A yayin taron kwamitin sulhun MDD, Wu Haitao, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD, ya bukaci kasa da kasa dasu kara taimakawa kasashen yammacin Afrika da yankin Sahel, a kokarin da suke na yaki da muggan laifuka da ta'addanci a kan iyakokin kasashen.
"Baki daya halin da ake ciki a yammacin Afrika da yankin Sahel akwai zaman lafiya, amma har yanzu kasashen suna fuskantar barazanar masu tsattsauran ra'ayin addini, da hare haren kungiyoyin 'yan ta'adda, da karuwar munanan laifuka da kuma bala'o'i daga idallahi", in ji shi.
Domin shawo kan wadannan kalubaloli, Wu ya ce magance wadannan matsaloli tun daga tushe shi ne abu mafi muhimmanci, don haka kamata yayi al'ummar kasa da kasa su mayar da hankali wajen taimakawa cigaban wadannan kasashen kana a taimaka musu wajen warware manyan kalubalolin da suka fi damunsu.
Da yake karkare jawabinsa, wakilin na kasar yayi alkawarin cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da kasa da kasa wajen taka muhimmiyar rawa don samun nasarar wanzar da tsaro da zaman lafiya a nahiyar Afrika.