in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu sanannun 'yan jaridun kasashen dake hanyar siliki sun fara ziyara a kasar Sin
2019-01-10 13:19:51 cri

 

A kwanakin baya ne wato ranar 7 ga wata, wasu sanannun 'yan jaridun kasashen dake kan hanyar siliki suka fara ziyara a kasar Sin daga nan birnin Beijing.

Ziyarar wadda ta zama irinta ta bakwai, da babban gidan talabijin da rediyo na kasar Sin wato CMG da ofisoshin jakadancin Sin dake kasashen da abun ya shafa suka shirya tare, tana kunshe da shahararrun mutane daga bangarorin al'adu da watsa labarai na kasashe daban-daban, ciki har da Turkiyya, da Masar, da Afghanistan, da Pakistan.

A ranar 7 zuwa 8 ga wata, wadannan baki sun kai ziyara kamfanoni da wuraren tarihi da dama a nan birnin Beijing, ciki har da kamfanin samar da bayanai da sadarwa na jiragen kasa na kasar Sin wato CRSC, da kamfanin kimiyiya da fasaha na BOE, da kamfanin cinikin kayayyaki ta Intanet na JD, tare kuma da fadar sarakunan gargajiya ta kasar Sin wato Forbidden City a turance da babban dakin adana kayan tarihi na kasa da sauransu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China