin kasa na zamani na farko a Najeriya da kuma yammacin Afrika.

Jirgin kasan ya fara aikin zirga zirga daga Abuja-Kaduna ne a ranar 27 ga watan Yulin shekarar 2016, bayan da wani kamfanin gine gine na (CCECC) na kasar Sin ya kammala aikin gina shi,kuma hukumar kula da sufurin jiragen kasa na Najeriya (NRC), shi ne babban mai kula da aikin sufurin.

Yakubu Garba, wani fasinja ne dake yawan amfani da jirgin kasan daga Abuja-Kaduna, ya bayyana irin gamsuwar da yake samu tun bayan da ya fara ta'amallai da jirgin kasar.

"Wannan babbar nasara ce. Daya daga cikin muhimmanci amfani da wannan jirgin kasan shi ne, akwai cikakken tsaro, musamman bisa lura da yanayin kalubalolin tsaron da ake fuskanta a Najeriya," Garba ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a babbar tashar jirgin kasan dake Idu.

Adamu Ahmed, wani mai yawon bude ido dan kasar waje, wanda ya hau jirgin kasan a karon farko ya bayyana cewa, jirgin kasan ya bashi cikakkiyar damar kallon yankunan karkarar Najeriya cikin lumana da tsaro, kasancewar jirgin kasan ya hada wasu daga cikin yankunan biranen kasar.

Jirgin kasan na Abuja-Kaduna shi ne layin dogo na zamani na farko wanda aka kaddamar a Najeriyar. Shi ne kuma kashin farko na aikin layin dogo na zamani daga Lagos-Kano.

An bullo da sabon jirgin kasan na zamani ne a Najeriya da nufin maye gurbin tsoffin jiragen kasan da ake amfani da su, inda aka fadada shi tare da kara masa saurin tafiya.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Fidet Okhiria, manajan daraktan hukumar jiragen kasan Najeriya NRC, yace ana matukar samun karuwar masu ta'ammali da jiragin kasan tun daga shekarar da aka kaddamar da fara zirga zirgar jiragen kasan.

A watan jiya, sama da fasinjoji 80,000 ne aka yi jigilarsu tsakanin Abuja-Kaduna a jirgin kasan, adadin da ya ninka yawan fasinjojin da ake samu a lokacin baya, in ji jami'in.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China