in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta dauki sabbin matakan sanya wa al'ummominta kaimin sayayya da kuma kara bude kofarta ga waje
2019-01-09 19:59:43 cri

A kwanan baya, mataimakin shugaban kwamitin raya kasa da gyare-gyare na kasar Sin Mr. Ning Jizhe, ya bayyana a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin cewa, kasar Sin za ta fitar da wasu manufofin sanya wa al'ummominta kaimin sayayya, da kara zuba jari na gari, domin tabbatar da ci gaban tattalin arzikinta kamar yadda ya kamata. A waje daya, a shekarar 2019, za ta bude kofofin wasu fannoni ga jarin waje domin tabbatar da kara bude kofarta ga waje.

A yayin taron kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS kan harkokin tattalin arziki da aka shirya a watan Disamba, an tsai da kudurin cewa, ya zama wajibi a bunkasa wata kasuwa mai karfi sosai a cikin gidan kasar Sin. Sabo da haka, a lokacin da yake ganawa da manema labaru, Mr. Ning Jizhe ya bayyana cewa, yanzu, yawan kudin shiga da mazauna kasar Sin ke samu yana ta karuwa, kuma bayyane take cewa suna son kara sayayya, musamman sayen kayayyaki masu inganci sosai. Sakamakon haka, dole ne matakan da hukumomin gwamnati za su dauka su yi daidai da bukatun da mazauna kasar suke da su, ta yadda za a tabbatar da ganin sayayya ta taka muhimmiyar rawa, kamar yadda ya kamata ga ci gaban tattalin arzikin kasar. Mr. Ning Jizhe yana mai cewa, kwamitinsa zai fitar da matakan sa kaimi ga mazauna kasar, ta yadda za su kara sayen motoci, da na'urorin wutar lantarki da ake amfani da su a cikin gida, da dai sauran kayayyakin dake jawo hankulan mazauna kasar.

Jami'in ya ce, "A shekarar da ta gabata, an sayar da motoci da yawansu ya kusan kaiwa miliyan 30 a kasar Sin, sai dai har yanzu za mu iya ba da jagoranci ga jama'ar kasar, domin su kashe kudi cikin kima, da rage gurbata muhalli, gami da kara sayen ingantattun kayayyaki. Da ana sayar da motoci a birane ne kawai, amma yanzu ana sayar da su a kauyuka, don haka muna la'akari da wasu dabarun da za a dauka, don sa kaimi ga manoma domin su kara sayen motocin."

Ning Jizhe ya kara da cewa, a bana kwamitin raya kasa da gyare-gyare na kasar Sin zai gabatar da wasu sabbin manufofi, masu alaka da hayar gidaje, da hidimar aikin gida, da kula da tsoffi da yara, game da neman daidaita wasu tsoffin manufofi a wadannan fannoni. Sa'an nan zai kau da shingayen da suka hana ruwa gudu a fannin zuba jari ga ayyukan al'adu, da wasannin motsa jiki.

A fannin zuba jari kuma, Ning ya ce, gwamnatin Sin za ta ware mafi yawan kudi ga ayyukan kaurar da matalauta, da samar musu gidaje, da aikin raya kauyuka, da ginin manyan kayayyakin more rayuwa, da sabunta fasahohi, da kuma daidaita tsare-tsaren tattalin arziki. Jami'in ya ce, "A bana gwamnati za ta kara zuba kudi bisa kasafin kudin da aka tsara, da kara saurin samar da kudaden ga fannonin dake da bukata, sa'an nan za a kara janyo hankalin 'yan kasuwa domin su ma su zuba karin kudi ga wasu manyan ayyukan gwamnati."

A yayin taron aikin tattalin arzikin kwamitin kolin JKS, an kuma sanar da habaka aikin kara bude kofa ga waje daga dukkan fannoni. Ning Jizhe ya ce, kwamitin raya kasa da gyare-gyare na kasar Sin, zai gaggauta aiwatar da manyan ayyukan jarin waje bisa bukatun kasar Sin na kara bude kofa ga waje. Ya ce, a farkon watanni 3 na shekarar bana, kwamitin zai gaggauta aiwatar da manyan shirye-shiryen jarin waje rukuni na biyu, kana ko wane shirin zai zuba jari tsakanin dalar Amurka biliyan 1 zuwa biliyan 10. Ning Jizhe ya kara da cewa, "Manyan shirye-shiryen jarin waje na bana, sun hada da shirin motoci masu amfani da wutar lantarki, da kuma shirin batir na motoci masu amfani da wutar lantarki da dai sauransu, tabbas ne gudanarwar shirye-shiryen a kasar Sin, zai taimaka matuka wajen raya tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata tare da kamfanonin kasar ta Sin."

Haka kuma, ya ce, a bana, ba kawai, za mu kawar da wasu manufofin hana shigowar jarin waje ba ne, har ma kuma, za mu gyara "jerin fannonin da 'yan kasuwar ketare za su zuba jari a kasar Sin" da "jerin fannoni masu dacewa da 'yan kasuwar ketare za su zuba jari a yankunan dake tsakiya da yammacin kasar Sin", domin shigar da karin jarin waje kan fannoni daban daban. (Sanusi Chen, Bello Wang, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China