Miao Wei ya ce, Sin na da babbar kasuwa, da cikakken tsarin sana'o'i, gami da karfin yin kirkire-kirkire, haka kuma tana da kyawawan muhimman ababen more rayuwar jama'a, da yanayin kasuwanci mai kyau, al'amarin da ya sa take da kwarewa, wajen tinkarar kalubale mai sarkakkiya daga kasashen waje.
Miao Wei ya kara da cewa, domin samar da wani kyakkyawan yanayi na ci gaban kamfanoni daban-daban, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da kyautata yanayin sana'ar kere-kere, da nuna himma da kwazo, wajen rage haraji, da kara bude kofa ga kasashen waje, musamman ma tabbatar da aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje, a fannonin da suka shafi kirar motoci, da jiragen ruwa, da jiragen sama. (Murtala Zhang)