in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ba da lambobin yabo na kimiyya mafiya daraja na kasar Sin na shekarar 2018
2019-01-09 15:27:47 cri

Jiya Talata 8 ga wata ne, aka yi taron ba da lambobin yabo na kimiyya mafiya daraja na kasar Sin na shekarar 2018 a birnin Beijing. Lambobin yabon sun shafi fannonin muhimman ilmin kimiyya da fasahohin sana'o'i, wadanda ke da nasaba da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma, lamarin da ya shaida rawar da cigaban kimiyya da fasaha ya taka ga bunkasar tattalin arziki da kyautatuwar zaman rayuwar jama'a. Baya ga haka, an jaddada muhimmancin kirkire-kirkiren fasaha yayin da ake raya masana'antu.

An karrama shirye-shirye 278 da kwararru 7 da lambobin yabo na kimiyya na kasar Sin na shekarar 2018. A ciki, Malam Liu Yongtan daga jami'ar ilmin masana'antu ta Ha'erbin da Malam Qian Qihu daga jami'ar nazarin aikin injiniya ta rundunar sojojin Sin sun samu lambobin yabo mafiya daraja, baya ga lambar yabo kan kimiyyar halitta, da kirkiro fasaha, da ta ci gaban kimiyya da fasaha, da ta hadin gwiwa tare da kasashen waje ta fuskar kimiyya da fasaha, da dai sauransu da aka ba da.

Chen Zhimin, mai kula da aikin ba da lambobin yabon ya bayyana cewa, a cikin shirye-shiryen da suka samu lambobin yabon na kimiyya na shekarar 2018, akwai wasu manyan shirye-shirye na matakin farko, lamarin da ya sa kasar Sin ta kara samun karfin fada-a-ji a dandalin duniya. A waje daya kuma, lambobin yabon sun shaida gudummawar da cigaban kimiyya da fasaha ya ba da ga bunkasar tattalin arziki da kyautatuwar zaman rayuwar jama'a. Chen yana mai cewa, 

"Shirye-shiryen da suka samu lambobin yabon kimiyya na shekarar 2018 sun jibanci kirkire-kirkiren fasahohin masana'antu, wadanda suka mara baya sosai ga ci gaban tattalin arziki. Bugu da kari kuma, ana ci gaba da samun sakamakon da suka shafi kyautatar zaman rayuwar jama'a da raya muhallin halittu, kana kirkire-kirkiren fasahohin masana'natu yana ta taka muhimmiyar rawa."

A cikin shekaru 40 da suka gabata bayan da kasar Sin ta fara bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, kasar Sin ta samu manyan nasarori a fannin ci gaban kimiyya da fasaha, har ma wasu muhimman fannoni sun kasance a sahun gaba a duniya, ta haka ana iya ganin cewa, kimiyya da fasha ya ba da babbar gudummawa ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma. A cikin wadanda suka samu lambobin yabon kimiyya, Malam Ma Hongqi dake aiki a kamfanin samar da lantarki bisa karfin ruwa na kogin Lancangjiang na rukunin Huaneng na kasar Sin ya samu lamba ta biyu bisa na'urar daga jiragen ruwa bisa karfin ruwa da ya kirkiro, bayan da ya kwashe shekaru 11 yana nazarin na'urar tare da hadin gwiwa da sassan da abin ya shafa. Ita dai wannan na'urar daga jiragen ruwa tana da tabbaci ne ga zirga-zirgar jiragen ruwa yadda ya kamata yayin da yake wucewa ta madatsar ruwa. Malam Ma ya bayyana cewa, ta hanyar samar da karfi ga na'urar daga jiragen ruwa bisa karfin ruwa a maimakon bisa karfin wuta, an kyautata tsaron na'urar sosai da kuma tsimin makamashi, don haka na'urar na da kyakkyawar makoma. Ya kara da cewa,

"Na'urar daga jiragen ruwa bisa karfin ruwa ta hada da aikin zirga-zirgar jiragen ruwa a kogin Lancangjiang da na kogin Mekong, hakan ya saukakawa jiragen ruwa na gida da na waje, lamarin da ya taka muhimmiyar rawa wajen hadin gwiwar kogunan biyu da aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya'. A halin yanzu, ana amfani da wannan na'ura a sauran koguna, ana kuma iya amfani da ita sosai a aikin raya yankunan duwatsu da na koguna a duk fadin kasarmu."

A 'yan shekarun da suka wuce, yawan wadanda suka kamu da cutar sankarar huhu yana ta karuwa, har ma matsakaicin yawan karuwar ya zarce dubu 700 a ko wace shekara. Furfesa He Jianxing daga asibiti na farko dake tsangayar jami'ar ilmin likitanci ta Guangzhou ya samu lambar yabon kimiyya ta biyu a wannan karo bisa aikin kirkiro na'urorin likitanci da fasahar yin tiyatar da ba sai an bude jikin mutum ba, aikin ya taimaka sosai wajen kashe zafin ciwo ga wadanda suka kamu da cutar sankarar huhu da ma yi musu tiyata yadda ya kamata, wannan ya taimaka wajen kyautata ingancin rayuwar wadanda suka kamu da cutar da ma rage yawan kudin ganin likita. Furofesa He ya ce,

"Ta hanyar kyautata fasahar, yanzu ana iya yi wa wadanda suka kamu da sankarar huhu allurar kashe zafin ciwo da ma kyautata daidaicin tiyatar da aka yi musu, har ma suna iya samun warkewa cikin sauri. Alal misali, ga wadanda suka kamu da cutar a matakin farko, suna iya warkewa cikin kwana daya, har ma ana iya sallamarsu daga asibiti bayan kwanaki uku. Hakan ana ganin cewa, yadda muke warkar da masu kamuwa da sankarar huhu a matakin farko, ya fi sauri in an kwatanta da masu kamuwa da mura. Ban da wannan bayan da muka yi kokari cikin shekaru 20 da suka wuce, mun samu ci gaba sosai wajen yin tiyata ba tare da an bude jikin mutum ba, har ma wasu fasahohinmu sun kasance a sahun gaba a duniya." (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China