Mai magana da yawun babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya bayyana cewa, ma'aikatan OCHA sun bayyana cewa, tun a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, an janye ma'aikatan jin kai 260 daga yankunan dake fama da tashin hankali, lamarin da ya katse taimakon jin kai da ake baiwa dubban daruruwan mutanen dake bukatarsa.
Da yake yiwa taron manema labarai karin haske kan lamarin, Dujarric ya ce, yayin da wasu ma'aikatan jin kan suka fara komawa wuraren aikinsu, rashin tsaro kuma na kawo cikas ga gudanar ayyukan jin kai kamar yadda aka saba.
Mai magana da yawun hukumar OCHA a Najeriya Erdward Kallon ya bayyana damuwa kan yadda tashin hankali a yankin arewa maso gabashin kasar ya raba mutane da dama da matsugunansu.
OCHA ta ce, ma'aikatan agaji 260 da aka janye, ita ce mafi yawa da hukumar ta yi, tun lokacin da ta fara kawo dauki a shekarar 2016.
Hukumar ta ce, sama da mutane miliyan 7 ne ke matukar bukatar taimako, sakamakon yakin da aka kwashe shekaru 10 ana tafkawa.(Ibrahim)