in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lippi yana fatan kungiyar wasan kasar Sin zata bada mamaki a gasar cin kofin Asiya ta 2019
2019-01-28 16:05:42 cri

Kociyan babbar kungiyar wasan kwallon kafan kasar Sin Marcello Lippi ya shirya kungiyar wasansa inda ya sha alwashin bada mamaki a gasar cin kofin Asiya ta shekarar 2019.

Kasar Sin, wacce bata taba samun nasarar lashe gasar ba, zasu fara buga wasansu da Kyrgyzstan a ranar Litinin. Koda yake kasar Sin bata taba kaiwa matakin zagaye na kusa da kusan karshe ba tun a shekarar 2004, Lippi har yanzu yayi amanna cewa "kungiyar wasan Dragon" zasu daga zuwa wani mataki da ba'a taba tsammani ba.

"Burinmu shine zamu yi iyakar kokarinmu kuma zamu samu kyakkyawan sakamako. Mun san cewa a gasa irin wannan akwai zababbu kamar su Japan, Australia, Iran da Koriya ta kudu, amma a koda yaushe akwai kungiyar wasa mai bada mamaki. Ina fatan zamu bada mamaki a wannan wasan "

"Nayi aiki a kasar Sin shekaru 7, nasan yadda fannin wasannin kasar Sin ke kulawa da babbar kungiyar wasa ta kasa, don haka inason zai samar da babbar gamsuwa a dukkan bangarori a fagen wasanni na kasar Sin." Inji kociyan dan shekaru 70 da haihuwa.

Dan wasan gaban kasar Sin Zheng Zhi, wanda shine dan wasa mafi tsufa a gasar cin kofin Asiyan ta 2019, zai yi hasarar buga wasa da kasar Kyrgyzstan saboda korar da aka yi masa.

"Mun san cewa za'a kori Zheng a rukunin farko na wasan, don haka mun yi kyakkyawan shirin domin shiga wannan wasan ba tare dashi ba."(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China